TAƘAITACCEN TSOKACI GAME DA AMERICA (2)
27 January 2021
A 1861 - 1865 ƙasar America ta shiga yaƙin basasa tsakanin arewacin ƙasar da kudancin ƙasar, biyo bayan zazzafan zaben da ya wakana wanda Abraham Lincoln ya yi nasara, a ciki. A wannan yaƙin ne aka ƴanta baƙaƙen fata duba da wasu dalilai na siyasa da tattalin arziƙi.
Har zuwa yaƙin duniya na ɗaya America bata taka wata rawar azo a gani a siyasar duniya ba, bal ma tana nisanta kanta daga shiga duk wani rikici na duniya, akan hakane ma aka zabi shugaba Woodrow Wilson wanda daga baya bayan wasu dalilai ya yanke kutsawar America yaƙin duniya na ɗaya yana mai goyon baya ga Ingila da Faransa da Rasha, waɗanda suke yaƙi da Daular Usmaniyya da Germany da Austria, wanda sakamakon wannan yaƙin ya sanya Ingila da Faransa suka zama sune sabbin jagororin duniya, hakanan kuma tasirin siyasar Ameirca da Rasha ya ƙaru.
A yaƙin duniya na biyu wanda ya wakana tsakanin Ingila da Faransa da Kuma Germany da Italy da Japan America d Rasha ba su yi saurin shiga ba sai lokacin al'amura suka yi nisa ingila ta gama jin jiki Faransa kuma an riga an cita nan Ameirca ta shiga bisa hujjar Japan ta kaimata hari, hakanan itama Rasha ta shiga wanda a lokacin take amsa sunan Tarayyar Soviet (USSR). Bayanan wannan yaƙin ne America da Tarayyar Soviet suka zama sabbin jagororin duniya.
Sakamakon barnar da yaƙin ya haifar a nahiyar Turai nan America ta kawo shirin Eroupean Recovery Plan (ERP) wanda aka fi sani da Marshall Plan da sunan tallafawa nahiyar wanda ta wannan shirin ta mallake ƙasashen Turai suka zama ƙarƙashin tasirinta, hakan kuma taƙara tattarasu ƙarƙashin Inuwar kawancen NATO domin tunkarar USSR wanda ita kuma a bisani ta kafa ƙwancen WARSAW
Bayanan kuma Sai America ta shiga kwatar in da Ingila da Faransa take yiwa mulkin mallaka da sunan tallafawa ƙasashen da ake mulka wajen ƙwatar kansu, kusan duk juyin mulkin da ya wakana daga ƙarshen 1940's har zuwa 1960's a ƙasashen da suke rainon Ingilane duk yaranan America ne suka jagoranci wannan juyin mulkin sune kuma suka maye gurbinsu don haka sai waɗannan ƙasashen kai tsaye suka koma ƙarƙashin inuwar America, waɗanda ba a yi juyin mulkin ba musamman ƙasashen larabawan da suke kan tsarin sarauta suka yi maza suka miƙa wuya suka shiga inuwar sabuwar jagorar duniya, da wannan lokacin America ta mallake siyasar rabin ƙasashen duniya, ya zama abin da ya ragemata shine mallake tattalin arzikin duniya.
Daga 1971 Zuwa 1974 America ta ci nasarar mallake tattalin arzikin duniya ta hanyar farlanta doller ta zama ita ce kuɗin cinikayya a duniya a maimakon Zinare hakan ya biyo bayan waƙi'ar Nixon Shock da yarjejeniyar Petrodollar da aka yi da ƙasashen Gulf, wanda ta ƙunshi sai da man fetur da doller kawai, ita kuma zata ba su kariya zata siyar musu da makamai, kuma wannan kuɗin da suka samu a cinikiyyar man fetur ɗin za zata ajye musu a bankunanta juya musu su.
1991 biyo bayan rugejewar USSR America ta zama ƙwaya ɗaya tilo mai jagorantar duniya, a wannan lokacin ta kai ganiyarta har zuwa 2001 ta shiga yaƙe-yaƙe a Afghanistan da Iraq wanda a wannan lokacin ta fara rauni da ja da baya daga duniya,
Zuwan Obama a 2009 wanda an kawo shine domin rarrashin mutane bama na America ba har na duniya, ya yi ƙoƙarin ɗago da ita America. Kusan a shuwagabannin a America babu wanda musulmai suka ɗanɗani kuɗarsu a hannunsa kamarsa,hakanan a lokacinsa ya fara zartar da Agendar Masoniyya wajen shar'anta fasadi da barna ƙarƙashin LGBT da yaɗa ilhadi.
Zuwan Trump wanda shi ƙadaine shugaba a tarihin America da yazo ba daga cikin ƴan Deep State ba ko kace ƴan Masoniyya wanda zuwansa ya ƙara sauya ƙasar..
A gaba zamu yi ɗan yi tsokaci akan Trump da kuma siyasarsa da dalilan da suka ka da shi a zabe hakanan da hasashen abinda watakila ka iya wakana a ƙasar
_#Abm Sani Umar_
https://www.facebook.com/Miftahulilmi.ml