DALILAN YAƊUWAR SHI’A A NIJERIYA [4]

DALILAN YAƊUWAR SHI’A A NIJERIYA [4]


 

Akwai dalilai masu yawa da suka taimaka wajen yaɗuwar tafarkin Rafilanci a nan ƙasar. Za mu duba muhimmai daga cikinsu [Dalili na farko ya gabata]. 

 Dalili na Biyu: Jahilci   

A yayin da malamai suka gaza sai jahilci ya samu filin baje koli. Juyin juya hali na ƙasar Iran ya faranta ran al’ummar Musulmi ganin yadda tutar Musulunci ta ɗaukaka da yadda daular kafirci mafi girma, Amurka, ta kunyata. Wannan ya sa Musulmi da yawa suka sha’afa da aƙidar mutanen Iran a lokacin da suka riƙa duban su a matsayin wani abin koyi da ya kamata kowa ya yi koyi da su. Da yawa daga Musulmi sun zaci cewa bajintar mutanen Iran da nasarar da suka samu ta ƴantar da kansu daga zaluncin Amurkawa da danniyar Turawan yammacin duniya baki ɗaya, sanadinta shi ne aƙidar Rafilanci da suka ƙudure. Wasu jahilai kuma suka riƙa zaton cewa munafunci da suke gani a wurin wasu sarakai da shugabannin ƙasashen Musulmi masu bin tafarkin Sunna tushensa shi ne aƙidarsu ta Sunna wace babu bore, ba gwagwarmaya, kuma babu ƙundumbala a cikinta. Wannan sai ya sa Musulmi da yawa, musamman matasa, masu tsananin son Musulunci da ƙin kafirci da jin takaicin halin ƙasƙanci da koma baya da al’umma suke ciki, suka riƙa ganin sun sami mafita a cikin koyi da mutanen Iran. 

 Wani abu da ya ƙara wa mutanen Iran farin jini da haiba a idanun Musulumi waɗanda zukatansu suke cike da son Musulunci amma ƙwaƙwalensu wayam, shi ne wasu kalmomi masu ƙyalli da ƙyal-ƙyali da suka riƙa amfani da su kamar gwagwarmaya, barranta daga ɗagutai, gogayya da kafircin duniya, yaƙi da waɗanda suka kangarewa Allah Ta’ala, fatattaƙar Yahudawa da ƴanto masallacin Baitul Maƙdis, kafa jumhuriyar Islama, yin shahada wajen ɗaukaka addinin Allah, da irin waɗan nan kalmomin take da kirari waɗanda Rafilawa suka yi ta burgewa da su. 

 Ga alama irin waɗan nan kalmomi su suka burge Zakzaki da maƙarrabansa inda suka yi ta maimaita su kamar yadda akun kuturu take kyaikwayon abinda aka gaya mata ba tare da ta san ma’anarsa ba. Da waɗan nan kalmomi su ma suka ja gayya, inda komai na Iran ya zama abin yayi, kama daga babbaƙun rawunansu zuwa manyan alkebbunsu, kai har da sunayensu da laƙabansu, da tafiyarsu da maganarsu. Hotunansu da jaridunsu da mujallunsu da uwa uba littafansu suka cika ko ina. A cikin wannan ruɗu, mugunyar aƙidarsu ta yi saraf ta shige ƙwaƙwalen dake haihai. Da haka ne Shi’a ta yaɗu a Nijeriya a ƙarƙashin inuwar gazawar malamai da gafalarsu. 


•••═══ ༻✿༺═══ •••
 - JERIN LITTAFAN SHI’A NA 7: ```"Zuwan Shi’a Nijeria"``` - na Prof. Umar Labɗo

 *✍ AnnasihaTv* 

- Masu son siyen littafan da ma wasu littafan Prof sai su tuntuɓe mu kamar haka;

 *Call/WhatsApp:* 08063836963

 *Twitter:* https://twitter.com/AnnasihaTv?s=09
Post a Comment (0)