ZINA BA TA YIN ƊA - ISTIBRA'
Wannan shine karatun Mufti Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya gabatar yau 06-01-2018 na Fiqhu in da yake karatu a cikin littafin Attalqeen Fi Fiqhil Maliky a Masjid Attauheed in da malam ya karasa bayani a cikin kasuwanci.
👉 Amma da farko sai da ya fara kawo Addu'o'i ingantattu daga Manzon Allah SAW wanda ya kamata mutum ya rika yi duk lokacin da ya ji bashi da lafiya.
👉 Akwai bayanai masu yawa sosai game da maganar *Istibra'i* - wato jini uku da ake son mace ta yi idan wani ya sadu da ita ba ta hanyar aure ba.
👉 Mene shari'a ta tanadar game da mutumin da ya aure mace bayan wata shida sai ta haihu?
👉 Shin har yanzu ana buƙatar tantance ɗa idan ana shakkar wane ne mahaifinsa na asali?
👉 Shin blood test ko DNA yana wadatarwa a shari'ar Musulunci don tabbatar da ɗa na wane ne?
👉 Shin shari'ar Musulunci ta yarda da shedar asibiti a matsayin hujja ga wanda yake zargin matarsa?
👉 Ina hukuncin mutumin da ya auri dadironsa ba tare istibra'i ba?
👉 Wace hanya za abi domin ganin an magance zubar da yara da aka same su ba ta hanyar aure ba?
👉 Idan mace an same ta ta yi ciki wane irin hukunci ne ya kamata iyaye su dauka?
👉 Shin da gaske ciki yana kwanciya har ya wuce shekara ɗaya a ciki kafin a haife shi?
👉 Wane ne ke da alhakin tabbatar da ɗa mallakin wane ne?
Wannan da ma sauran amsoshin duk a cikin wannan karatu da Malam ya gabatar.
=====
Salisu Hassan Webmaster
08038892030
06/01/2017
=====
Allah Ya saka muku da alkairi saboda kokarin sharing da kuke yi
Ga dukkan mai son samun karatukan malam ta WhatsApp ya yi saving wannan lambar a wayarsa sannan ya aiko da cikakken sunan sa da jihar da yake ta Whatsapp din sannan ya ce yana son karatun malam = 08038892030