BA A KAFA IZALA A KAN WATA AYYANANNIYAR MAZHABA BA

Dr Jalo Jalingo. BA A KAFA IZALAH A KAN WATA AYYANANNAR MAZHABA BA: 1. Kungiyar Izalah, da kuma kungiyoyin da suka zama shimfidar kafa ta watau: "Thaqaafah" da "Zaharar Haqqu" da "Al-Aqeedatus Saheehah" babu daya daga cikinsu da aka kafa ta a kan wata ayyanannar Mazhaba, a'a su wadannan shimfidar da kuma ita kanta kungiyar Izalah an kafa su ne a kan yin aiki da Alkur'ani da Hadithi da kuma Ijma'in Al'ummah. 2. Gini a kan wannan a inda duk mazhabar Malikiyyah ko wanin mazhabar Malikiyyah suka dace da Alkur'ani da Hadithi da kuma Ijma'i, to lalle Kungiyar Izalah na tare da su a nan dari bisa dari, a inda kuma mazhabar Malikiyyah ko waninta suka saba wa Alkur'ani da Hadithi da kuma Ijma'i to lalle kungiyar Izalah ba ta tare da su a nan. 3. Babu aibanta Imam Malik, ko aibanta mazhabar Malikiyyah cikin wannan matsaya ta Kungiyar Izalah kamar yadda wasu muta'assibai ke kokarin nuna wa duniya, a'a yin hakan shi ne kololuwar nuna girmamawa ga shi Imam Malik saboda da hakan ne ya umurci almajiransa a garin Madinah; a inda ya ce da su: a duk inda maganata ta saba wa Alkur'ani da Hadithi to ku yi jifa da ita a kan bango. 4. Tabbas babu inda lafazin ambaton mazhabar Malikiyyah ya zo koda sau daya ne a cikin constitution din Kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa Iqamatis Sunnah. Babu inda za a sami lafazin Mazhabar Malikiyyah a rubuce tun daga shafin farko na Constitution din Kungiyar har zuwa shafinsa na karshe, wannan kuwa babban taufiqi ne da Allah Ya yi wa shugabannin da suka rubuta wa Kungiyar constitution. 5. Lalle abin da yake rubuce cikin constitution din Kungiyar Izalah shi ne: Ita kungiya ce ta addinin Musulunci tsantsa kamar yadda Annabi Muhammadu mai tsira da amincin Allah ya taho ta shi, wacce take dogara da Alkur'ani da Hadithan Manzon Allah da kuma Ijma'i. Allah Ya taimake mu. Ameen.

Post a Comment (0)