TAMBAYA
========
👇
Mallam ina kwana Mallam don ALLAH inada tambayoyi
1) nice janabah ta kamani sakamakon mafarki acikin barci gashi kuma lokacin sanyi toh akwai ruwan da nake amfani dashi na tap(famfo) mai dumi sai aka sama matsala ruwan ya kare kuma na kunnan tanda na ruwan wutar nepa bata da karfi ruwan yaki hawa akwai ruwanda wanda shi kuma yayi sanyi diyawa kuma ina fama da sanyi hakan ya sanya nayi tayammum nayi sallah saboda ina ganin lokacin sallah zai iya wucewa kafin ruwan ya hawa tanda.
2) wankan janabah sifatul_ijzah mutum zai iyayi da shower, bucket ko buta ko wani abu dai haka.
AMSA
=====
👇
1. Hakan da kikayi yayi daidai, Sabida wucewar lokaci bakiyi sallah ba, anan ne Allah ya chanja mana taimama a matsayin kamar kinyi wanka kinyi alwala ne, amma na temporary, idan kika sami ruwan dumi sai kiyi wanka shikenan. Kuma bazaki sake wannan sallar ba.
2. Idan kika kuskure bakinki kika shaka ruwa a hancinki sai ki kunna shawa kiyi wankanki, kuma wanka yayi, daga karshe kawai zaki wanke kafafunki, shikenan.
Allah shine masani.
✍
ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876