TAFIN HANNU BAYA TARE HASKEN RANA

TAFIN HANNU BAYA TARE HASKEN RANA




Dan Adam kowa akan qaddarar sa zai rayu, don haka muna hakuri a mu'amala da yiwa Juna uzuri da zaton alheri

Wasu sun ɗauka a rayuwa su kaɗai ne suka fi cancanta da ɗaukaka da ni'imar ALLAH

A duk lokacin da ALLAH Yayi ɗaukaka da ni'imarsa ga wani bawan sa sai su shiga ƙuncin zuciya da damuwa har a fuskokinsu

Bayin Allah mu sani duk Wanda ya dogara ga Allah ya isar masa, don haka Sam kar ka waiwaya ka dubi masu Maka wani kulle kulle da makirci da kiyayya, ba Mai iya kwace rabon ka, ko canza qaddarar ka

In kana tsoron Allah kowa sai ya ji tsoron ka kuma ba yadda suka iya da Kai, Amma in baka tsoron Allah to komi sai yana baka tsoro

Allah ya bamu dacewa duniya da lahira, amin 

Mu dage da Addu'a, da mayar da komi ga Allah da nisantar sa6on Allah

#Zauranmukarudajuna
Post a Comment (0)