NA KARBI KYAUTA DAGA KARUWA KO YA HALATTA NA AMFANA DA ITA?

*_NA KARBI KYAUTA DAGA KARUWA, KO YA HALATTA NA AMFANA DA ITA?_*

                              *Tambaya*
Assalam,malam akwai hujjar da ta kore kar6ar kyauta daga karuwa ?

                                    *Amsa*
Wa'alaikum salam, Tabbas Annabi ﷺ ya haramta cin kudin karuwa, wanda ta samu ta hanyar karuwanci, kamar yadda hakan ya zo a hadisi mai lamba: 1567, wanda Muslim ya rawaito.

Saidai malamai suna cewa: Duk wanda ya zama a cikin dukiyarsa akwai halal da haram, to idan ya maka kyauta za ka iya amsa, mutukar ba ka tabbatar daga haram ya dauko ya baka ba, saboda Annabi ﷺ ya yi mu'amala da yahudawa kuma a cikin dukiyarsu akwai halal da haram, har ma ya mutu silkensa na yaki yana jingene a wajansu.

Don neman Karin bayan duba Al-muhallah na Ibnu Hazm 6/184.

Allah ne mafi sani

26/1/2015

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Post a Comment (0)