TAMBAYA TA 61

*DAGA HANNU A MAKABARTA YAYIN ADDU'A GA MATATTU ! ! !*
*Tambaya*

Assalamu alaikum  Tanbaya malam.Malam meye hukuncin mutun in yamutu in an kaishi makabarta wasu suke daga hannu suna addua sai su shafa su tafi, nama wani malami tambaya ya ce ba daidai ba ne, ni kuma tunanina daga hunnun ayi addua shine mafi rinjaye, malam menene gaskiya ?
*Amsa:*

Wa alaikum assalam To dan'uwa ya tabbata a hadisin Muslim mai lamba ta : 974 cewa : Annabi s.a.w. ya ziyarci makabartar Baki'a ya kuma daga hannu har sau uku yayin  addu'a ga mamatanta"
Hadisin da ya gabata yana nuna mustabbancin daga hannu yayin addu'a ga mamaci a makabarta.
Nawawy yana cewa Akwai hadisai da yawa wadanda suka zo akan daga hannu yayin addu'a, don haka duk wanda ya iyakance wuraren da Annabi s.a.w. ya daga hannaye,  ya yi mummunan kuskure"  Almajmu'u  3\489.
Saidai malamai suna cewa : yin addu'ar jama'a da murya daya a makabarta na daga cikin bidi'o'in da ba  su da asali.

Allah ne mafi sani

*Amsawa*✍🏻

*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*
2\3\2015

Post a Comment (0)