MATSAYIN AHALUL BAITI A WAJEN ƳAN SHI’A

MATSAYIN AHALUL BAITI A WAJEN ƳAN SHI’A  




A wajen ƴan Shi’a, Ahalul Baiti, kamar yadda suka fahimce su, su kaɗai su ne Musulmi kuma babu mai zama Musulmi sai wanda yake son su kuma yake jiɓintar su, jiɓinta da so waɗanda suka dace da fahimtar Rafilawa. A kan wannan ne suka gina aƙidarsu cewa Sahabbai duka sun yi ridda bayan rasuwar Annabi (SAW) sai mutum bakwai kawai. Waɗannan mutane su ne Miƙdad binul Aswad, Abu Zarrin Algifari, Salman Alfarisi, Ammar binu Yasir, Abu Sasan Al’ansari, Huzaifa binul Yaman da Abu Amra, Allah ya ƙara musu yarda. [A duba babin Akidar ƴan Shi’a dangane da Sahabbai a cikin littafinmu Bacin Tafarkin ƴan Shi’a da Akidojinsu]. Waɗannan Sahabbai bakwai da ƴan Shi’a suka yarda da Musuluncinsu, babu abinda ya raba su da sauran Sahabbai ƴan uwansu sai kawai cewa sun yi ƙaurin suna da kasancewa su masoyan Ali binu Abi Ɗalib ne kuma sun goyi bayansa a rikicin da ya faru tsakaninsa da Mu’awiyya binu Abi Sufyan. Wannan yana nuna cewa, a ganin ƴan Shi’a, ba Musulmi sai Ahalul Baiti, sai kuma waɗanda suka bi su, suka jiɓince su. Don haka ne suka sanya imani da imamai a matsayin ɗaya daga shika-shikan Musulunci. Babban malamin Hadisi a wajen ƴan Shi’a, Muhammad binu Ya’aƙub Alkulaini, ya ruwaito Abu Ja’afar, imamin Rafilawa na shida, yana cewa: “An gina Musulunci a kan abubuwa guda biyar: sallah da zakka da hajji da azumi da wilaya (watau imama).” [Usulul Kafi na Muhammad binu Ya’aƙub Alkulaini, bugun Darul Kutubil Islamiyya, Teheran-Iran, ba tarihi, mujalladi na 2, shafi na 18]. Idan mai karatu ya kula zai ga cewa, a cikin wannan ruwaya ta ƴan Shi’a imama ta maye makwafin Kalmar Shahada wacce ba’a ambace ta ba. To imama, a wajen ƴan Shi’a, ita ce Kalmar Shahada kuma sun kawo ambatonta a ƙarshe domin ɓad da bami.        

Don haka, matsayin Ahalul Baiti a wajen Rafilawa ya wuce a ce wai su zaɓaɓɓu ne, ko masu girma, ko masu falala a addini. A’a, sun wuce nan! Ahalul Baiti a wajen ƴan Shi’a su ne addinin kansa. Don su aka halicci duniya da lahira, suna sama da annabawa da manzanni da mala’iku makusanta, don haka ya wajaba a bauta musu. Wannan zai bayyana a fili idan muka yi darasun matsayin imamai a wajen Rafilawa. 



•••═══ ༻✿༺═══ •••
 - JERIN LITTAFAN SHI’A NA 5: "Ahalul Baiti a mahangar Ƴan Shi’a da Ahalus Sunna" - na Prof. Umar Labɗo

✍ *AnnasihaTv* 

- Ga masu son siyen littafan da ma wasu littafan Prof sai su tuntuɓe mu kamar haka;

 *Call/WhatsApp* : 08142286718

 *Twitter* : https://twitter.com/AnnasihaTv?s=09
Post a Comment (0)