Hukuncin Ahalus Sunna A Wajen ƴan Shi'a]: Halaccin La’antar Su

[ Hukuncin Ahalus Sunna A Wajen ƴan Shi'a]: Halaccin La’antar Su 
•••═══ ༻✿༺═══ •••


Ƴan Shi’a suna ƙudure halaccin la’antar Ahalus Sunna da ma duk wani Musulmi wanda ba ya bin tafarkinsu. Kuma Ahalus Sunna ɗin ba wai kawai ɗaiɗekunsu da gama-garinsu ba, a’a har da shugabanninsu da magabatansu, kama tun daga Sahabban Annabi (SAW) har ya zuwa ko wane ƙaramin Musulmi da yake rayuwa a yau. A haƙiƙa ma, la’antar da suke wa Sahabbai ba sa yi wa ƙananan Musulmi irinta.  

Ruwaya ta gabata, a baya kaɗan, daga shaihinsu Alkhu’i inda yake cewa, “Lallai ya tabbata cikin ruwayoyi da (littafan) addu’o’i halaccin la’antar masu saɓa mana…” Wannan shi ne hukuncin wanda duk yake saɓa musu, watau ba ya bin tafarkinsu na Rafilanci. Su kuwa Sahabbai, musamman manya-manyansu kamar Abubakar da Umar da Usmanu da A’isha da Hafsa, Allah ya ƙara musu yarda, to su la’antar su ibada ce wacce ake samun lada mai tarin yawa da ita. 

Akwai ruwayoyi masu yawa a littafan Rafilawa da suke nuna ladan la’antar Abubakar da Umar, Allah ya ƙara musu yarda. Ga ɗaya daga cikinsu: 

Mulla Kazim, wanda yake mashahurin malami ne na Shi’a, ya karɓo ruwaya, yana dangana ta bisa ƙarya ga Ali Zainul Abidin binul Hussain binu Ali binu Abi Ɗalib. Ya ce, Abu Hamza Althumali ya karɓo daga Ali Zainul Abidin ya ce, “Wanda ya la’anci Jibtu da Ɗagutu (yana nufin Abubakar da Umar) la’ana guda, Allah zai rubuta masa lada dubu sau dubu, ya kankare masa zunubi dubu sau dubu kuma ya ɗaukaka masa daraja dubu sau dubu saba’in. Kuma wanda ya la’ance su da yammaci la’ana guda za’a rubuta masa kamar haka.  (Mai ruwaya) ya ce:  Sai shugabanmu Ali binu Hussaini ya wuce (bayan ya faɗi wannan magana, ni kuma) sai na shiga wurin shugabanmu Abu Ja’afar Muhammad Albaƙir na ce masa: Ya shugabana, wata magana ce na ji daga mahaifinka. Sai ya ce: Faɗe ta mu ji, ya kai Thumali. Sai na maimaita masa maganar. Sai ya ce:  Haka take, Thumali. Ko kana so in yi maka ƙari?  Sai na ce:  E, ya shugabana.  Sai ya ce:  Wanda ya la’ance su la’ana guda a ko wace safiya ba za’a rubuta masa zunubi ba a wannan wunin har yammaci, kuma wanda ya la’ance su la’ana guda da yammaci ba za’a rubuta masa zunubi ba har ya wayi gari.” [A duba Ajma’ul Fala’ih na Mulla Kazim, 513].    

Wannan ya sa malaman Rafilawa suka wallafa addu’o’i na musamman don la’antar Abubakar da Umar, Allah ya ƙara musu yarda, waɗanda ƴan Shi’a suke maimaitawa safe da yammaci, da kuma a bayan salloli na farilla, kamar yadda Musulmi suke wurdi da lazimi. Mafi shahara a cikin waɗannan addu’o’i ita ce addu’ar nan da suke kira Du’a’u Sanamai Ƙuraishin, watau Addu’ar Gumakan Ƙuraishawa Biyu (suna nufin Abubakar da Umar). [Domin ganin wannan addu’a, sai a duba littafin Bacin Tafarkin ƴan Shi’a da Aƙidojinsu, babin Aƙidar ƴan Shi’a Dangane da Sahabbai]. 

Har yau, akwai wata addu’ar la’ana mai lugude, wacce ta ƙunshi la’antar magabata guda tara, waɗanda suka haɗa da Sahabbai da Tabi’ai, tare da maimaita la’ana ga Umar sau tara. Ga yadda lafazin addu’ar yake: 
Allahumma il’an Umara, thumma Ababakarin wa Umara, thumma Usmana wa Umara, thumma Mu’awiyya wa Umara, thumma Yazid wa Umara, thumma Ibna Ziyadin wa Umara, thumma Ibna Sa’adin wa Umara, thumma Shamran wa Umara, thumma Askara hum wa Umara. Allahumma il’an A’ishata wa Hafsata wa Hindan wa Ummal Hakam. Wal’an man radiya bi af’ali him ila yaumil ƙiyamah. [A duba La’ali’ul Akhbari na malaminsu Muhammad Attursirkani, bugun Ƙum, Iran, ba tarihi, 4/92].   
 Ga ma’anar addu’ar: Ya Allah ka la’anci Umar, sa’an nan Abubakar da Umar, sa’an nan Usmanu da Umar, sa’an nan Mu’awiyya da Umar, sa’an nan Yazidu da Umar, sa’an nan Ibnu Ziyad da Umar, sa’an nan Ibnu Sa’ad da Umar, sa’an nan Shamru da Umar, sa’an nan Askar nasu da Umar. Ya Allah ka la’anci A’isha da Hafsa da Hindu da Ummul Hakam, kuma ka la’anci (duk) wanda ya yarda da ayyukansu har ya zuwa ranar Alƙiyama.

 Wannan babbar addu’a ta ƴan Shi’a tana bukatar darasu. Da farko dai bari mu bi sunayen da suka zo a cikinta domin mu san su waye. Abubakar da Umar da Usmanu da Mu’awiyya, Allah ya ƙara musu yarda, ba sa bukatar bayani; kowa ya san su. Haka nan A’isha da Hafsa. Yazidu kuwa shi ne ɗan Mu’awiyya wanda ya gaje shi a mulkin daular Musulunci, kuma wanda a zamaninsa ne aka kashe Hussaini(RA). Ibnu Ziyad shi ne gwamnan Kufa a zamanin mulkin Yazidu, kuma rundunarsa ce ta kashe Hussaini(RA). Shi kuwa Ibnu Sa’ad (sunansa Umar binu Sa’ad binu Abi Waƙƙas) shi ne kwamandan rundunar da ta kashe Hussaini(RA). [Domin bayanin rawar da Yazidu da Ibnu Ziyad da Ibnu Sa’ad suka taka wajen shahadar Hussaini(RA) a Karbala, sai a nemi littafinmu Wa Ya Kashe Hussaini? bugun Zomo Press, Kaduna, 2010]. Shamru ban san shi ba; ban gane wanda suke nufi da shi ba. Ga al’adar Rafilawa idan suka yi amfani da kalmar Askar to A’isha suke nufi da ita, saboda raƙumin da ta hau a yaƙin Jamal sunansa Askar. Kuma da yake an ambace ta da suna a cikin addu’ar, muna iya ɗauka cewa ita ma an ninka mata la’ana ne saboda tsananin ƙiyayya, kamar yadda aka ninninka wa Umar. Hindu kuwa ita ce mahaifiyar Mu’awiyya (RA) kuma Ummul Hakam ita ce kakar Marwan binul Hakam, uban yawancin khalifofin Banu Umayya, ciki har da Umar binu Abdil’aziz khalifa mai adalci, Allah ya yi masa rahama.

Dalilin la’antar waɗannan manyan bayin Allah a wajen ƴan Shi’a abu ne mai sauƙi. Su dai Abubakar da Umar da Usmanu, Allah ya ƙara musu yarda, laifinsu a wajen Rafilawa shi ne wai sun hana Ali binu Abi Ɗalib khilafa, kuma sun hana ma Faɗima (RA) gado na gonar da mahaifinta Annabi(SAW) ya bari. Ita kuma A’isha (RA) ta yi faɗa da Ali a Yaƙin Jamal. Hafsa(RA) ba ta yaƙi Ali ba, kuma ba ta yi ma Faɗima kome ba. Don haka muna iya ɗauka cewa wata ƙila ƙiyayyar ubanta, Umar binul Khaɗɗabi, ce ta nashe ta, ta ja mata wannan la’ana. Mu’awiyya kuwa, Allah ya ƙara masa yarda, shi ne uban masu laifi, a ganin ƴan Shi’a, domin shi ya yaƙi Ali kuma ya tankwaɓe masa khilafa a bayan da ya same ta. Kuma wannan babban laifi nasa shi ya shafi mahaifiyarsa, Hindu. Ummul Hakam, kakar Marwan binul Hakam, ƴan Shi’a suna ɗauka cewa jikanta, Marwan, shi ne ya zuga Usmanu ya yi gaba da Ali. Kuma ga shi jikokinsa sun yi ta more mulki, suka hana jikokin Ali ɗanawa. Su kuwa Yazid da Ibnu Ziyad da Ibnu Sa’ad su suka kashe Hussaini(RA). Wannan ita ce aƙidar ƴan Shi’a da fahimtarsu, kuma ita ta sa suke la’antar waɗannan manyan bayin Allah ba dare ba rana. [Domin darasun ra’ayin Ahalus Sunna dangane da wannan aƙida da fahimta ta Rafilawa, sai mai karatu ya nemi littafan Kaddara Ta Riga Fata na Muhammad Mansur Ibrahim da Wa Ya Kashe Hussaini? na Umar Labdo].

To sai dai shin ko mai karatu ya san don me aka yi ma Umar (RA) luguden tsinuwa da la’ana a cikin wannan addu’ar? Me ya sa aka fara la’anar da shi, kuma aka yi ta maimaita sunansa tare da sauran? Amsar wannan tambaya dogon labari ne, amma muna iya taƙaice shi da cewa, a cikin Sahabban Annabi kaf, kai a cikin wannan al’umma duka, kai a cikin bil Adama baki ɗaya tun daga Annabi Adamu har ya zuwa yau, kai a cikin halitta dukkaninta, mutum da aljan, ba wanda ƴan Shi’a suka fi ƙi kamar Sayyidina Umar, Allah ya ƙara masa yarda. [Duba abinda suka fadi dangane da shi a cikin littafinmu Bacin Tafarkin ƴan Shi’a]. Don me? Saboda ya rushe daular kakanninsu Majusawan Farisa, ya maye makwafinta da daular Musulunci. Wannan shi ne laifinsa wanda ƴan Shi’a ba za su taɓa yafe masa ba har abada!  


•••═══ ༻✿༺═══ •••
 - JERIN LITTAFAN SHI’A NA 5: "Matsayin Musulmi a wajen Ƴan Shi’a" - na Prof. Umar Labɗo

✍ *AnnasihaTv* 

- Ga masu son siyen littafan da ma wasu littafan Prof sai su tuntuɓe mu kamar haka;

Call/WhatsApp: 08142286718

Twitter: https://twitter.com/AnnasihaTv?s=09
Post a Comment (0)