Assalaamu alaikum Wa rahmatullah!
*TAMBAYA*
Allah ya qara ilimi, ya bada ladan fatawa.
Malam don Allah, taron addu'a da sadakan uku da akeyi bayan zaman makoki na kwana uku yana da hurumi a musulunci???
Shin akwai wani amfani da wannan adduar take dashi ga mamaci?
Har akanyi abinci, kamar waina, a dinga rabawa ga duk wanda yazo wurin zaman makokin a ranar, da sunan SADAQA.
Don Allah Malam ayi min bayanin matsayar musulunci akan wannan al'amarin na *SADAKAR UKU*.
Nagode kwarai, Allah ya saka ma Malam da alkhairi.
*AMSA*
Wa'alaykumussalam.
Sadakar uku ba karantarwar manzon Allah bane, hakanan ba aikin sahabbai da tabi'ai bane, shari'a bata iyakance lokuttan da ake yiwa mamaci addu'a ba, dazarar mutum ya rasu yana bukatar addu'a har iya rayuwar shi mai Addu'ar.
Tara mutane bayan kwana uku, da dafa abinci da raba waina duk wadannan bidi'o'ine da aka kirkiro daga baya, *Babu wani dalili na shari'a akan haka*.
Manzon Allah ya fada cewa : .... "duk wanda ya kirkiro a cikin al'amarin mu (Addini/shari'a) abinda baya cikin addinin/shari'a toh an mayar masa".... Don haka nisantar aikata haka shine dai dai.
Wallahu A'alam
*_Malam Nuruddeen Muhammad Mujahid_*