*_HUKUNCIN WANDA YA AURI MACE SABODA KYANTA??_*
*Tambaya*
Malam : Akwai wani hadisi da yake Magana kan cewa kowa ya auri mace kawai dan kyanta Allah zai hana masa jindadin kyan, ko dan kudinta kawai Allah zai hana masa jin dadin kudin,.... shin kuwa hadisin akwai shi kuma ya inganta?
*Amsa*
Ga Yadda Hadisin yake: Duk Wanda ya Auri Mace saboda kudinta, Allah zai kara masa Talauci, duk Wanda ya Auri Mace saboda kyawunta Allah zai kara masa muni.
Saidai a cikin hadisin akwai Abdussalam bn Abdulkuddus wanda yake rawaito hadisan karya, don haka hadisin bai inganta ba, kuma ba za'a kafa hujja da shi ba.
Allah ne mafi sani
26/1/2014
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.