ZUWA GA BABAWO BUHARI

Zuwa Ga Babawo Buhari.. Wasu tambayoyi ne nakeso nayi makasu akan Furucin da kayi na cewa Matsan Nigeria malalata ne kuma Basuda ilimi. 1) Shin Mai gaskiya a cikin Shekaru 3 da ka shafe kana Matsayin President na Najeriya Makarntun Primary nawa ka Gina, Secondary nawa ka kirkira, makarantun Gaba da sakandare nawa ka Samar, sannan Uwa uba Jamioi nawa ka Samar a wannan Kasar da Har zakace mutane basa son karatu? 2) a cikin Kasafin Kudin da kakeyi duk Shekara shin Kazo nawa kake warewa Bangaren ilimi don Ganin ya inganta? Munasa masaniyar cewa kasafin kudin Shekarar data wuce kaso shida a cikin Dari(6%) kawai ka warewa bangaren ilimi 3) ya mai girma Mai gaskiya Daga hawanka mulki Masanaantu nawa Gwamnatin ka ta kirkira don maganace matsalar aikin yi? 4) Matasa dayawa sun gama makaranta suna Neman aikin yi amma Ranar da kaje Ka kaiwa Majalisa budget kace ka dakatar da Duk wani Recruitment (Daukar aiki) shin meyasa ? 5) Shin Danka Yusuf aikin me yake ko sanaar har yake hawa Babur din tsere na Miliyan 50? 6)Muna da masaniyar Duk yayanka a kasar ingila suke karatu , wane hubbasa kayi na ganin ka infanta ilimin Kasar Najeriya don Ganin ka daidaita yayan talakawa da yayanka? Daga Abubakar Sadeeq sheka

Post a Comment (0)