AƘIDUN SHI'A DA TA'ADDANCINSU A TSAWON TARIHI //04

AƘIDUN SHI'A DA TA'ADDANCINSU A TSAWON TARIHI //04


WALLAFAR: Malam Najeeb El-Kabir Kwarbai

A CIKIN WATA RUWAYAR MALAMAN SHI'A GAME DA ABDULLAHI ƊAN SABA'I.

Daga Abi Abdullah Ya ce: “Allah ka la'anci Abdullahi ɗan Saba'i, shi ne wanda yace Amirul Muminina (AS) Allah ne! bayan kuma Amirul Muminina ya kasance bawa ne daga cikin bayin Allah, kuma mai biyayya gareShi. Azabar wailun (wuta) ta tabbata ga wanda yayi ƙarya a garemu, lallai wasu mutane suna faɗar wasu maganganu a kanmu, alhalin ba mu faɗa ba. Mun barranta a garesu, mun barranta a garesu.” [Duba: Rijalul Kishiyyu 70-71]

Waɗannan ruwayoyi guda biyu, kaɗan ne daga cikin ruwayoyin, akwai wasu da yawa suna nan cike a cikin littafan Shi'a.

A cikin waɗancan ruwayoyi da aka kawo, ya tabbatar mana ƙarara cewa Abdullahi ɗan Saba'i haƙiƙa an yi shi a tarihi, ba tatsuniya ba ce, kuma labarin shi ba shaci faɗi ba ne.

Mawallafin littafin “USULULIL ISMA'ILIYYA” Vernarid Louis ya tabbatar da samuwar Abdullahi ɗan Saba'i, duk da cewa shi wannan marubuci ORIENTALIST ne (wato kiristoci masu bin diddiƙin al'amuran musulunci, kuma su yi rubutu a kai).

Waɗannan zantukan da muka kawo maganganun malamai ne masana ta ɓangarorin Shi'a da Sunnah da kuma waɗanda ba musulmi ba, kamar yadda muka faɗa. Abu na gaba shi ne za mu ɗan waiwayi kaɗan daga cikin maganganun wasu da suke inkarin samuwar Abdullahi ɗan Saba'i.

1. Murtadhal Askariy: Yana da littafi wanda ya rubuta, kuma cikin littafin yayi inkarin samuwar Abdullahi ɗan Saba'i a cikin littafin, kuma ya yi ƙoƙarin ya kare maganganun shi da cewa Abdullahi ɗan Saba'i labarinsa tatsuniya ce kawai bata da asali. Wanda ya ƙirƙiro ƙissar shi ne Saif ɗan Umar, labarin kuma ya yaɗu ne ta littafin tarihin Ɗabariy.” [Duba Littafin: Abdullahi Bin Saba'i, bugawa Beirut, bugu na farko. Shekara ta 1974-1394]

AMSAR WANNAN MAGANA TA SHI BATA WUCE ABUBUWA KAMAR HAKA BA:

i- Bayan ruwayar da Imamu Ɗabariy ya kawo ta hanyar Saif ɗan Umar, akwai wasu ruwayoyin da suka zo daban, daga ciki akwai:

● Ta hanyar Ammar Ad-Duhuniy daga Abil Ɗufail.

● Ta hanyar Shu'uba daga Salama daga Zaid ɗan Wahab. [Duba: Tarikhu Dimashk 6/29, a ƙarƙashin tarjamar Abdullahi ɗan Saba'i]

ii- Idan muka koma littafan hadisai guda huɗu (Kutubul Hadis Al-Arba'a) waɗannan littafai ne na Shi'a. Da kuma littafin “Wasa'ilul Shi'a” za mu ga sun kawo wasu ruwayoyint ta wasu hanyoyin daban suke nuna samuwar Abdullahi ɗan Saba'i. Daga ciki akwai:

● Ta hanyar Muhammad ɗan Usman Al-Abdiy daga Yunus ɗan Abdurrahman daga Abdullahi ɗan Sinan daga Babanshi daga Abiy Ja'afar (AS). [Duba: Rijalul Kish-shiyyu 48]

● Ta hanyar Yaƙub ɗan Yazid daga Muhammad ɗan Isah daga Ibn Abiy Umar daga Hisham ɗan Salim zuwa ga Aba Abdillah (AS). [Duba: Rijalul Kish-shiyyu 48]

Saboda haka waɗannan ruwayoyi sun isa su nuna cewa ba ta hanya ɗaya kaɗai labarin Abdullahi ɗan Saba'i yazo ba, kamar yadda suke cewa. 

2. Ɗaha Hussain: Shi ma ya yi inkarin Abdullahi ɗan Saba'i a cikin littafinsa mai suna “Aliyu wa Banuhu...” Shi wannan mawallafin a yadda ɗabi'unsa suke, don ya kawo irin wannan maganganu a littafinshi ba abun mamaki ba ne. Saboda a cikin littafinshi mai suna “Ash-Shi'irul Jahiliy” shafi na 22, ya bayyana cewa bai yadda Annabawan Allah guda biyu Ibrahim (AS) da Isma'il (AS) sun gina Ka'aba ba, har yake cewa: “Ko da Alƙur'ani ya ba da labari akan haka, wannan ba ya nuna hakan ya faru. Saboda haka mutum irin wannan, wanda yake ɗabi'ar shakku akan abun da yake akwai tabbacin an yi shi, ba a kafa hujja da irinsu da maganganunsu. 

Zamu ci gaba in shaa ALLAH.
Post a Comment (0)