YANA DAGA CIKIN SUNNAH RASHIN GAISAWA DA MUTUMIN DA AKE TUNANIN ZA A IYA KAMUWA DA CUTAR DA TAKE DAMUNSA
Amru bin Sharid Ath-Thaqafiy ya ba da labari daga Mahaifinsa ya ce:-
Qabilar Thaqif sun zo yi wa Manzon Allaah ( صلى الله عليه وسلم ) mubaya'a, ya kasance a cikin su akwai wani mutum kuturu, lokacin da mutumin ya taso zai yi mubaya'a ga Manzon Allaah ( صلى الله عليه وسلم ), sai manzon Allaah ( صلى الله عليه وسلم ) ya aika masa da saqo cewa:-
*" Lallai mun yi maka mubaya'a, ka koma inda kake ( ba sai ka qaraso nan ba) "*
Wannan hadisin Imam Muslim ne ya riwaito shi, hadisi mai Namba 4256.
*Ga Matanin hadisin cikin nan*
👇👇
قَالَ الإمام مُسْلمُ رحمه الله:-
4256 حَدَّثَنَا يَحْيَى بْنُ يَحْيَى ، أَخْبَرَنَا هُشَيْمٌ ، ح وَحَدَّثَنَا أَبُو بَكْرِ بْنُ أَبِي شَيْبَةَ ، حَدَّثَنَا شَرِيكُ بْنُ عَبْدِ اللَّهِ ، وَهُشَيْمُ بْنُ بَشِيرٍ ، عَنْ يَعْلَى بْنِ عَطَاءٍ ، عَنْ عَمْرِو بْنِ الشَّرِيدِ ، عَنْ أَبِيهِ ، قَالَ : كَانَ فِي وَفْدِ ثَقِيفٍ رَجُلٌ مَجْذُومٌ ، فَأَرْسَلَ إِلَيْهِ النَّبِيُّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ "إِنَّا قَدْ بَايَعْنَاكَ فَارْجِعْ "
👈 صحيح مسلم
👈 كتاب السَّلَامِ
👈 بَابُ اجْتِنَابِ الْمَجْذُومِ وَنَحْوِهِ
👈 حديث رقم 4256
✍ *Habib Aboo Ammar*