SATI UKU MIJINA BAYA KULANI, SAI NAKE KIRAN SAURAYINA AWAYA MUNA DEBEWA JUNA KEWA
HISNUL-MUSLIM
TAMBAYA
Assalamu alaikum MALAM Dan Allah gatambaya MALAM kanwatace wanisabani yashiga tsakaninta damijinta MALAM adalilin tagayamai gaskiya akan wani abudayake Wanda baidaceba taimai nasiha yajitsoran Allah yadaina shine yake fishida ita bayacin abincinta bayamata magana bayakusantarta kumata bashi hakuri akanbatai randatai yau sati ukku kenan sunahaka MALAM kokiranshi tai awayabaya dauka towannan kuncin datakeciki haryakai tastani mijinnata bata kaunarshi yanzo todama akwaitsohon saurayinta tanada lambarshi shine takekiranshi sunawa dantadebe kewar bakincikin datakeciki hartana tunanin tanemi saki gurin mijinta dantaje ta aurishi wancan saurayinnata shine takeneman shawara Dan Allah ataimakamata ngd.
AMSA
To abinda mujin yayi baikyautaba indai ayanda tambayar tazo haka abin yake azahiri to hakika tafishi gaskiya domin tsakanin mace da miji akwai shawara da wa'azi da nasiha da kowa yake da hakkin yayiwa abokin zaman alokacinda yadace
Sannan kaurace mata dayayi wannan sabawa dokar Allah ne dayasan uqubar da Allah yatanada akan abinda yayi dabai aikataba lallai yaji tsoran Allah yadawo gareta tareda neman afuwarta
To itakuma matakinda tadauka baikamataba itama haramunne abinda tayi tasabawa Allah taketare dokar Allah lallai inaso tasani yanzu zunubinda take dauka yafi wanda yake dauka kamar zina takeyi domin zina kala kala ce munyi bayanin cewa akwai zinar baki akwai ta ido akwai ta hannu akwai takafa akwaita farji to koshakka babu tayi kuskure
Anan kuma ni Abusalmah inaso nace wani abu "wato dagajin matakinda tadauka kasan cewa itama dama bamai tsoran Allah bace to wacca bata da tsoran Allah daya zatace wai tayiwa mijinta nasiha yaji tsoran Allah? Kaga wannan akwai alamar tambaya watakilama to mijin yafita gaskiya domin dana lura da tambayar sosai sainaga dama gashi alrady tanada lambar saurayinta to akanme take ajiye da lambar saurayinta? Maye yake tabbatar mana cewa dama basa waya saiyanzu d akasamu saban? Idanma basa waya akanme take ajiye da lambar? Amsa shine dama kenan ta ajiye lambarne randa bamijinta shikenan tanada safaya daling to kuma kaji wai wacca takeda wannan halayyar itace zatace kuma wai taga mijinta yanayin abinda baikamataba tayimar wa'azi yaji tsoran Allah to yaya bazakiwa kanki wannan nasiharba matakinda kika dauka saimuka fahimci kamar kema bakya tsoran Allah din"
Shawarata anan shine lokacinda haka tafaru saiku shigar da manyanku ciki iyaye waliyai suyimuku sulhu abashi hkr adaidaita tsakaninku asamu masalaha dahaka kikai dayanzu wani zancan akeyi ba wannanba amma saikema kikadau mataki marakyau to yanzu kindau matakin sabawa Allah kuma ahakan kikeso Allah yakawo miki dauki akan wannan sabanin dakuke ciki
Lallai kuyi kokarin samun gyara maikyau Allah kuma yadaidaita tsakaninku
Allah shine masani
JUNAIDU BALA ABDULLAHI
Abu Salmah
Masu buqatan shiga Wannan Zaure na hisnul Muslim suyiwa daya daga cikin wadannan number magana ta whatsApp+2348065523065
+2348162067271
Domin Neman Karin bayani akan wata fatawa sai Ku kira wannan numbar↓
+2347065588557
سبانك اللهم وبحمدك، اشهد ان لا اله الا انت استغفرك واتوب اليك،
Kuna iya samun mu ta facebook ta wannan link indanke Qasa
https://mobile.facebook.com/Hisnul-Muslim-667684316700356/?fref=none