👻 *ALJANI NE A JIKINKI //2* 👻
*ALAMOMIN ALJANI NA ZAHIRI*
👻Wainnan dama wasu suna daga cikin Alamomin da Aljani zai iya nuna kansa amma sai wanda ya san su ne zai fahimtar da ke. Aljani mugu shine wanda baya bayyana kansa balle a masa magani, wanda zai fadar dake ya tashi, ai ya nuna a masa magani kenan tun da an san dashi, mugun kuwa baya tashi sai dai ya rinka azabtar dake ta fanni iri iri. Aljani ya kan sa mutum ya rinka jin wainnan dama wainda basu ba saboda kowa akwai irin nasa Alamomin, gasu kamar haka:
👻1. Yawan ciwon kai mai tsanani da jiri.
👻2. Ciwon Mara, baya da kuma kwankwaso.
👻3. Jin motsi a gabanki kamar tana. Ko kiji motsi a cikinki yana zuwa bangare bangare.
👻4. Jin abu kamar kiyashi na bin jikinki, ko kamar tsutsa, haka nan zaki rinka jin motsi a kanki kamar wani abu na tafiya.
👻5. Jin wani abu mai dan nauyi ya kwanta a wani bangaren jikinki, wani lokacin ya tashi daga wannan wurin ya koma wani wurin.
👻6. Jin zafi ko sanyi a tafin kafarki, ko kiji wannan wurin yayi dumi kamar an sa wuta, can kuma sai ya matsa ya koma wani wurin.
👻7. Jin wani abu kamar yana hadiye ki.
👻8. Rashin son kitso ko wani abu da zai taba kanki.
👻9. Rashin barci da daddare.
👻10. Yawan faduwar gaba da tsorata da abu qanqani.
👻11. Rashin son mutane da gudun mutane, da tsoron mutane in ta shiga wurin da akwai mutane dayawa kamar kasuwa, da rashin son magana da mutane.
👻12. Yawan fushi da tsiya, kiji kowa ma haushi yake baki haka nan kiji kin tsani mutane.
👻13. Qin aure, da rashin son maza, mace taji bata son namiji yace yana sonta, ko yace zai turo gidan su, wata ma gaba daya zata ga babu mai kulata, babu mai cewa yana son ta. Ko kuma idan wani ya fito neman auren sai zancen ya lalace saurayin yace ya fasa, in shi kuma yake so sai taji ita kuma bata son shi.
👻14. Zaki rinka ji kamar ana miki magana, ana cewa ki aikata wani mugun abu, ko idan kina kallon wuqa sai kiji kamar ana cewa ki coka ma wane, ya zamana dai ba a rabaki da mugun tunani.
👻15. Yawan jin zafin jiki, kasala da kuma ciwo na rashin dalili, wato ba a rabaki da zazzabi jikinki yayi zafi, kuma ko kin sha magani baya bari.
👻16. Yawan son kade kade da raye raye, wato aljani zai rinka saki yin wasu abubuwan da da can ba halinki bane, lokaci daya sai aga kin canza kin tashi daga mutumiyar kirkin da aka sanki.
👻17. Yawan kallon madubi da yawaita kallon jikinki tsirara a madubi.
👻18. Son dare, ya zama kin fi son dare akan rana, haka nan da son zama a cikin duhu.
👻19. Jin kamar ana kiran sunanki ko firgita yayin da kike ke kadai a wuri, koma ki rinka ji kamar ana biyoki in kina tafiya, ko kamar wani abu na bin qafarki.
👻20. Yawaita kuka na rashin dalili ko rashin kuka, wasu sun ce yana daga cikin alamun aljani.
👻21. Qin karatun Qur'ani, da kasa karanta Qur'ani koma daukansa, kiji rabin kanki na miki ciwo ko wani bangare na kanki kamar zai tsage saboda tsananin ciwo, ko kuma jin bacci da kasala, kiji kamar an cire miki karfin jikinki, kuma kiyi ta hamma kina jin bacci. Ko kuma ana fara karanta Qur'ani gabanki yayi mugun fadi, kuma ki rinka ji a ranki baki so, ko kiji kamar ana tsira miki allura a kunni.
👻22. Jin kamar ana tsira miki allura a jikinki, duk da wasu sun ce alamun sihiri ne to amma aljani ma yana sawa kiji kina zaune an tsikara miki abu kamar allura har sai kin yi zunbur kin tashi.
👻23. Rashin jin dadin saduwa da tsanar miji yayin da ya nuna alamar yana son saduwa da ita, ko kuma koda yayi zata ji ita bata ji komai ba, wato dai an dauke mata sha'awa. Da kuma jin dadi yayin jima'i.
👻24. Jin kamar kin aikata wani abu ba a cikin hankalin ki ba, wato kamar kina bacci kamar kina farke.
👻25. Ganin inuwa kamar na wani, ko kiji an danneki baki numfashi, sai kin yi addu'a sannan a tashi kanki.
👻26. Yanke jiki ki fadi baki san in da kanki yake ba har aljani yayi magana, ko ki fadi ba tare da yayi magana ba, amma dai kin san baki san abun da ya faru ba.
👻27. Jin kamar an daura miki dutse a zuciyar ki, wato ki ji nauyi a ranki, ko kiji an matse miki numfashin ki, ko in kin kwanta ki kasa numfashi da kyau.
👻28. Samun ciwukan da da can baki dasu, aljani yana sawa mutum ciwo a jikinsa wanda likita zai duba ya gani wata rana kuma ace ba a gani ba, sai ka ga mace tana ta yawon neman magani bata san aljani bane ke wahalar da ita.
👻29. Yawan waswasi musamman a ibada. Da rashin son yi ibadan na gaba daya.
👻30. Rikitar miki da al'ada, yanzu zaki ganki ba jini ya dauke, sai kin yi tsarki kinyi sallah sai kawai ki sake ganin jini haka zai ta miki wasa.
👻31. Hana haihuwa, aljani yakan hana mace haihuwa, ko kuma in ta tashi haihuwa sai an tsaya a kanta saboda zasu azabtar da ita.
👻32. Zama da datti da qazanta, aljani yakan hana mutum tsafta da zama cikinsa idan yana jikinsa, musamman idan aljanin arne ne.
👻33. Sumbatu da firgici a cikin baccin ki, zaa ga kina maganganu marasa kan gado koma kiyi ta firgita kina ajiyar zuciya kuma duk bacci kike.
👻Wainnan dama wasunsu dayawa suna daga cikin alamar akwai aljani a tare dake.
👻In kuma namiji ne shima zai iya experiencing problems dinnan ba wai dole sai mace ba.
👻Kamar rashin son aure, rashin sha'awa gaba daya, mafarkin suna soyayya da wata mace har sun yi aure duk a mafarki, da tsanar matar sa haka nan yaji ya tsani matar sa. Allah Ya tsare daga sharrin su.
Rubutawa:- Sadiya Lawwal Abubakar
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.