ASALIN YAƊUWAR SHI’A A NIJERIYA

بسم الله الرحمن الرحيم 
 


Asalin yaɗuwar Shi’a a Nijeria ya fara a tsakanin matasa, yawanci ƴan makaranta, masu aikin yaɗa addinin Musulunci waɗanda aka san su da sunan ƴan Uwa Musulmi. Wannan suna fassara ce kai tsaye ta sunan wata Ƙungiya, Al’ikhwanul Muslimun, wacce Imam Hassan Albanna ya kafa a ƙasar Masar a cikin shekarun 1930. Babbar manufar ƙungiyar shi ne mayar da Musulmi zuwa ga hukunce – hukuncen Musulunci a kafatanin fagagen rayuwarsu wanda ya haɗa da fagen siyasa, tattalin arziƙi, tarbiya da zamantakewa da kuma dangantakarsu da waɗanda ba Musulmi ba. Ƙungiyar ta yaɗu a yawancin ƙasashen Musulmi ciki har da Nijeriya.  

 Tare da ƙungiyar Ƴan Uwa Musulmi akwai ƙungiyar Ɗalibai Musulmi ta Nijeriya, watau M.S.S. wacce aka kafa ta shekaru 50 da suka wuce. Waɗan nan ƙungiyoyi biyu sashen su ya haɗe da sashe kuma suna yin nashaɗinsu a jami’o’i da manyan makarantun ƙasar nan. A wani yayi nashaɗinsu yana shafar ƴan makarantun sakandare ta hanyar tarukan horaswa da suke shiryawa ɗaliban ƙananan makarantu a lokacin hutu. Masu shagala da aikin da’awa a ƙarƙashin inuwar waɗan nan ƙungiyoyi yawancinsu matasa ne maza da mata masu karatun fannonin ilmi dabam – daban, kamar Kimiya da Likitanci da Tattalin Arziki, amma kaɗan ne daga cikinsu suke karanta Musuluncin kansa. Wannan ya sa, koda yake suna da son Musulunci ga kuma gafin ƙuruciya, amma suna da ƙarancin ilmin addini. Saboda haka a lokacin da Shi’a ta shigo ƙasar nan, a kan doron juyin juya hali na Musulunci (!) na ƙasar Iran da kirarinsa mai ɗaukar hankali na kafa jumhuriyar Islama da zartar da hukunci da Shari’a, sai yawancin waɗannan samari suka hau jirgin Shi’a da tikitin juyin Islama. Daga cikin waɗan nan samari akwai Malam Ibrahim Ya’aƙub Alzakzaki.


 - JERIN LITTAFAN SHI’A NA 7: " ```Zuwan Shi’a Nijeria```" - na Prof. Umar Labɗo

 *✍ AnnasihaTv* 

- Masu son siyen littafan da ma wasu littafan Prof sai su tuntuɓe mu kamar haka;

 *Call/WhatsApp:* 08063836963

 *Twitter:* https://twitter.com/AnnasihaTv?s=09
Post a Comment (0)