*_ALAMOMIN KARBAR TUBA_*
*Tambaya*
Assalamu alaikum dan Allah malam akwai hanyar da mutum yake gane Allah ya yafe masa zunubin da yayi, ya kuma nemi yafiya ?
*Amsa*
Wa'alakumus salam To dan'uwa akwai alamomin da malamai suka fada, wadanda suke nuna Allah ya karbi tuban bawansa, ga wasu daga ciki:
1. Aikata ayyukan alkairi, da son yin abin da zai kusantar da shi zuwa ga Allah.
2. Mutum ya dinga kallon gazawarsa wajan biyayya ga Allah.
3. Ya zama yana yawan girmama zunubin da ya tuba daga shi, yana kuma jin tsoron komawa zuwa gare shi .
4. Ya dinga kallon dacewar da aka ba shi ta tuba, a matsayin ni'ima daga Allah.
5. Ya zama yana yawan nisantar zunubai, sama da kafin ya tuba.
6. Yawan istigfari.
7. Son kusantar salihan bayi.
Allah ne ma fi sani.
5/06/2018
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.