NASIHATA A GARE KI 'YAR UWA : A matsayinki na mace musulma, mai imani, zan in yi miki nasiha akan rayuwar duniyarmu. Allah madaukakin sarki da ya halicci mutane sai ya fifita sashen su akan sashe. Wani an fifita shi da kudi, wani da lafiya, wani da lilimi wani da hikima wani da mulki. Nasihata a gare ki ita ce, a koda yaushe kada kike kallon wadanda suke sama dake ta bangaren falalar da Allah yayi musu, na kudi, ko ilimi ko kyau ko mulki. Domin yin hakan ya kan sa mutum ya manta da ni'imar da Allah yayi masa, sannan yin hakan yana gadar da hassada. A koda yaushe kike kallon na kasa da ke, ma'ana wadanda Allah ya fifita ki a kansu a wannan rayuwa. Tabbas Allah ya baki idanun gani, wasu kuma makafi ne, Allah ya baki kafafun tafiya, wasu kuma guragu ne, Allah ya baki ilimi na zamani da na addini, wasu kuma jahilai ne, Allah ya baki kunnuwan da kike ji, wasu kuma kurame ne, Allah ya baki bakin magana, wasu kuma bebaye ne, Allah ya baki lafiya, wasu kuma suna asibiti, ba lafiya. To yin hakan zai sa kike tuna ni'imar Allah a gare ki. Wannan ita ce babbar nasihar da manzo s.a.w. yayi mana, a hadisin da bukhari da muslim suka rawaito. Annabi Muhammad s.a.w yana cewa: " ﻻ ﺗﻨﻈﺮﻭﺍ ﺍﻟﻰ ﻣﻦ ﻫﻮ ﻓﻮﻗﻜﻢ، ﺍﻧﻈﺮﻭﺍ ﺍﻟﻰ ﻣﻦ ﻫﻮ ﺃﺳﻔﻞ ﻣﻨﻜﻢ، ﻓﻬﻮ ﺃﺟﺪﺭ ﺃﻻ ﺗﺰﺩﺭﻭﺍ ﻧﻌﻤﺔ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻜﻢ ". ﻣﺘﻔﻖ ﻋﻠﻴﻪ . Ma'ana: " kada kuke kallon na sama da ku, ku ke kallon na kasa da ku, hakan ne zai sa ba za ku tozarta ni'imar da Allah yai a gare ku ba." DON HAKA..'YAR UWA: ●Ki zama mai hakuri a rayuwarki. ●Duk abin da zaki fada, to ya zama gaskiya. ●Kiyi biyayya ga mijinki, ki girmama yan uwansa. ●Ki yi masa nasiha da gyara idan yayi kuskure. ●Idan baki dashi ki roki Allah ya baki miji na gari. ●Kar ki ba da sheda, ko ki fadi abin da baki da ilimi akan sa. ●Kar ki raina dan adam komai kaskancin shi na zahiri. ●Mai matsayi a wajen Allah shi ne wanda yake da takawa. ●Ki nemi shiriyar Allah a koda yaushe. ●Sannan ki zama mai saukin sha'ani a rayuwa. ●Ki mu'amalanci mutane da kyakkyawar mu'amala. ●Ki yi biyayya ga iyayenki. Ki taimaka musu. Dalibinku: Bukhari Musa Adam