DALILAN YAƊUWAR SHI’A A NIJERIYA [1]

DALILAN YAƊUWAR SHI’A A NIJERIYA [1] 



Akwai dalilai masu yawa da suka taimaka wajen yaɗuwar tafarkin Rafilanci a nan ƙasar. Za mu duba muhimmai daga cikinsu. 

 *Dalili Na Farko: Gazawar Malamai* 

Dalili na ɗaya kuma mafi muhimmanci, shi ne gazawar malamai a shugabancin jama’a da shiryar da su, da yi musu jagora da katangance su daga ɓata. Domin famintar wannan dalili za mu kasa malamai gida uku. 

1. *Malaman zaure,* ko kuma malaman buzu kamar yadda ake kiran su a wasu wurare. Wannan kashi a cikin malamai su ne mafi girma, mafi alƙadari kuma mafi ƙima a idanun mutane. Amma duk da girma da ƙimarsu da muke gani, za mu rufe ido mu faɗi gaskiya game da su domin gaskiya ta fi ko wane mai ƙima ƙima. 

 Matsala ta farko da malaman zaure, yawancin su, shi ne imma dai suna da ƙarancin sani ko kuma ilminsu ya saɓa Sunna. Ɗauki ilmin Tauhidi ga misali, wanda shi ne mafi muhimmanci kuma mafi ɗaukakar dukkan ilman Musulunci. Har yanzu malamanmu na buzu ba su rungumi tafarkin Sunna ba a babin Tauhidi; Tauhidinsu imma Ash’ariya ne ko kuma Tauhidin masu Ilmul Kalam wanda yake da tushensa a wajen Mu’utazilawa ko Falasifawa. 
 A fannin Fiƙihu, wanda shi ne fannin da malaman zaure suka yi fice, yawancinsu a Fiƙihun Malikiya kawai suka tsaya. Idan mutum ya duba cewa banda sauran mazhabobi uku fitattu, watau Hanafiya, Shafi’iya da Hanbaliya, akwai mazhabobin Zahiriya da Zaidiya, banda mazhabobin ɗaiɗekun malamai waɗanda ba su samu yaɗuwa ba kamar mazhabar Imam Thauri da Imam Auza’i da sauransu, sai mutum ya ga cewa babu shakka malamanmu kaɗan suka ɗebo a Fiƙihun Musulunci. Ba’a maganar fannin Usulul Fiƙhi. Kuma ko a Malikiya ma, wasu littafai ne ƙididdigaggu suke laƙema, wasu manyan littafan mazhabar yawancinsu ba su karanta su, kamar Tafsirin Ƙurɗubi da Tafsirin Abubakar Ibnul Arabi, da Altamhid na Ibnu Abdilbarri da Bidayatul Mujtahid na Ibnu Rushd, da sauransu. A nan ba kuɗin goro muke yi wa malaman ba; amma muna bayyana halin yawancinsu ne. 

 A fannin Tafsiri kuwa, ya ishe ka manuniya cewa a ƙasar Hausa duka idan mutum ya ce, “Na tafi wajen jalalaini,” to wajen karatun tafsiri yake nufi saboda tafsiri shi ne jalalaini kuma jalalaini shi ni tafsiri. Wannan yana nuna yadda malamanmu suka tsaya a kan littafin Tafsirul Jalalaini na Jalaluddinil Mahalli da Jalaluddinis Suyuɗi kawai a koyo da koyarwarsu na fannin Tafsiri. Idan aka duba cewa wannan littafi bai kai matsayin moɗa guda ba a cikin kogi dangane da abinda aka rubuta a fannin Tafsiri, sai a ga cewa tabbas abinda malamanmu suka rasa ya fi abinda suka samu a cikin wannan fanni. Bari batun ilmin Usulul Tafsir. A nan ma, ba kuɗin goro muke yi wa malaman ba; amma hukunci a kan mafi yawa ake yin sa, mafi ƙaranci togewa ne. 

 Matsalar Luga a wajen malaman buzu makomarta ita ce ga matsalar manhaja da tsarin koyarwa. Koyon Luga yana da rukunai uku: karatu da rubutu da furuci. Ga alama malaman zaure karatu kaɗai suke yi saboda a tsarin karatun zaure babu zancen a bayar da aiki a rubuto, watau abinda ake cewa da Larabci “tamrinat” ko “tamarin”, ko kuma da Turanci “exercises”. Wannan ya sa koda yake malaman zaure yawanci suna da babbar taska ta ɗaiɗekun kalmoni, “vocabulary”, amma magana da Larabci tana yi musu wuya, haka nan rubutawa. Kuma koda yake ana iya lura cewa malaman buzu gwanayen rubutun waƙa ne da Larabci, makomar wannan, wata ƙila, shi ne cewa ita waƙa ƴar kyaikwayo ce. 

 Haka nan a fannonin Hadisi da Tarihi da Sira da Firaƙ; malaman buzu, in ka ɗauke su gaba ɗaya, suna da ƙarancin rabo a cikin waɗan nan ilmai. Rashin ilmin Firaƙ, watau ilmin ƙungiyoyin bidi’a da aƙidojinsu, shi ya sa malaman zaure suka rasa ta yi a gaban kogin Shi’anci yayin da ya yi ambaliya domin ya tafi da matasan Musulmi. Manyan littafan da aka rubuta a ilmin Firaƙ kamar Almilal wal Nihal na Shahrastani da Maƙalatul Isl amiyina wa Ikhtilaful Musallina na Imam Abul Hassan Al’ash’ari da Alfarƙu bainal Firaƙ na Shaihul Islami Abdulƙahir Albagdadi da Alfisal fil Milal wal Ahwa’i wal Nihal na Ibnu Hazm Al’andalusi da sauransu, yawancinsu ko sunayensu ba su taɓa ji ba.

Wannan ya sa suka ɗauka cewa wai Shi’anci wani wasan yara ne wanda za su bari in sun girma! Idan aka ce su bincika abinda yake faruwa a tsakanin Rafilawa sai su ce, haba wannan hayaniyar ƙuruciya ce suke yi, za su bari ne. Sai ga shi waɗan nan malamai waɗanda suka tashi zaune tsaye a saboda wasu ƴan ƙungiyoyi da suka ce wai suna zagin waliyai, sai ga shi ana zagin Sahabban Annabi (SAW), ana kafirta su, amma sun yi shuru. Saboda haka malaman suka kyautata alwala amma suka gaza sallah! 

 Abinda ya gabata dangane da ilminsu ne; amma idan muka duba ayyukansu sai mu ga abin mamakin. Mun gabatar da bayani cewa a cikin malaman Musulunci a nan ƙasar, malaman zaure su ne mafi yawa, mafi alƙadari kuma mafi ƙima a idanun mutane. Abinda ya sa suka zama haka shi ne cewa su magadan Jihadin Shaihu Danfodiyo ne. Amma a yau, ayyukansu da halayensu sun saɓa da na malaman Jihadi. Malaman Jihadi sun yi ilmi mai zurfi, kuma littafan da suka bari suna shaidawa da haka, amma malamanmu na yau abin ba haka yake ba. Shaihu Usmanu ya rubuta kimanin littafai 90, Shaihu Abdullahi kimanin 70; Muhammad Bello ɗan Shaihu kimanin 80; Nana Asma’u kimanin 55; amma malamanmu na yau, saboda gafala rubutun ma laifi suka ɗauke shi. Idan ka ce su rubuta littafi sai su ce wai ba su gama da waɗanda aka riga aka rubuta ba; idan kuma kai ka rubuta sai su ce ka yi karambani. Alhali Shaihu Usmanu, a cikin littafinsa Najmul Ikhwani, yana kira ga Musulmi da su riƙa karanta littafan malaman zamaninsu, saboda malaman ko wane zamani su suka fi sanin matsalolin wannan zamanin, kuma wajibinsu ne su nemawa matsalolin magani. 

 Malaman jihadi sun yi wa’azi, malaman buzu ba sa yin wa’azi sai kaɗan. Malaman jihadi sun yaƙi bidi’a, malaman zaure su bidi’ar suke yaɗawa kuma duk wanda yake yaƙi da bidi’a to su shi ne abokin gabarsu. Malaman jihadi sun nesanci sarakai da masu mulki, na yanzu kuwa shige musu suke yi. Malaman jihadi sun yi jihadi kuma sun jaddada addini, malamanmu na yau ba su san ko inda za’a kama bakin zaren ba. Malaman Jihadi sun tsaya tsaiwar daka, sun yi gwagwarmayar tabbatar da gaskiya da tsai da adalci, malamanmu na yau cewa suke yi yanzu zamanin yin shiru ne da lazimtar cikin gida, kamar yadda wani babban malamin zaure ya faɗa wa Shaihu Abubakar Mahmud Gumi. [Duba Where I Stand na Abubakar Mahmud Gumi, bugun Spectrum Books, Ibadan-Nijeriya, 1992, shafi na 51]. Malaman jihadi sun gina al’umma, malaman buzu sai aikin gina gidajensu na gado. Ko wane malami ya ƙasaita sai ka ji ya naɗa khalifa, wai ɗan da zai gaje shi. Ko waye ya ce musu ilmi gado ne? Malaman jihadi sun ce a yi sana’a (duba Ahkamul Makasib na Muhammad Bello) su kuwa yawanci ba sa sana’ar, balle su ce wani ya yi, sai cin abinda suke kira albarkacin makaranta!! Wani malamin ma har faɗa yake yi don me za’a ce Musulmi su daina bara!! Kuma ƙarya yake yi; shi ƴaƴansa ba sa bara. 
 Kai a yau ta kai cewa malaman buzu da yawansu, ba wai kawai sun raba gari da tafarkin Shaihu Ɗanfodiyo ba da tarihinsa da koyarwarsa, a’a yaƙar sa ma suke yi! Sun ƙaurace wa littafansa da ilminsa da koyarwarsa. Mutum zai yi shekara guda cur bai ji sunan Ɗanfodiyo ya gudana a bakin ɗayansu ba a wajen karatu ko wa’azi. Maimakon haka, sun rungumi koyarwar wasu jahilan malamai waɗanda bas u zo ƙasar nan da kome ba sai diwanin waƙe-waƙe. 

 Wannan shi ne halin yawancin malaman azure, kuma shi ne tushen kusan dukkanin matsalolin da muke fama da su a yau. Don haka babu mamaki idan ba su taka rawa ta ku-zo- ku-gani ba wajen hana yaɗuwar Shi’anci a ƙasar nan.

•••═══ ༻✿༺═══ •••
 - JERIN LITTAFAN SHI’A NA 7: " ```Zuwan Shi’a Nijeria```" - na Prof. Umar Labɗo

 *✍ AnnasihaTv* 

- Ga masu son siyen littafan da ma wasu littafan Prof sai su tuntuɓe mu kamar haka;

 *Call/WhatsApp* : 08063836963

 *Twitter* : https://twitter.com/AnnasihaTv?s=09
Post a Comment (0)