*_HUKUNCIN FADIN "BALAA" A KARSHEN SURATU ATTIN_*
*Tambaya*
Assalam alaikum warahmatallah Malam dafatan kana lafiya amin. Malam akwai addua da akeyi a yayin da aka karanta Suratin Tin a karshen surar wato "Balaa nahanu ala zalika laminash shahideen". Ya ingancin wannan addua yake? Wassalam Allah ya kara lafiya.
*Amsa*
Wa'alaikum assalam, akwai hadisin da Abu-dawud ya rawaito mai lamba ta (887) wanda ya tabbatar da hakan, saidai malaman hadisi sun raunana shi kamar Nawawy a cikin Al-majmu'ú 3/563.
Saidai wasu daga cikin malaman Malikiyya sun só fadin hakan in an karanta karshen Surar WATTIN, hakanan wasu a cikin Hanabila.
Allah ne mafi sani.
04/08/2017
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren MIFTAHUL ILMI (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.