YA TURA WANI GIDAN BOKA BAI SANI BA

*_YA TURA WANI GIDAN BOKA BAI SANI BA?_*

                               *Tambaya*
Assalamu Alaikum
Dr, nine wani ya faka a motor dinshi sai ya tambaye ne shin na san gidan wani mutumi sai nayi mishi kwatance sai daga baya na tuna gidan boka zai je, meye hukuncin wanda ya yi hakan?

Allah ya sakawa malan da gidan aljannah fiddausi

                                 *Amsa*
Wa'alaikum assalam, Mutukar ba da saninsa ba ya nuna masa, Allah ba zai kama shi da laifin hakan ba, saboda Allah ya yiwa al'umar Annabi Muhammad S.A.W afuwa cikin abin da suka aikata da kuskure ko mantuwa kamar yadda ayar karshe a suratul Bakara ta tabbatar da hakan.

Allah ne mafi sani

11/10/2017

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren MIFTAHUL ILMI (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Post a Comment (0)