GYARA DA RADDI WA MALAMAI 1)Da dai ace Idan manyan Malamai [ Manya a shekaru ko ilimi] sukayi abinda ake gani kuskure ne anbar manyan Malamai irinsu suyi musu raddi ko gyara da zaifi a kan kananan yara suyi[ a shekaru da ilimi] 2) Idan karamin yaro dan shekara goma sha ko ashin da zaiyi kalaman batanci ga malami dan shekara hamsin da ko sittin da dasunan gyara, ina ganin wannan baya nuna fahimta ko son addini ko ilimi, yana nuna al ummar mu tana bukatar tarbiyya da girmama na gaba. 3) Mafiyawan abubuwan da ake gyara ko raddi akai mas'aloli ne na ijtihadi. Duk yadda nike ganin ina kan daidai ko kake ganin kana kan daidai a wata mas'ala ijtihadi ne, ba tabbas din cewa a kan daidai muke koda mas'alar da muke tattaunawa tana kan daidai. 4) Annabi S.A.W yana cewa: "Albarka tana tareda manyan ku." 5) Ana raddi ne ko gyara domin a fahimtar ba domin ayi cin mutunci ba. Zaiyi kyau masu raddi wa Malamai su karanta wannan littafen na Shaykhul Islam Ibn Taymiyya domin karin samun hasken yadda ake muamala da wanda aka sabawa a hafimta👇 Allah ya ganar damu dai dai yayi muna muwa faka ya karba mana. Rubutawar: ✍🏼 Sheikh Dr. Jabir Sani Maihula.