BUHARI BA ZAI NEMI GAFARAR 'YAN NIJERIYA BA

*BUHARI BAZAI NEMI AFUWAR YAN NAJERIYA BA* . ✏AMINU MUSA ADO . BANGA WANI DALILIN DA ZAI SA ACE WAI SHUGABAN KASAR NAJERIYA . GEN. MUHAMMAD BUHARI . YA NEMI YAFIYAR YAN NAJERIYA AKAN KALAMAN DA YAYI BA A KASAR ENGLAND YAYIN TARON INGANTA TATTALIN ARZIKIN KASASHE. . HASALI MA YAN NAJERIYA DA YAWANCIN KAFAFAN YADA LABARAN SOCIAL MEDIA DA CONVERSATIONAL MEDIA NE YA KAMATA SU NEMI YAFIYAR BUHARI BISA KARYA DA KAGE DA SUKAI MASA. . ABUNDA BUHARI YA FADA A WANCAN TARO SHINE: . "KASO SITTIN CIKIN DARI NA MATASAN NAJERIYA MATASA NE YAN KASA DA SHEKARA DA TALATIN. YAWANCIN SU BA SUJE MAKARANTA BA, KUMA BASU TASHI SUN NEMI AIKIN YI BA. SANNAN KALUBALANTAR CEWA GWAMNATI CE ZATA BASU ILIMI, LAFIYA, DA GIDAN ZAMA KYAUTA" . TO MENENE ABUN LAIFI ANAN? ABUNDA BUHARI YA FADA GASKIYA NE. YAWANCIN MATASAN MU HAKA SUKE. . A NAJERIYA NE ZAKA GA MATASHI DA WAYAR NAIRA DUBU HAMSIN KO TALATIN A HANNUN SA, AMMA YA KASA BIYAWA KANSA KUDIN RIJISTIRESHIN DIN MAKARANTA WANDA BE WUCE NAIRA DUBU GOMA SHA BIYAR BA. DA ZARAR KAI MASA MAGANA SAI YACE WAI GWAMNATI TAKI BIYA MASA KUDIN MAKARANTA . HAKA A NAJERIYA NE ZAKA MATASHI YA KASHEWA BUDURWAR DA BA AURAR TA ZAIYI BA NAIRA DUBU GOMA AMMA YA KASA CIRE NAIRA DUBU GOMA SHA BIYU YA BIYAWA KANSA NECO . A NAJERIYA NE ZAKA MATASHI YA BIYA NAIRA DARI YA SHIGA GIDAN KALLAN BALL AMMA YA KASA SAYEN BRIGHTER GRAMMAR NA NAIRA HAMSIN . KUMA ANA MAGANA SAI KAJI YANA KALUBALANTAR GWAMNATI AKAN KIN YI MASA GIDA KO BIYAN KUDIN KARATUN SA . . TO MENENE KARYA A MAGANGANUN BUHARI? . A KUMA DAIDAI LOKACIN DA BUHARI YAYI WANCAN BATU, A WANNAN LOKACI KUMA YA NUNA KIN AMINCEWAR SA DA YARDA DA AURAN JINSU. AMMA SAI GASHI ME MAKON A YABA MASA BISA WANCAN KOKARI SAI GASHI WASU KAFOFIN YADA LABARAI DA MATASA A SOCIAL MEDIA SUN FUTO SU NAWA BUHARI KARYAR WAI YACE YAN NAJERIYA CIMA ZAUNE NE, JAHILAI NE KO MALALATA NE. . A INA BUHARI YA FADI WANNAN MAGANAR? MUNGA BIDIYO DA AUDIO WANNAN MAGANAR AMMA BANJI INDA BUHARI YA FADI WACCAN MAGANA BA. . DAN HAKA BANA GOYAN BAYAN BUHARI YA FITO YA NEMI WATA YAFIYA AKAN WACCAN MAGANAR BA, DOMIN ABUNDA YA FADA KARARAR GASKIYA NE . MASU TUNANIN SAI SUN YADA KARYA KO KAGE SANNAN ZASU KADA BUHARI TO SU SANI SUN MAKARA DOMIN ITA GASKIYA BA A KAWAR DA ITA DA KARYA . DAGA KARSHE INA KIRA GA MATASA YAN UWANA YAN NAJERIYA DA SU NATSU SU GANE MENENE DAIDAI SU GANE MENENE BA DAIDAI BA. YA KAMATA SU FAHIMCI YANDA WA INCAN TSOFAFFIN BARAYIN AZZALUMAN DA SUKA WAWUSHE DUKIYAR KASAR MU, SUKA JEFA MU HALIN DA MUKE CIKI SUNE KE AMFANI DAMU WAJAN YADA KARYA DA JITA JITA DAN BATA BUHARI . INA SON MATASA DA YAN NAJERIYA SU TUNA YANDA ABUBUWA SUKA FARU A SHEKARUN 2015, 2014 DA 2013 SANNAN SU KALLI HALIN DA AKE CIKI A HALIN YANXU . DA FATAN ZAMU ZURFAFA TUNANI . ALLAH YA TAIMAKI KASAR MU NAJERIYA . YA TALLAFI YAKIN AREWA DA AL UMMAR WANNAN YANKI . YA TAIMAKI MUSULINCI DA MUSULMAI . AMINU MUSA ADO 07033971982

Post a Comment (0)