MATSAYIN AHALUL BAITI A WAJEN AHALUS SUNNA
Ahalus Sunna suna ɗaukar Ahalul Baiti a matsayin Musulmi na gari, masu baiwa da ɗaukaka, waɗanda Allah ya zaɓe su, ya keɓance su da falala da baiwa saboda kusancinsu da Annabi(SAW). Saboda haka suna girmama su irin girman da ya cancance su a Shari’a, ba tare da azarɓaɓi ko wuce gona da iri ba, kuma suna ƙaunar su saboda sonsu son Annabi ne, kuma son Annabi son Allah ne.
Waɗanda suke a cikinsu Sahabbai ne, kamar Ali da Faɗima da Hassan da Hussaini da Aisha da Hafsa da Abbas da ɗansa Abdullahi, da Ja’afar da Aƙilu da sauransu, to waɗannan suna ba su daraja biyu: kasancewarsu Sahabbai kuma kasancewarsu Ahalul Baiti. Waɗanda kuma ba Sahabbai ba ne, ba su rayu tare da Annabi ba, kamar sauran ƴaƴan Faɗima ƙanana Ruƙayya da Ummu Kulthum, da sauran ƴaƴan Ali waɗanda ya haifa da wasu matan nasa dabam, irin su Muhammad binul Hanafiyya da ƴan uwansa, da sauran zuri’o’in baffanin Annabi (SAW) da ƴan uwansa: zuri’ar Abbas, zuri’ar Hamza, zuri’ar Aƙilu, zuri’ar Ja’afar, da sauransu, to waɗannan ana ba su darajarsu da Allah ya ba su ta kusanci ga Annabi (SAW) da haɗa dangantakar jini da shi. Haka nan kuma, Ahalus Sunna suna yin salati ga Ahalul Baiti tare da Annabi (SAW) a duk sa’ad da suka yi masa salati.
Ahalus Sunna suna son Ahalul Baiti so irin na Musulunci, so na Shari’a, ba so na jahiliyya ba. Saboda haka, ba sa wuce makaɗi da rawa a wajen ƙaunar su da girmama su. Ba sa dangana musu almarori, ko su ƙudure cewa suna da wani kayan gado na annabta wanda suka keɓanta da shi koma bayan sauran Musulmi, ko su ce sun san gaibu, ko kuma su kaɗai suka cancanci khilafa, da sauran irin waɗannan ƙudure-ƙudure na masu addini da jahilci ko son zuciya. A wajen mu’amala da Ahalul Baiti, Ahalus Sunna suna tsayawa a kan koyarwar Alƙur’ani da Sunna, ba sa wucewa ko taƙi ɗaya.
Haƙƙoƙin Ahalul Baiti a kan Musulmi
Ahalus Sunna suna ƙudure cewa, Ahalul Baiti Allah ya ƙara musu yarda baki ɗaya, suna da haƙƙoƙi a kan ko wane Musulmi waɗanda yake wajibi ne a kiyaye da su, kuma a bayar da su ta fuskar da ta kamata. Waɗan nan haƙƙoƙi sun haɗa da:
1. Ƙaunar su da jiɓintar su da ba su girma, saboda faɗin Allah Maɗaukaki, “Ka ce (ya Muhammad): Ba na tambayar ku wata ijara a kansa (iyar da aike), face dai soyayya ta cikin zumunta.” (Suratush Shura: 23) Ibnu Kathir ya bayyana cewa, daga cikin ma’anonin ayar tana nufin, “Ku so ni ta hanyar son makusantana. Watau ku kyautata musu.” Kuma ya dangana ruwayar haka ga Imam Bukhari. [Duba Tafsiru Ibni Kathir na Abul Fida Isma’il binu Kathir, bugun Maktabatus Safa, Alƙahira, 1423/2002, mujalladi na 7, shafi na 123].
2. Yin salati a gare su tare da Annabi(SAW), watau haɗawa da su a salati duk sa’ad da aka yi masa. Kuma ana iya yin salati ga ɗayansu yayin da aka ambace shi shi kaɗai.
3. Ba su kaso daga khumusi (watau kashi ɗaya bisa biyar) na ganima, saboda faɗin Allah Maɗaukaki, “Kuma ku sani cewa, abin da kuka sami ganima daga wani abu, to, lalle ne Allah yana da humusinsa kuma don Manzo, kuma saboda masu zumunta.” (Suratul Anfali: 41) Ibnu Kathir ya ce malamai masu yawa suna ganin kason masu zumunta ana ba da shi ga Banu Hashim da Banul Muɗɗalib. [Duba Tafsiru Ibni Kathir, mujalladi na 4, shafi na 37].
4. Ƙuduri mai ƙarfi da cewa nasabar Annabi(SAW) ita ce mafi ɗaukakar nasaba, kuma danginsa su ne mafi darajar dangi.
5. Kare su da tsare mutuncinsu da kuɓutar da su daga ƙarerayin da aka laƙa musu a bisa jahilci ko son zuciya. Misali irin ƙarerayin da malaman Shi’a suke laƙa musu na abubuwan da suka saɓa da abinda kakansu, Manzon Allah (SAW), ya zo da shi na haske da shiriya dake cikin Ƙur’ani da Sunnah.
Muhimmyar Faɗakarwa: Waɗan nan haƙƙoƙi da aka ambata suna tabbata da sharuɗɗa biyu: Musulunci da tabbatar nasaba. Watau mutum sai nasabarsa ta tabbata cewa ya haɗa jini da Annabi(SAW), kuma ya karɓi Musulunci sa’an nan yake cancantar waɗan nan haƙƙoƙi.
•••═══ ༻✿༺═══ •••
- *JERIN LITTAFAN SHI’A* NA 5: "Ahalul Baiti a mahangar Ƴan Shi’a da Ahalus Sunna" - na Prof. Umar Labɗo
✍ AnnasihaTv
Call/WhatsApp: 08142286718