TAMBAYA TA 10

TAMBAYA ======== 👇 Assalamu Alaikum dafatan malam yana cikin koshin lfy mal tambaya ta anan itace idan mutum ya wuce wadnda suke shangiya ko sigari zai iya musu sallama 2)mal nine ina da saurin haddace abu amma ina saurin mantawa shine nake neman shawarar ma ya ya kamata nayi a hutu lfy AMSA ====== 👇 Ya halatta Kayiwa wadanda ka tarar suna shan giya sallama, amma sai in kana da yakinin zasu amsa Maka sallamarka daidai. Dalili anan shine, ita sallama ae Addu'ah ce, saboda haka kaga mashaya sune ma sukafi chanchanta da ayi musu Addu'ah ta shiriya. Idan Amincin Allah ya tabbata a garesu, sai kaga sun shiryu sun dena abinda sukeyi na shaye - shaye. shikenan sai kaga sun koma kan hanya madaidaiciya. Suma Su zama mutanen kirki irin kowa. 2. Maganar saurin mance abinda ka haddace kuma, bansan me kake haddacewa ba har kake saurin mancewa, Sabida bakayi bayani ba, kana nufin haddar karatu ko waka ko idan an baka sako ne kake saurin mantawa, kaga bazan San me kake saurin mantawa ba. Allah shine masani. ✍ ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876
Post a Comment (0)