KARIN KUMALLO...!!! INA FARIN CIKINA YA TAFI?

KARIN KUMALLO...!!!
INA FARIN CIKINA YA TAFI? 



Wani lokaci sai ka ji farin cikinka ya ragu kamar an kewaye zuciyarka da damuwa. Amma kuma ka rasa takamammen dalilin haka. Babu mamaki dalilin shi ne: 
1. Wani aikin alheri ne da ka saba yi lokacinsa ya yi amma baka yi ba.
2. Sakaci ne da sallar jam'i musamman asuba.
3. Qarancin ganawa da mahalicci.
4. Zumuncinka da qur'ani ne ya ragu.
5. Harshenka ne bai jiqewa da zikiri.
6. Salatinka ga Manzo S.A.W yai qaranci.
7. Qarancin sadaka da faranta wa bayin Allah rai. 

Zai yi wahala mai kula da wadannan ya samu kanshi a cikin qunci. Allah Ka kawo mana farin cikin duniya da lahira. Ameen. 

✍️ Muktar Mustapha

Post a Comment (0)