IMAMAN ƳAN SHI’AH SUN FI ANNABAWA DA MALA'IKU

[IMAMAN ƳAN SHI’AH SUN FI ANNABAWA DA MALA'IKU] 




Har ila yau, ƴan Shi’a suna wuce gona da iri wajen son imamansu da girmama su da kambama su har su fifita su a kan annabawa da manzanni da mala’iku makusanta ga Ubangiji. Ya zo a cikin irin ruwayoyin da suke danganawa ga Annabi (SAW) cewa wai ya ce da Ali (RA): “Lallai Allah mai girma da ɗaukaka ya fifita annabawansa manzanni a bisa mala’iku makusanta, kuma ya fifita ni a kan dukkanin annabawa da manzanni. Ya kai Ali, fifiko a bayana ya tabbata a gare ka da imamai masu zuwa a bayanka.” *_[A duba Ilalush Shara’i’i na Muhammad binu Babawaihi Alƙummi Assaduk, bugun Almaktabatul Haidariyya, Najaf- Iraƙ, shafi na 5]_*. A cikin wani littafin nasu mai suna Haƙƙul Yaƙin fi Usulid Din, mai littafin, Abdullahi binu Shabbar, yana cewa, “Ya wajaba a yi imani cewa Annabinmu da alayensa ma’asumai suna da fifiko a kan annabawa da manzanni da mala’iku makusanta saboda hujjoji masu yawan gaske da suka zo da haka.” *_[A duba Hakkul Yakin fi Usulid Din na Abdullahi Shubbar, bugun Darul Kitabil Islami, Bairut, ba tarihi, mujalladi na 1, shafi na 209]_*.
Banda wannan duka, Rafilawa suna tabbatar wa da imamansu sifofin allantaka. Daga cikin irin abubuwan da suke danganta wa Ali binu Abi Ɗalib(RA) akwai wannan ruwaya cewa wai ya ce, “Ni ne idanun Allah; ni ne hannun Allah; ni ne ƙofar Allah.” A wata ruwayar kuma ya ce, “Ni ne ilmin Allah; ni ne zuciyar Allah mai kiyayewa; ni ne harshen Allah mai furuci; ni ne idanun Allah masu gani; ni ne haƙarƙarin Allah; ni ne hannun Allah.” *_[A duba Basa’irud Darajat na Muhammad binu Hassan Alsaffar, bugun Manshuratul A’alami, Teheran-Iran, 1362, shafi na 81]_* .
Dangana irin waɗannan ruwaroyi na ƙarya bai tsaya kan Ali ba kawai, a’a har ma ga Annabi(SAW) suna danganawa. Sulaim binu Ƙais ya ruwaito cewa Manzon Allah(SAW) ya faɗi ga Ali kamr haka: “Ya Ali, kai kana daga gare ni, ni ina daga gare ka. An gauraya namanka da namana, da jininka da jinina…. Wanda ya yi musun wilayarka ya yi musun allantakar Allah. Ya Ali, kai ne tutar Allah mafi girma a bayan ƙasa bayana, kuma kai ne bango mai girma a ranar Alƙiyama. Wanda ya shiga inuwarka ya rabanta domin hisabin talikai duka yana hannunka kuma makomarsu na gare ka. Mizani naka ne; siraɗi naka ne; taron Alƙiyama naka ne; hisabi naka ne. Wanda ya fake da kai ya tsira kuma wanda ya saɓa maka ya halaka. Allah ka shaida, Allah ka shaida.” *_[Kitab Sulaim binu Ƙais na Sulaim binun Ƙais Alkufi, bugun Manshuratul A’alami, Teheran-Iran, ba tarihi, shafi na 244-245]._* 
Kamar yadda mai karatu yake iya gani, a wajen ƴan Shi’a imamai su ne komai. Suna gaba da annabawa da manzanni kuma suna tarayya da Ubangiji a allantakarsa. Wannan ya sa aka samu wasu daga cikinsu waɗanda suke bauta musu kuma suna bayyana wannan a fili ta wajen irin sunayen da suke saka wa ƴaƴansu, kamar Abdul Hussain, Abdul Amir (Amir suna nufin Ali), da sauransu. 
Wannan ita ce aƙidar ƴan Shi’a dangane da imamai, kuma wannan shi ne yadda suka ɗauke su. Babu shakka wannan aƙida ta saɓa da Alƙur’ani mai girma da hadisan Annabi(SAW) ingantattu. Kai ta ma saɓa da hankali lafiyayye. Haka nan kuma ta saɓa da aƙidar imaman su da kansu, saboda imaman Shi’a dukkaninsu, tun daga kan Ali binu Abi Ɗalib har ya zuwa na ƙarshensu, mabiya Sunnar Annabi ne, sai dai malaman Shi’a sun laƙa musu ƙarerayi don su fake da su, su samu dammar ɓatar da al’umma. 
Wannan shi ne ƙudurin Ahalus Sunna dangane da imaman Shi’a, Allah ya ƙara musu yarda, cewa duk abinda aka dangana musu wanda ya saɓa da Alƙur’ani da Sunna, to ƙarye ce ake yi musu. Muna roƙon Allah ya isr musu wannan ƙarya da ƙazafi da Yahudawa da Majusdawa suka laƙa musu. 
A nan gaba, za mu ware imamai da ambato, mu yi bayanin matsayinsu a wajen Ahalus Sunna a wani littafi na musamman, in Allah ya yarda. 



•••═══ ༻✿༺═══ •••
 - JERIN LITTAFAN SHI’A NA 6: " ```Ahalul Baiti a mahangar Ƴan Shi’a da Ahalus Sunna```" - na Prof. Umar Labɗo

 *✍ AnnasihaTv* 

- Ga masu son siyen littafan da ma wasu littafan Prof sai su tuntuɓe mu kamar haka;

 *Call/WhatsApp:* 08142286718

 *Twitter:* https://twitter.com/AnnasihaTv?s=09
Post a Comment (0)