*_INA RAGE GIRMAN BUHU SABODA SAMUN RIBA?_*
*Tambaya*
Assalamu Alaykum hayyakallahu ya sheik Dan Allah INA Neman sanin halaccin wannan business din , shinkafa idan an shigo da ita daga Niger ko kwatano bata da riba, to idan an kawo ta kafin akai ta kasuwa ana cire kwano daya a kowane buhu sai mutum ya tada buhunhuna to wannan ita CE ribar sa, yin hakan ya halatta ko yana cikin tauye mudu? Allah ya dawo da DR lafiya
*Amsa*
Wa'alaikum assalam, Haramcin wannan a fili yake, tun da ALMUNDAHANA ne da kuma Algus, saboda duk wanda zai saya, zai saya ne a matsayin cikakken buhu daga Niger ko kwatano.
Annabi S.A.W yana cewa a cikin hadisin da Muslim ya rawaito "Duk wanda ya yi mana Algus ba ya cikinmu".
Ayoyin farko na Suratul Mudaffifina Sun yi bayanin azabar da Allah ya tanadarwa Masu tauye mudu.
Wanda ya kiyaye dokokin Allah zai kiyaye shi, wanda ya saba masa zai hadu da shi a madakata.
Babu wata wadata da Allah zai yiwa mutum fiye da hakuri da Kuma wadatar zuci.
Allah ya hallakar da Al'umar Annabi Shuaibu saboda tauye mudu kamar yadda kissoshinsu suka zo a Suratul A'ARAF da suratu HUD da SHU'ARA'I haka nan Ankabuti.
Allah ne mafi sani
27/08/2017
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren MIFTAHUL ILMI (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.