HATSARIN 'YAN FIM GA AL'UMMAH

HATSARIN 'YAN FIM GA AL'UMMA
'Yan Fim, wadanda aka fi sani da 'Yan Drama, suna daga
cikin rassa na Kungiyoyin Boko Aqida mafi hatsari ga
al'umma, kuma mafi saurin tasiri a kanta, saboda su ne suke
yada barnarsu a aikace, kuma a cikin jama'a ba tare da wani
tsaiko ko tsangwama ba.
Duka kungiyoyin Boko Aqida kusan sun yi tarayya a kan
halasta Alfasha da yaki da Addinai da kyawawan dabi'u, inda
dukkansu sun dauki wannan a matsayin babbar manufa, kuma
babban jigo a tafiyar tasu.
Kungiyoyin Boko Aqida, tun daga kan Masuniya
(Freemasonry, Masonic), da Sakulanci (Secularism), da
Gurguzanci (Socialism), da Kwaminisanci (Communism),
Ilhadi (Atheism), duka wadannan kungiyoyi da hanyoyi na
tsarin rayuwa, dukkansu sun yi tarayya wajen jefar da Addini
a cikin rayuwa, da kuma jefar da kyawawan halaye da dabi'u,
bisa ikirarin 'yancin rayuwa.
To su wadannan 'Yan Fim, an samar da su ne don yada
Aqidar 'yancin rayuwa ba tare da zama karkashin qaidin
Addini ko kyawawan dabi'u na kunya da kamun kai ba, tare
da yaki da su. Shi ya sa za a ga fina – finai da ake yi duka
kusan suna kira ne ga bayyana tsiraici da yaduwar alfasha a
cikin al'umma ta hanyar cire shamaki tsakanin jinsin maza da
mata.
Shi ya sa 'Yan Fim suka zama hanya mafi muhimmanci ga
Kungiyoyin Boko Aqida wajen watsa barna da sharrinsu a
cikin al'umma.
A Turai, akwai kungiya ta Boko Aqida da ta yi fice da wannar
manufa ta halasta alfasha da rushe kyawawan halaye
(Libertine), wacce ake kira da 'Yan wayewa (Modernity),
wadanda suka tattaro tunaninsu da Aqidunsu daga wasu
munanan kungiyoyi masu yawa, kamar Marxism,
Existentialism, Freudian, Darwinism, Surrealism, Avatar.
Manufar wannar kungiya ita ce rushe tushen Addini, da
dukkan abin da ya zo daga gare shi na Aqidunsa da
dokokinsa da kyawawan dabi'unsa, har da halaye da dabi'u na
'yan'adamtaka da suka tabbata ta hanyar fidira da asalin
halittar mutum, suna rushesu da hujjar –wai- tsoffin Aqidu ne
da tsoffin dabi'u da ba su dace da zamani ba, don haka suke
halasta wa mutane rayuwar sharholiya da halasta alfasha da
kosar da sha'awa ta jinsi. Duka wannan da sunan 'yanci, da
nitsewa cikin zurfin rayuwa ta jin dadi.
Saboda haka, ita wannar Kungiya, ita ce madarar kungiyoyin
Ilhadi mafiya hatsari, kuma ta wannan bangare ne ta zama ta
fi sauran kungiyoyin Boko Aqida hatsari, saboda ta ginu ne a
kan rashin mutunci da tsantsar yarinta, da rashin sanin ya-
kamata, da raba rayuwa da Addini da mutunci da dabi'u na
mutuntaka a cikin rayuwa. Shi ya sa alfasha da zina da
luwadi da madigo da giya suke da matukar tasiri a cikinsu,
kuma suke kira zuwa ga halastasu.
DON HAKA, DAGA CIKIN HANYOYI DA WADANNAN SUKE BI
WAJEN WATSA BARNA A CIKIN AL'UMMA, DA GURBATA
TARBIYYA DA MUTUNCI DA KYAWAWAN DABI'U NA
MUTUNTAKA, AKWAI SHIRYA FINA – FINAI NA SOYAYYA DA
ALFASHA, DA BAYYANA TSIRAICI DA NUNA RAYUWAR
HOLEWA DA SHARHOLIYA DA IZGILANCI MA ADDINI DA
KYAWAWAN HALAYE DA DABI'U NA MUTUNCI DA
MUTUNTAKA. WANDA DAGA KARSHE HAR SU KAI GA
SHIRYA FINA – FINAI NA BATSA DA ZINACE – ZINACE
(Pornography), WANDA AKA FI SANI DA BF (Blue Film).
Duk da cewa; wannar kungiya ta bayyana ne a Turai, to
amma tunanin yana da tushe a cikin wasu Kungiyoyi da suke
dangantuwa zuwa ga Muslunci, kamar yadda aka samu 'Yan
Jahamiyya masu cewa; Imani shi ne Sanin Allah a zuciya
kawai. Ma'ana; IMANI KAWAI A ZUCIYA YAKE BAN DA
GABOBI. SABODA HAKA MATUKAR MUTUM YA SAN ALLAH
A ZUCIYARSA, TO YANA DA DAMAR YA YI TA YIN DUK ABIN
DA YAKE SO, BA SAI YA AIKATA FARILLAI KO YA YI WANI
AIKIN ALHERI BA, KUMA DUK YAWAN MUNANAN AIYUKA DA
MUTUM ZAI AIKATA, DUK GIRMANSU BA ZA SU CUTAR DA
SHI BA. WANNAN YA SA ZA KA JI WADANDA SUKA NITSE
CIKIN ALFASHA DA KIRA ZUWA GA HALASTATA KAMAR
'YAN FIM SUNA CEWA; IMANI A ZUCIYA KAWAI YAKE, KO
SU CE: ALLAH DA ZUCIYA KAWAI YAKE AMFANI.
Haka 'Yan Shi'a Badiniyya, wadanda gaba daya suka gina
Addininsu a kan halasta Haram ta kowace fiska. Ta yadda su
a wajensu babu wani abu da ake kira Haram cikin abin da
Shari'a ta haramta.
Haka akwai irin wannar Aqida ta halasta alfasha wa mutane
a wajen 'Yan Dariqun Sufaye Masu Guluwwi, wadanda aka fi
sani da 'Yan Hakika ('Yan Freedom), su ma duka suna tafiya
ne a kan wannan tunani.
An samu masu kira ga wannar mugunyar Aqida a wajen
Zindiqai cikin Sufaye da 'Yan Falsafa irinsu Ibnu Arabiy, da
Hallaj, Ibnu Rawandiy, da kuma mawaka masu wannan tunani,
irinsu Abu Nawwas, Al- Ma'arriy da makamantansu.
Shi ya sa za ka samu duka mabiya wannan tunani kusan
dukkansu, daga Zindiqai da Mulhidai da 'Yan Falsafa ne, cikin
Mawaka da Makida da 'Yan Rawa da 'Yan Fim, da sauran
nau'o'in 'yan sharholiya masu halasta alfasha da kira zuwa
gareta.
Saboda haka, wannar Aqida da wannar hanya, kamar yadda ta
fi muni a Turai, haka ita ce Aqida mafi muni cikin masu
dangantuwa zuwa ga Muslunci.
DON HAKA, LALLAI WAJIBI NE MUTANE SU YI HATTARA DA
'YAN FIM, SU KIYAYESU MATUKA. YA WAJABA A KAN
JAMA'A GABA DAYA, SU SA IDO A KAN TARBIYYAR
AL'UMMA GABA DAYANTA, A KIYAYI IRIN WADANNAN
KUNGIYOYI NA BOKO AQIDA DA RASSANSU, DA YARANSU,
MUSAMMAN MAFI HADARINSU, WATO 'YAN WAYEWA,
WADANDA SUKA KUNSHI 'YAN FIM DA 'YAN RAWA, ALAL
HAKIKA YAKI SUKE DA ADDINI DA KUMA KYAWAWAN
HALAYE DA DABI'U NA 'YAN'ADAMTAKA DA MUTUNTAKA.
Allah ya yi mana tsari da hanyoyin Iblis.
Via : Aliyu Muh'd Sani

Post a Comment (0)