HUKUNCIN YIN HUDUBA GA YARON DA AKA HAIFA

*_HUKUNCIN YIN HUDUBA GA YARON DA AKA HAIFA_*

                             *Tanbaya*
Assalamu alaikum malam
DAN ALLAH INA NEMAN KARIN BAYANI AKAN HUDUBAR SUNA DA YADDA AKE YI.

                                  *Amsa*
Wa'alaikum assalamu Game da kiran sallah da ikama a kunnen yaron da aka haifa wannan bai inganta ba, saboda hadisin kiran sallah Tirmizi ya rawaito shi da sanadi mai rauni, Baihaki kuma ya rawaito shi a Shu'abul-imani sai dai a sanadinsa akwai maruwaita guda biyu wadanda ake tuhumar su da karya, amma hadisin da ya zo akan yin ikama kuwa, to malamai sun ce hadisi ne na karya.

*SAI DAI YA TABBATA A SUNNAH ANA TAUNA DABINO A SAWA YARO  A BAKI.*

Allah ne mafi sani.

31/12/2013

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Post a Comment (0)