Mugun nufin ƴan Shi’a ga Al’umma



بسم الله الرحمن الرحيم 
 GABATARWA  

Ƴan Shi’a suna da baƙin tarihi wanda yake cike da ta’addanci da rura wutar fitina tsakanin Musulmi da taimakon kafirai a kansu wajen yaƙar su da cinye ƙasashensu, domin su, kamar yadda Ibnu Taimiya yake faɗi, “A koda yaushe suna neman taimako da kafirai da fajirai wajen biyan buƙatunsu kamar yadda suke taimakon kafirai da fajirai wajen biyan nasu buƙatun.” *_[Minhajus Sunna na Ibnu Taimiyya, bugun Darul Kutubil Ilmiyya, Bairut, ba tarihi, mujalladi na 2 shafi na 195]._* Wannan shi ne halin Rafilawa a tsawon tarihinsu, a ko wane zamani, kuma a ko wane wuri.    
A nan Nijeriya, an ruwaito madugunsu, Ibrahim Yaƙub Alzakzaki, yana faɗa wa Kiristoci, waɗanda yake gayyata wajen Maulidinsa: “Ba da ku muke faɗa ba,” yana nufin su da Musulmi suke yaƙi; ba da kafirai ba. Su kafirai abokan tafiya ne; saboda haka Kiristoci suke halartar Maulidin Ƴan Shi’a, inda suke ɗaga Kuros, watau suna nuna alamar addininsu a fili ba a ɓoyewa.   
Baƙin tarihin ƴan Shi’a aiwatarwa ne ga miyagun aƙidojinsu na ƙiyayya da gaba ga Ahalus Sunna, da ma duk wani Musulmi wanda ba ya bin tafarkinsu. Malaman Shi’a suna ƙoƙarin cusa gaba da ƙiyayya da mugun nufi a zukatan mabiyansu ta hanyar ruwayoyin ƙarya da suke dangana wa Imamansu, waɗanda suke nuna halaccin jinin duk wanda ba ɗan Shi’a ba, [Duba littafinmu, Matsayin Musulmi a wajen ƴan Shi’a]. da yin albishir da mummunar makomar da take jiran sa.   
 A wannan taƙaitaccen littafi, za mu fara da bayanin mugun nufin ƴan Shi’a ga al’umma kamar yadda yake a cikin aƙidunsu da littafan manyan malamansu. Sa’an nan daga bisani mu kawo misalai na baƙin tarihinsu wanda yake tabbatar da ƙaddamar da wannan mugun nufi a aikace.    

 - JERIN LITTAFAN SHI’A NA 7: " ```Mugun nufin ƴan Shi’a ga Al’umma```" - na Prof. Umar Labɗo

 ✍ AnnasihaTv 

- Masu son siyen littafan da ma wasu littafan Prof sai su tuntuɓe mu kamar haka;

 Call/WhatsApp: 08063836963

 Twitter : https://twitter.com/AnnasihaTv?s=09
Post a Comment (0)