TAMBAYA
=========
👇
Slm! Don Allah Malam wani hanya mutun zaibi ya saki matar sa wanda bazaiyi NIDAMA ba, saboda na gaji da halin ta wallahi Babar matsalal itace wajen saduwa malam Muna jimawa gida daya amma bamu haduba kuma Allah yayi ni da sha'awa mai karfi wanda yakai badan tsoran Allah ba dana fada neman mata, kuma munje har gidansu sunki daukar mataki , nikuma bani da halin auren mata biyu dan bani gun da zan sata munfi shekara biyu a haka, gaskiya na gaji. Allah yabani.
AMSA
======
👇
Karka saketa, kayi addu'ar Allah ya kawo Maka abinda zaka kara da wata.
Kuma ina mai tabbatar Maka da cewar, tinda zakayi ne dan ka kare kanka, Allah zai taimakeka, zai baka abinda zakayi, kuma zai wadata ka ta inda baka tsammani.
Sabida idan ka saketa, bakasan wadda zaka aure ba, zaka iya auren wadda ta fita sha'awa ko wadda bata kaita sha'awa ba, kaga idan wadda bata kaita yawan sha'awa bane, nasan biyun zasu isheka insha Allahu.
Allah shine masani.
✍
ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876
Allah shine masani.
✍
ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876