ABUBUWAN DA KE KAWO NUTSUWA A CIKIN ZUCIYA

*_ABUBUWAN DA SUKE KAWO  NUTSUWA A CIKIN ZUCIYA_*

                              *Tambaya*
Assalamu alaikum
Don Allah malam ta yaya zan samu nutsuwa a cikin zuciya ta?, saboda wani lokacin sai na ji zuciyata, kamar an kunna min wuta, wasu lokutan kuma bakin ciki ya hana ni bacci

                                 *Amsa*
Wa'alaykumussalam To dan'uwa akwai abubuwan da malamai suka yi bayani cewa: suna kawo nutsuwa a zuciya, ga su kamar haka:

1. Cikakken tauhidi, ta yadda mutum zai bar duk wata shirka da bidi'a da abin da yake kaiwa zuwa gare su.

2. Shiriya da hasken da Allah yake jefawa a zuciyar bawa, wanda duk lokacin da aka rasa shi, sai bawa ya kasance cikin kunci.

3. Ilimi mai amfani, saboda duk lokacin da ilimin mutum ya yalwata, zai samu jindadi a zuciyarsa.

4. Dawwama akan zikirin Allah, saboda fadin Allah "Wadanda suka yi imani zuciyoyinsu suna nutsuwa da zikirin Allah" Suratu Arra'ad aya ta 28

5. Kyautatawa bayin Allah, saboda duk mutumin da yake yin kyauta zai kasance cikin kwanciyar hankali, kamar yadda marowaci yake  kasancewa cikin kunci.

6. Fitar da kyashi da hassada daga zuciya.

7. Barin kallo da zancen da ba shi da fa'ida.

8. Barin baccin da ba shi da amfani.

9. Cin abinci gwargwadon bukata, da rashin karawa akan haka.

10. Rashin cakuduwa da mutane sai gwargwadon bukata.

Kishiyoyin wadannan abubuwa su ne suke  jawo bakin ciki da damuwa da kuma kunci.

Don neman karin bayani duba zadul-ma'ad  2\22

Allah ne mafi sani

17/8/2014

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren MIFTAHUL ILMI (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Post a Comment (0)