BADA GIDAN HAYA GA MASU BAUTAR COCI?
Tambaya?
Assalamu Alaikum.
Malam dan Allah miye matsayin Musulmi da ya gina hotel kuma yana baiwa kafirai haya suyi choci?
Amsa:
Wa alaikum assalam, Bai halatta ba, saboda Allah madaukakin sarki ya hana taimakawa mai aikin sabo. Aya ta biyu a cikin suratul Ma'ida tana cewa: "Kuma ku dinga tamakekeniya wajan aikata alkairi, Amma kada ku yi tamakekeniya wajan aikata sabo". Ibadar COCI shirka ce kamar yadda ayoyi da yawa a suratul Ma'ida suka siffanta Wanda yake bautawa annabi Isa da kafiri.
Allah Ne mafi Sani.
Dr Jamilu Zarewa
16/08/2016
Tags:
Tambaya Mabudin Ilimi