Labarin yarinyar da kowa ke so

Labarin yarinyar da kowa ke so




 An ce: Wani yaro ya ce wa mahaifinsa: Ina so in auri wata yarinya da na gani, kuma ina son ta ne saboda kyawunta da kwarjin idanunta.
 Sai ya amsa masa yana mai farin ciki da jin dadi ya ce: Ina wannan yarinyar take baban yace yana son yaga yar wane gida ce?

 Da suka je sai baban ya ga wannan yarinya sai ya yaba da kyawunta, ya ce wa dansa: Ka ji yarona, yarinyar nan bata dace da kai ba, kai kuma ba ka dace da ita ba, wannan ta cancanci a Aura mata mutum irina wanda ya kware a rayuwa.

 Yaron ya yi mamakin maganar mahaifinsa, ya ce masa: A’a, amma zan aure ta a hakan baba, ba kai ba.

 Suka yi gardama, suka je ofishin ’yan sanda don warware matsalar, da suka ba wa jami’in labarinsu, sai ya ce musu: Ku kawo yarinyar mu tambaye ta wanda take so, yaron ko uba.

 Da hafsa ya ganta sai ya yi mamakin kyawunta da kwarjininta, sai ya ce musu: Wannan bata dace da ku ba, sai dai ga wani fitaccen mutum a kasar nan kamar ni.

 Sai su uku suka yi rigima, suka je wajen waziri dan ya warware tsakaninsu, sai da waziri ya ganta, Sai waziri ya ce: “wannan irina na kawai ya kamata ta aura, nan ma suka yi ta rigima har sai da lamarin ya kai ga sarkin garin.

 Da suka zo sai ya ce: Ni zan warware muku matsalar, Ku ku kawo yarinyar, da sarki ya gan ta, sai ya ce: Basarake kamar ni ne kawai zai aure ta, ni kuma zan aure ta. Duk suka yi sabani, suka yi gardama.

 Yarinyar ta ce, "Ina da mafita!"

 Zan gudu, ku bi ni, duk wanda ya fara kama ni zan zama rabonsa, ya aure ni, ta gudu, kowa ya bi ta, saurayi, da uba, da hafsa, da waziri, da basarake. , suna bin ta da gudu su biyar suka fada cikin wani rami mai zurfi.

 Sai yarinyar ta dube su daga sama ta ce: Kun san ko ni wace ce?

 Nice duniya!!!!

 Ni ce duk mutanen da ke gudu a bayana suna tsere don samun na
 Suna shagaltar da kansu daga addininsu, suna bina har sai sun fada cikin kabari ba za su rabauta da ni ba?
Post a Comment (0)