SHARHIN FIM DIN CHENNAI EXPRESS

SHARHIN FIM ƊIN CHENNAI EXPRESS 

Chennai Express fim ɗin Indiya ne da aka fitar a cikin shekara ta 2013. Fim ɗin ya jiɓinci abubuwa irin su ban dariya, Cakwakiya, ƙaddara da kuma ƙarfin hali. A yayin fitar da wannan Fim, an fitar da shi ne a cikin Harsuna da dama Kamar Turanci, Faransanci, Sipaniyanci, Jamananci, Hibranci, Dutanci, Turkanci da kuma Malanci. Bugu da ƙari, an Fassara wannan Fim a cikin Harshen Hausa. 

MA'AIKATA 

Bada Umarni: Rohit Shetty

Ɗaukar Nauyi:Gauri Khan, Ronnie Screwvala,Siddharth Roy Kapur da Karim Morani

Tsara Labari: Yunus Sajawal

Rubuta Labari: K. Subash

Bada Labari: Shah Rukh Khan

Haɗa Sautin Waƙoƙi: Vishal–Shekhar

Haɗa Take: Amar Mohile

Jami'in Shiri: Dudley

Tacewa: Steven H. Bernard

Kamfanin Da Ya Shirya: Red Chillies Entertainment

Kamfanin Da Ya Rarraba Shi: UTV Motion Pictures

Ranar Fita: 8 August 2013 (Kasuwannin Duniya)

9 August 2013 (India)

Tsawon Shirin: Minti 141

Ƙasa: India

Harshe: Hindi

Kasafi: ₹115 crore

Asusun Kasuwanci: ₹423 crore

Fim ɗin farko da aka so a shirya a tsakanin Shah Rukh Khan da Rohit Shetty maimacin wani fim ne mai suna Angoor (1982). Amma a Ƙarshe sai aka zaɓi labarin Chennai Express wanda a da, an ajiye shi ne a matsayin Kota Kwana wa SRK. Da Fari an so a sakawa shirin suna Ready Steady Po ne amma daga baya sai aka canja zuwa Chennai Express. An fara Ɗaukar wannan Fim ne a Mehboob Studio a cikin watan Oktoba 2012 Yayinda aka kammala a cikin watan Mayu 2013. An ɗauki ɓangare mai girma na wannan Fim ne a Ooty, inda aka kafa kayan aiki masu yawa a Wai. 

A Yayinda wannan Fim ya fita, ya sha suka kuma ya sha yabo daga masana da kuma masu shayi akan Fina Finai. Sai dai duk da haka, fim ɗin ya kafa tarihi sosai a Asusun kasuwancin Fina Finan Indiya da kuma duniya baki ɗaya inda ya zamo fim da yafi kowanne sauri wajen haɗa ₹1 billion (US$14 million) a kasuwancin Fina Finan India. Haka kuma fim ɗin ya samu nasarar doke 3 Idiots inda ya zama fim ɗin Bollywood da yafi kowanne kawo kuɗi a wancan lokacin. 
Ya zuwa watan Maris na 2018, Chennai Express ne fim na 11 daga cikin Fina Finan Bollywood da suka fi kowanne fim kawo kudi a Kasuwannin duniya baki ɗaya. Sannan kuma, Chennai Express shi ne fim na farko da aka fara fitar da shi a rana ɗaya a Ƙasar India 🇮🇳 da kuma Peru 🇵🇪. 

LABARIN FIM ƊIN 

Rahul Mithaiwala (Shah Rukh Khan) wani Narayan Tuzuru ne da ke zaune a garin Mumbai, Kakannin sa ne suka raine shi tun yana ɗan shekara takwas a duniya har zuwa girman sa. Kakan Rahul Watau Bhishambhar (Lekh Tandon) yana da Shagunan Siyar da Alawa da kuma sauran kayan Maƙulashe, kuma anan ne Rahul yake aiki a matsayin mai kula da Shagon. 

Kafin Zagayowar ranar bikin Haihuwar Bhishambhar a karo na ɗari 100, abokan Rahul watau Bobby da Baman sun gayyace shi zuwa Goa domin yawon buɗe ido da Shaƙatawa, kuma ya amince zai bi su. Sai dai Kash! A ranar da za'a yi wannan shagali ne Bhishambhar ya mutu Yayinda yake kallon ɗan wasa Sachin Tendulkar a Talbijin a wani wasan Ƙwallon Gora. Bayan mutuwar Bhishambhar, sai Kakar Rahul Neetu ta faɗa masa cewa Bhishambhar yabar wasiyya cewa idan ya mutu yana so a raba tokar sa Izuwa gida biyu, ɗaya a zuba a cikin Kogin Ganga ɗayan kuma a Kogin Rameshwaram. Don haka sai ta roƙi Rahul da ya ɗauki rabin Tokar yaje ya zuba a cikin kogin Rameswaram. Ba tare da yaso ba haka dai ya amsa, amma yana so yayi waccan tafiya tare da abokan sa zuwa Goa. 

Rahul, Bobby da Baman sai suka tsara cewa kawai su zuba tokar a Kogin Goa, to amma ita Neetu sai ta matsa kan cewa sai tayi mishi rakiya, hakan ya tilasta wa Rahul bin jirgin ƙasa domin yin wannan tafiya. Sai ya siyi tikiti ɗaya tal na Jirgin ƙasan Chennai watau Chennai Express, tare da tsara cewa zasu haɗu da Abokan sa Bobby da Baman a tashar Mahaɗar Kalyan. Sai dai kuma, Rahul ya manta ya ɗauki tukunyar tokar Yayinda ya fita, da ya dawo ɗauka kuma, tuni jirgi ya ɗau aniyar tashi. Bayan ya samu damar Ɗaukar tokar sai yayi nufin fita daga jirgin domin komawa wajen Abokan sa, Rahul na Leƙowa da nufin ya sauka, sai ya hango wata Budurwa ta nufo shi a guje tana so ta hau jirgin, a nan dai ya taimake ta tare da wasu mutum huɗu kuma har wa yau suka hau jirgin, Yayinda shi kuma ya rasa damar sauka daga jirgin a Sanadiyyar haka. 

Anan cikin Jirgin, sai Rahul ya nemi ya tashi wannan budurwa wacce ta ke magana da shi a kaikaice cikin Shahararrun Waƙoƙin Fina Finan Indiya. Ta hakane ta bayyana mishi cewa waɗannan mutane huɗun da ya taimakawa so suke yi su sace ta. 
 Rahul sai ya ara mata wayar hannun sa domin ta kira abokan ta, amma sai waɗannan mutane suka fisge wayar tare da jefar da ita. Rahul ya fusata sosai amma dole ta sa shi yayi shiru saboda suna ɗauke da muggan Makamai. Amma sai ya faɗawa mai amsar tikitin jirgin domin yayi wani abu, shima nan take suka jefa shi waje inda ya faɗa wani ƙaton kogi. Cikin Firgici Rahul ya Fahimci cewa waɗannan mutane huɗu Ƴaƴan Kawunnan wannan budurwa ce wacce ta bayyana sunan ta a matsayin Meenalochni "Meenamma" Azhagusundaram. Ta gudo ne daga gida sabili da auren dole da mahaifinta yake so yayi mata da wani ɗan Jagaliya mai suna Tangaballi. Shi kuwa Mahaifin Meenamma, watau Durgeshwara "Durgesh" Azhagusundaram, wani hamshaƙin Ɗan Jagaliya ne mai ƙarfin iko da ya shahara a duk faɗin yankin Tamil Nadu.

Daga nan sai Meenamma ta tafi da Rahul zuwa wajen Durgesh in da ta gabatar da shi a matsayin wanda take. Tangaballi sai ya ƙalubalanci Rahul akan su gwabza Aga wanda zai yi nasara. Shi kuwa Rahul cikin rashin sani sai ya amince bisa ga ƙarancin fahimtar harshen Tamil da yake da shi. A daren da za'a yi wannan Fafatawa sai Rahul ya gudu tare da taimakon wani ɗan sanda mai suna Shamsher, bisa tsautsayi kuma sai ya ɓige a cikin jirgin wasu ƴan ta'adddan Ƙasar Sri Lanka waɗanda suke Safarar Haramtattun abubuwa ta ruwa. Yayin ƴan sanda suka kama Rahul suka tuhume shi, sai ya basu labarin sa, a Ƙarshe dai sai gashi an dawo da shi ƙauyen Komban. 

Cikin tsoron abinda ka iya faruwa da shi, Rahul sai yayi Basaja da cewa zai sheƙe Meenamma inda ya ɗauke ta suka gudu a cikin motar mahaifinta. Bayan motar ta lalace, sai Rahul da Meenamma suka yi ƴar cacar baki suka rabu kowa yayi nashi wuri. Kasancewar Rahul bai san hanya ba sai ya dawo wajen Meenamma inda ta yi mishi Jagoranci zuwa ƙauyen Vidhamba. Meenamma sai kuma ta faɗawa mutanen ƙauyen cewa su Sabbin amarya da ango ne da suke buƙatar kariya da kuma hutu inda mutanen ƙauyen suka amince da su. 

A cikin wannan yanayi ne Meenamma ta fahimci cewa ta kamu da soyayyar Rahul. Idan Rahul yayi shirin Guduwa, sai taƙi amincewa saboda bata so mutanen ƙauyen su gane abinda ke tsakanin su. Watarana sai Tangaballi ya kama Rahul Yayinda yayi yunƙurin guduwa, amma sai mutanen ƙauyen suka taimaka musu suka Fece. Bayan sun gudun ne sai Meenamma ta lallaɓa Rahul kan ya je ya zuba tokar Bhishambhar a ruwa, har ma ta yi mishi rakiya zuwa kogin Rameswaram ɗin. A kan Hanyar su ta dawowa ne Rahul ya fahimci cewa shima fa ya kamu da Son Meenamma, don haka sai yaƙi faɗa mata inda zasu, amma sai ya ɗauke ta zuwa ga mahaifinta Durgesh domin ya fahimtar da shi halin da Meenamma take ciki ko zai fahimta, har ma ya faɗa wa Meenamma cewa yana son ta. 

Daga nan kuma sai Rahul ya faɗawa Tangaballi da yaran sa cewa ya shirya wa wannan fafatawar yanzu inda suka kacame da faɗa a wurin. Duk da cewa an yiwa Rahul dukan tsiya tare da yi masa Jina-Jina, a Ƙarshe dai shi yayi Nasara. Durgesh da Tangaballi sai suka tuba, suka amintu cewa Soyayyar Talakan gari kamar Rahul ta fi girman ji da kuma ƙarfin iko. Daga nan Sai Durgesh ya Amincewa Rahul Da ya auri Meena. A nan ne Rahul ya bar saƙon da ke bayyana cewa Shi so bai san wani yare ko Ɓangaranci ko harshe ba, kuma in dai mutum yana da ƙarfin zuciya, to babu abinda ba zai gagare shi. 


JARUMAN SHIRIN DA MATSAYIN SU. 

* Shah Rukh Khan - Rahul Mithaiwala
* Deepika Padukone - Meenalochni "Meenamma" Rahul Mithaiwala (nèe Azhagusundaram)
* Nikitin Dheer - Tangaballi 
* Sathyaraj - Durgeshwara "Durgesh" Azhagusundaram 
* Mukesh Tiwari - Sifeta Shamsher
* Kamini Kaushal - Neetu Bhishambhar Mithaiwala 
* Puvisha Manoharan - Radhika "Radha" Azhagusundaram 
*vLekh Tandon - Bhishambhar Mithaiwala 
* Mohan Raman - Malamin Majami'a 
* Yogi Babu - ɗan fasa ƙwaurin Sri Lanka
* Jasper - Ɗan Jagaliya 
* King Kong 
* Jimmy Moses - Direba 
* Rakesh Kukreti - Bobby 
* Priyamani - a "1 2 3 4 Get on the Dance Floor"

WAƘOƘIN FIM ƊIN DA MAWAƘAN SU 

1. "1 2 3 4 Get on the Dance Floor" Vishal Dadlani, Hamsika Iyer, Sricharan 
2. "Titli" Gopi Sunder, Chinmayi, Srimathumitha 
3. "Tera Rastaa Chhodoon Na" Anusha Mani, Amitabh Bhattacharya 
4. "Kashmir Main Tu Kanyakumari" Sunidhi Chauhan, Arijit Singh, Neeti Mohan 
5. "Ready Steady Po" Vishal Dadlani, Brodha V, Smokey, Enkore, Natalie Di Luccio 
6. "Chennai Express" S. P. Balasubrahmanyam, Jonita Gandhi 
7. "Titli" Zoheb Khan, Phoenyx
8. "Chennai Express (Mashup)" DJ Kiran Kamath 
9. "Lungi Dance" Yo Yo Honey Singh 


<••••••••••••••••••••••••••••>
  Hãïmâñ Khãñ Řăééş_* <••••••••••••••••••••••••••••>
 08185819176
Twitter: @HaimanRaees 
 Instagram: Haimanraees 
 Infohaiman999@gmail.com

Post a Comment (0)