*_HUKUNCIN MIJIN DA MATARSA TA NEME SHI DA JIMA'I BAI AMSA MATA BA_*
*Tambaya:*
malam ina roko a taimaka min da amsar tambayata, malam na san idan miji ya nemi matar sa don saduwa ita kuma ta ki, ta aikata babban zunubi, to idan mace ta nemi mijin ta shi kuma yaki, shi ma ya aikata zunubi ne ko ko?
*Amsa*
To dan'uwa hadisi ya tabbata daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi cewa "Idan miji ya kira matarsa zuwa shimfidarsa ba ta amsa masa ba, to mala'iku za su tsine mata har ta wayi gari" kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 1436.
Sai dai abin da malamai suke cewa shi ne: namiji ba shi da laifi, idan matarsa ta neme shi bai amsa mata ba mutukar ba da nufin cutar da ita ya yi hakan ba, domin namiji da mace sun bambanta, saboda mace za'a iya saduwa da ita ko da ba ta da sha'awa, namiji kuwa sai yana da sha'awa, zai iya saduwa, don haka akwai bukatar ace yana da nishadi kafin ya iya jima'i, idan haka ne kuwa ba zai yiwu ya sadu da mace ba duk sanda take so ba, Allah kuma ba ya dorawa rai sai abin da za ta iya, sannan sha'awar maza ta fi ta mata karfi, saboda haka yawanci namiji ne yake neman matarsa ba akasin haka ba.
Allah ne ma fi sani.
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren MIFTAHUL ILMI (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.