AUREN MAI CIKIN SHEGE DON RUFA MATA ASIRI

*AUREN MAI CIKIN SHEGE DON RUFA MATA ASIRI* *TAMBAYA TA 020* Assalamu Alaikum. Malam, wata ce ta yi cikin-shege da wani mutum, sai ta nemi wani daban ya rufa mata asiri ya aure ta. Yanzu haka dai sun yi auren. Yaya hukuncin auren ya ke a Shari’a? *AMSA* W alkm slm w rhmtul Laah. [1] Ma’anar cikin-shege shi ne: Ta samu cikin ta hanyar ‘saduwa’ da wanda ba mijin da aka ɗaura musu sahihin aure ba. Kowa kuwa ya san cewa wannan mummunan haram ne a cikin koyarwar addinin musulunci. Allaah ya ce: وَلَا تَقْرَبُوا الزِّنَى، إِنَّهُ كَانَ فَاحِشَةً وَسَآءَ سَبِيلاً Kuma kar ku kusanci zina, domin ita alfasha ce kuma mummunar hanya ce. [2] Sannan wannan ɗan da aka samu ta wannan hanyar ba za a jingina shi ga wanda ya yi mata cikin ba, a shari’ance. Don haka, koda ɗayansu ya mutu babu gado a tsakaninsu, haka ma duk wata dangantaka da ta ke tsakanin Uba da ɗa. [3] Hukuncin da Shari’ar Musulunci Mai Adalci ta yanke musu shi ne: Idan ba su yi aure ba a yi wa kowane ɗaya daga cikinsu buloli guda ɗari a gaban jama’ar musulmi, ba tare da nuna wani tausayi gare su ba, kamar yadda ya ambata a cikin Suratun Nuur. Idan kuwa dukkansu ko ɗayansu ya taɓa yin aure, to sai a ƙara masa da jefewa da duwatsu har sai ya mutu, kamar yadda Sunnah Sahihiya ta nuna. [4] Amma game da maganar aurenta da wani musulmi, wannan ba zai yiwu ba sai bayan ta cika waɗansu sharuɗɗa, kamar haka: Sai ta tuba tuba ta gaskiya a bisa sharuɗɗan da Malamai suka shimfiɗa, tun kafin mahukunta su samu iko a kanta. Allaah Maɗaukakin Sarki ya ce: الزَّانِي لَا يَنْكِحُ إِلَّا زَانِيَةً أَوْ مُشْرِكَةً، وَالزَّانِيَةُ لَا يَنْكِحُهَا إِلَّا زَانٍ أَوْ مُشْرِكٌ، وَحُرِّمَ ذَلِكَ عَلَى الْمُؤْمِنِينَ Mazinaci ba ya yin aure sai da mazinaciya ko mushirika, kuma mazinaciya ba mai aurenta sai mazinaci ko mushiriki, kuma an haramta wannan ga muminai. Sai ta yi istibra’i, watau ta zauna na tsawon lokacin da za a tabbatar cewa babu jariri a cikin mahaifarta. Amma a nan, tun da an tabbatar da cewa tana da ciki to ba zai yiwu a ɗaura auren ba sai bayan ta haihu, saboda maganar Allaah Ta’aala cewa: وَأَوْلَاتُ الْأَحْمَالِ أَجَلُهُنَّ أَن يَّضَعْنَ حَمْلَهُنَّ Kuma masu cikunna iddarsu ita ce su haife cikinsu. Don haka, in dai har da gaske ne cewa wannan matar ta yi cikin-shege kuma ta yi aure da wani don ya rufa mata asiri, to ba shakka an yi haram, wannan auren bai halatta ba. Kuma dole ne a raba su, ta koma ta zauna har sai ta haife cikin nata tukun. Wal Laahu A’lam. *Shaikh Muhammad Abdullah Assalafiy* 24 - 02 - 2018 http://Www.facebook.com/Muneer-Yusuf-Assalafy-502666713417261/?re
Post a Comment (0)