'YAN HAKIKA BA' YAN TIJJANIYYA BANE

‘YAN HAKIKA BA ‘YAN TIJJANIYYA BANE Babu Kunya Babu Tsoro Ayau Munyi Niyyar Bayyana Gaskiya –Marigayi Abubakar Ladan SHARAR FAGE: Idan baku manta a shekarun baya an samu wani tataccen maras rabo wanda ya fito yaci zarafin Annabin tsira (s.a.w), a daren da al’amarin ya faru na danyi rubutu kadan akansa a shafina na facebook, sai wasu suka yita yin zagi wasu kuma suce ba zai yiwu dan tijjaniyya masoyin manzo yayi hakan ba. Washe gari da safe sai na saki Audio din a facebook sai mutane suka tabbatar sannan kuma aka fara yunkurin daukar mataki a ranar da dare sai na tsayar da damar sauke wannan audio ta yadda ko mutum yaje ba zai iya saukewa ba. A lokacin munji yunkuri da hukumar Hisba ta jihar Kano ta fito tayi inda har aka yi nasarar cafke masu ruwa da tsaki akai, kuma aka tafi kotu har ta kai ga yanke musu hukunci wanda har yanzu ba’a samu aiwatar da hukuncin ba. Ana cikin wannan yanayi gidan radio Freedom ya gabatar da wani shiri na musamman inda aka gayyato manyan malaman addini daga kowane bangare da muke dasu Izala, Darika da ma wadanda basa tare da kowanne an jona wannan shirin a wasu tashoshin FM da muke dasu a Kano a lokacin. Domin sauke wannan tattaunawar sai kadanna wannan link din dake kasa: http://darulfikr.com/s/44755 Mutanen gari suka kasa kunne suji shin menene gaskiyar al’amarin? Sai muka ji duka malaman sun hadu akan cewa ‘Yan Hakika fa ba ‘Yan Tijjaniyya bane, wannan shine abinda ya faru a wannan zaman. Tun a lokacin ni dai an sakamin shakku a matsayina na dankaramin dalibi ganin cewa anjima ana fito mana da mugayen akidu irin wannan daga cikin litattafan su, amman yau lokaci guda ace mana ba akidarsu bace? Shin dainawa suka yi ko kuma dama sharri ake musu? An samu malamai irinsu Dr. Abdallah Gadon Kaya, Dr. Ahmad B.U.K da suka fito suka bayyanwa duniya gaskiyar lamari akai. Domin samun amsar wadancan tambayoyin bara na waiwayi kundina na kuma mika tambayoyin ga Ahlin abin. Dan uwa daure ka saurari wadannan zantuka guda goma (10) daga bakin shehin malami babban jagoran tijjaniyya na Nigeria Sheikh Dahiru Usman Bauchi ta yaso sai kayi al’kalanci kan shin wannene ba wannene ba? Ga Taken Maganganunsa: 1. Abinda Yasa Ake Yawan Ambaton Sunan Shehu Tijjani Sabanin Sunan Allah http://darulfikr.com/s/44749 2. Shehu Tijjani Jikan Annabi ne http://darulfikr.com/s/44751 3. Matsayin Shehunnai da yadda suka zamo tsani wajen zuwa gurin Allah http://darulfikr.com/s/44750 4. Bai dace wani ya ja shehu Tijjani zuwa fadar Annabi ba sai dai shi yaja http://darulfikr.com/s/44753 5. Yadda aka hadu kiri da muzu da Shehu Tijjani da Annabi har ya bashi Tijjaniyya http://darulfikr.com/s/44753 6. Yadda aka baiwa dukkan ‘yan Tijjaniyya gida a Aljanna, ko wanda yayi amfani da abinda shehi yayi amfani dashi. http://darulfikr.com/s/44754 7. Asalin kyallen Wazifa misalinsa da tutar Nigeria da kuma jam’iyyun siyasa http://darulfikr.com/s/44756 8. Annabi ne yasa a rubuta Jawahirul Ma’aniy. http://darulfikr.com/s/44757 9. Annabi yace Shehu Tijjani ya koma dansa, haka ma sahabbansa da muridan shehu. http://darulfikr.com/s/44759 10. Duk ‘yan Tijjaniyya Suna da gida a Illiyuna. http://darulfikr.com/s/44758 ‘Yan uwa muyi nazarin wadannan maganganun duka akwai HAKIKANIN HAKIKA acikinsu ya rage naka kayi alkalanci. Note: Dalilin fito da wadannan abubuwa shine samun wani zindiqi da akayi yayi wata mummunar waka ta cin zarafiin Allah da manzonsa, maganganun shehu ba anan suka tsaya ba amman a gaba idan da hali zaku jimu. Haza Wasalam, Mu Dai Hakkin Mu Gaya Muku, Ko Ku Karba Ko Kuyi Dariya Dariyarku Ta Zam Kuka Gaba Da Nadamar Mai Kin Gaskiya. # BasheerSharfadi #Darulfikr.com 09035830253

Post a Comment (0)