TAMBAYA TA 62

*_INA SO NA SABAWA ALLAH ! ! !_*

Wani saurayi ya je wajen Ibrahim dan Adhama, (daya daga cikin magabata), sai  ya ce masa zuciya ta tana tunkuda ni zuwa sabo, ka yi min wa'azi, sai ya ce masa :
Idan ta kiraka zuwa sabawa Allah to ka saba masa amma da sharuda guda biyar, sai saurayin ya ce fadi mu ji :

1. Idan za ka sabawa Allah, to ka boye a wurin da ba zai ganka ba, sai saurayin ya ce:  tsarki ya tabbata ga Allah, yaya za'a yi na boye masa, alhalin babu abin da yake buya gare shi, sai ya ce : yanzu ba ka jin kunya ka saba masa alhali kuma yana ganinka.

2. Idan za ka sabawa Allah to kar ka saba masa  cikin kasarsa, sai saurayin ya ce :   tsarki ya tabbata ga Allah, ina zan je, alhali duka duniya ta sa ce, sai ya ce masa yanzu ba ka jin kunya ka saba masa alhali kana  zaune a saman kasarsa.

3. Idan za ka sabawa Allah to ka daina cin arzikinsa, sai saurayin ya ce :  tsarki ya tabbata ga Allah, ta yaya zan rayu alhali duka ni'imomi daga gare shi su ke, sai ya ce masa yanzu ba ka jin kunya ka saba masa alhali yana ciyar da kai kuma yana shayar da kai, yana ba ka karfi.

4. Idan  ka sabawa Allah, to idan mala'iku suka zo tafiya da kai wuta, ka ce ba za ka tafi ba aljanna za ka, sai saurayin ya ce :  tsarki ya tabbata ga Allah ai sun fi karfina, kora ni za su yi.

5. Idan ka karanta zunubanka a takardarka ranar alkiyama ka ce : ba kai ka aikata su ba, sai saurayin ya ce :  tsarki ya tabbata ga Allah, ina mala'iku masu kiyayewa, sai ya fashe da kuka ya tafi yana maimaita wannan Kalmar ta karshe.

SHIN KANA TUNA WADANNAN IDAN ZA KA AIKATA ZUNUBAI ?

*_Dr. Jamilu Yusuf Zarewa_*

1/3/2014

Post a Comment (0)