MATSAYIN IMAMAI A WAJEN ƳAN SHI’A

MATSAYIN IMAMAI A WAJEN ƳAN SHI’A 




Matsayin imamai a wajen ƴan Shi’a babu sama da shi, domin suna aza su a bisa da annabawa da manzanni, kuma a wani yayi su ba su sifofin allantaka.  
ƴan Shi’a suna ɗaukar imamai a matsayin ma’asumai, waɗanda ba sa kuskure kuma ba sa aikata zunubai ƙanana ko manya, kamar annabawa da manzanni ba bambanci. Saboda haka, ba sa mantuwa, ba sa tuntuɓe, ba sa sha’afa, ba sa rafkanuwa. Dangane da wannan, wani babban malaminsu da ake kira Muhammad binu Nu’uman Almufid, yana faɗin, “Lalle imamai waɗanda suke tsaye matsayin annabawa wajen zartar da hukunce-hukunce da tsai da haddoji da tsare shari’o’i da ladabtar da talikai ma’asumai ne kamar ismar annabawa, kuma bai yiwuwa su yi rafkanuwa a cikin wani lamari na addini, kuma ba sa mance wani abu na hukunce-hukunce.” [A duba Awa’ilul Makalat na Muhammad binu Nu’uman Almufid, bugun Darul Kitabil Islami, Bairut, 1403/1983, shafi na 71-72]. Wani malamin nasu mai suna Abu Ja’afar Muhammad binu Ali binu Hussain binu Musa binu Babawaihi Alƙummi (wanda aka fi sani da laƙabin Assaduƙ) yana cewa, “Ƙudurinmu dangane da annabawa da manzanni da imamai shi ne cewa su ma’asumai ne, tsarkaka ne daga dukkan wani datti. Kuma cewa su ba sa aikata zunubi ƙarami ko babba, kuma ba sa saɓawa Allah abinda ya umarce su kuma suna aikata abinda aka umarce su. Wanda ya kore musu isma dangane da wani abu na lamarinsu to haƙiƙa ya jahilce su, kuma wanda ya jahilce su to shi kafiri ne.” [A duba Aka’idul Ithnai Ashariyya na Ibrahim Almusawi Alzanjani, bugun Muassasatul Wafa, Bairut, ba tarihi, mujalladi na 2, shafi na 157].
ƴan Shi’a Rafilawa suna ƙudure cewa imamansu sun san gaibu, kuma suna da sanin abinda ya faru tun farkon halitta da abinda zai faru har zuwa ranar Alƙiyama. Malaminsu Kulaini ya ruwaito daga imaminsu na shida, Abu Abdillahi, ya ce, “Na rantse da Ubangijin Ka’aba, na rantse da Ubangijin wannan ginin (Ka’aba) -ya maimaita sau uku- da na kasance tare da (Annabi) Musa da Haliru da na faɗa musu cewa ni na fi su sani, da na ba su labarin abinda ba su sani ba; domin Musa da Haliru (AS) an ba su sanin abinda ya kasance ne (kawai) amma ba’a ba su sanin abinda zai zo da abinda zai kasance ba har zuwa ranar Alƙiyama. Mu kuwa (watau imamai) mun gaji wannan ilmi daga Manzon Allah gado na haƙiƙa.” [Usulul Kafi na Muhammad binu Ya’aƙub Alkulaini, mujalladi na 1, shafi na 261]. Malaminsu, Muhammad binu Nu’uman Almufid, ya tabbatar da wannan aƙida tasu. Ya ce, “Imamai daga zuri’ar (Annabi) Muhammad (SAW) sun kasance suna sanin abinda yake ɓoye cikin zukatan wasu bayi, kuma sun san abinda zai kasance kafin kasancewarsa.” [Awa’ilul Makalat na Muhammad binu Nu’uman Almufid, shafi na 75].
ƴan Shi’a suna ƙudure cewa wahayi yana sauka ga imamansu. Domin tabbatar da haka, sun ruwaito daga imaminsu Abu Abdillahi, ya ce, “Mu ana ba mu guzuri (na ilmi) dare da rana, kuma ba don ana ba mu guzuri ba da abinda yake gare mu (na ilmi) ya ƙare. (Mai ruwaya) Abu Basir ya ce: Allah ya sanya ni fansar ka, wane ne yake zuwa muku? Ya ce: Daga cikinmu akwai wanda yake gani da ido ƙuru-ƙuru; daga cikinmu akwai wanda yake ji da kunnensa amo kamar amon sarƙa a cikin tasa. (Mai ruwaya) ya ce: Na ce: Allah ya sanya ni fansarka, waye yake zuwa muku da wannan? Ya ce: Wani halitta ne wanda ya fi Jibirilu girma.” [Biharul Anwar na Muhammad Baƙir Almajalisi, bugun Muassasatul Wafa, Bairut, ba tarihi, mujallaadi na 26, shafi na 53].  Mai karatu yana iya gani cewa wannan ruwaya ba ta bar wani yanayi na saukar wahayi ga annabawa da manzanni ba face ta tabbatar da shi ga imamai. 
 
 

•••═══ ༻✿༺═══ •••
 - JERIN LITTAFAN SHI’A NA 5: " ```Ahalul Baiti a mahangar Ƴan Shi’a da Ahalus Sunna```" - na Prof. Umar Labɗo

 *✍ AnnasihaTv* 

- Ga masu son siyen littafan da ma wasu littafan Prof sai su tuntuɓe mu kamar haka;

 *Call/WhatsApp:* 08142286718

 *Twitter:* https://twitter.com/AnnasihaTv?s=09
Post a Comment (0)