ALZAKZAKI DA YAƊUWAR SHI’A



ALZAKZAKI DA YAƊUWAR SHI’A  
Sunan Zakzaki ya fara fitowa a farkon shekarun 1980 lokacin da, bayan kammala karatunsa a fannin Tattalin Arziƙi daga Jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria, ya ƙi ya je aikin bautar ƙasa, watau N.Y.S.C. saboda, kamar yadda ya ce, shi ba ya bautawa ƙasa; Allah kaɗai yake bautawa.  Duk da raunin wannan magana da rashin fahimtar addini da take nunawa a fili, wannan mataki da Zakzaki ya ɗauka ya ba shi farin jini kuma ya mayar da shi tamkar wani gwarzo a idanun matasa waɗanda wutar son addini take ci a zukatansu amma ƙwaƙwalensu sun yi duhu duɗum saboda jahilci.  Zakzaki ya wayi gari ana lasafta shi daga cikin shugabannin ɗalibai da matasa masu sha’awar addini. 

Ba’a daɗe da haka ba, sai mahukuntan ƙasar Iran masu bin tafarkin Shi’anci, a cikin ƙoƙarinsu na neman goyon bayan Musulmin duniya musamman a kan yaƙinsu na shekaru takwas da ƙasar Iraƙi, suka riƙa gayyatar malamai da matasa masu sha’awar addini daga ko wane ɓangare na duniyar Musulmi domin su halarci bikin shekara – shekara da suke yi don tunawa da nasarar juyin juya halinsu.  Zakzaki na daga cikin waɗanda aka gayyata daga Nijeriya. 
Mahukuntan Iran waɗanda suke ɗaukar nauyin baƙinsu zuwa da komowa, suna nunawa baƙin karamci, suna girmama su ainun kuma ga alama suna ba su ɗan goro a matsayin sallama.  Banda wannan, suna ƙoƙarin cusa wa baƙin nasu aƙidar Shi’anci ta hanyar laccoci, muhalarori, tarukan ƙarawa juna sani da kuma kyautar littafai masu yawa.  Ga alama ta wannan hanya sun yi nasarar ribace wasu da shigar da su tafarkinsu kamar Zakzaki, wasu kuwa sun gane makircinsu sai suka raba gari da su.  Daga cikin waɗanda aka gayyata daga Nijeriya kuma amma ba’a yi nasarar janye su zuwa Shi’anci ba akwai Malam Abubakar Tureta daga Kaduna da Malam Abubakar Jibril daga Sakkwato wanda ya zama a sahun gaba wajen yaƙar Shi’anci a Nijeriya. 

Alaƙar Zakzaki da Iran ta ci gaba da yin ƙarfi a hannu guda, a ɗaya hannun kuma shahararsa ta bunƙasa, kuma magoya bayansa suka ƙara yawa, a yayin da ya buɗe ressa a yawancin jihohin arewacin ƙasar nan, yana kira da sunan gwagwarmayar kafa hukuncin Musulunci da yaƙar waɗanda ya kira ɗagutai.

Mabiyan Zakzaki sun yi ban gaskiya da shi ainun, sun yarda da shugabancinsa har suna ganin wanda duk bai ɗauke shi a matsayin shugaba ba kamar shi ba Musulmi ba ne, suna cewa wanda ya mutu bai yi masa mubaya’a ba to ya mutu mutuwar Jahiliya.  Shi kuwa ya yi amfani da amince masa da suka yi, ya riƙa gabatar musu da koyarwar Shi’a da aƙidojinsu sannu a hankali kuma koda yaushe aka tsorata su da kusancin shugabansu da Iran, sai ya ba su tabbacin cewa shi babu abinda ya haɗa shi da Iran sai gwagwarmaya da yaƙar Amurkawa da Yahudawa da ɗagutai.  Amma kuma a hannu guda, Zakzaki ya ci gaba da shigo da alamu da bukukuwan Rafilawa kamar babbaƙun rawuna, bikin Ashura, da sauransu.

Haka nan gogan naka ya ci gaba da taƙiya, yana yaudarar almajiransa da magoya bayansa har ranar da dubunsa ta cika.  Wata mujalla daga cikin irin mujallun da ake bugawa a ƙasar Iran ana aikowa da su Nijeriya ta buga wata maƙala wacce a cikinta aka ci zarafin Sahabin Annabi (SAW) mai shuhura watau Abu Huraira (R.A).  Wannan ya tayar da hankalin wasu daga cikin mabiyan Zakzaki inda suka nemi ya fito fili ya la’anci wannan maƙala amma ya ƙiya.  Wannan shi ya buɗe idanun da yawa daga cikin mabiyansa, waɗanda a da jahilci da bin son zuciya ya rufe idanun nasu.  Daga nan aka samu wani reshe a cikin mabiyan Zakzaki wanda ya yi ta matsawa malamin lamba a kan ya fito fili ya bayyana matsayinsa dangane da ko Shi’a yake yi ko a’a. Zakzaki ya ci gaba da noƙewa har dai daga bisani tusa ta ƙurewa bodari kuma gaskiya ta yi halinta.  A cikin shekarar 1995 aka yi uwar watsi bayan wani taron ƙure ƙarya da aka yi wa Zakzaki a hedkwatarsa a Zaria.  Mabiyansa da yawa, ciki har da manyan almajiransa, suka ɓalle, suka yi shelar barrantarsu da Zakzaki da tafarkinsa na Rafilanci kuma suka kafa tasu ƙungiya ta yunƙurin jaddada Musulunci a kan tafarkin Ahlus Sunna, Jama’atu Tajdidil Islam (J.T.I.), a ƙarƙashin shugabancin Malam Abubakar Mujahid.  A yanzu asirin Zakzaki ya tonu kuma taƙiya ta ƙare, amma kash!  Biri ya riga ya yi ɓarna.   


•••═══ ༻✿༺═══ •••
 - *JERIN LITTAFAN SHI’A NA 7: "Zuwan Shi’a Nijeria" - na Prof. Umar Labɗo* 

✍ *AnnasihaTv* 

- Ga masu son siyen littafan da ma wasu littafan Prof sai su tuntuɓe mu kamar haka;

Call/WhatsApp: 08063836963

Twitter: https://twitter.com/AnnasihaTv?s=09
Post a Comment (0)