SHARHIN FIM DIN RAEES

SHARHIN FIM DIN RAEES
Raees Fim Din India ne da aka yi a shekarar 2017, Fim Din ya kunshi Jarumai irin su Shah Rukh Khan , Mahira Khan Da Nawazuddin Siddiqui.
Fim Din Raees ance anyi shi ne akan rayuwar wani dan Ta'ada mai suna Abdul Latif. Sai dai kuma, wadanda suka shirya Fim Din sun karya hakan, tare da fadin cewa labarin Fim Din Zallar Kirkira ce kawai. Fim Din ya samu Karbuwa sosai domin sai da ya zamo Fim Din Bollywood da yafi kowane Fim kawo kudi a 2017 kafin Fim Din Salman Khan Tiger Zinda Hai yazo ya buge shi daga baya.
LABARIN FIM DIN
Fim Din ya fara ne daga Shekarun -1960s ya kuma kare a shekarun 1980s.
Labari ne akan Raees (Shah Rukh Khan ) wanda yake zaune a Gujarat , Jahar da tafi kusan kowacce Jaha tsaurara doka akan Haramtattun Kaya. Tun yana dan karamin sa ya fara aiki da masu saida kayan maye tare da abokin sa Sadiq (Mohammed Zeeshan Ayyub). Raees yana aiki ne wa Jairaj (Atul Kulkarni ), wanda yake Safarar kayan maye ta hanyar baiwa 'Yan Sanda cin hanci. who smuggles alcohol illegally by bribing the police. Raees yana rayuwa ne bisa tsarin da Mahaifiyar sa ta fada masa cewa kowacce Sana'a kyakkyawa ce, kuma babu wani Addini Da ya fi Sana'a matukar Sana'ar ba Zata cutar da kowa ba.
Watarana, sai Raees ya yanke Shawarar fara nashi Kasuwancin. A garin hakan ne ya hadu da Musabhai ( Narendra Jha) a Mumbai, kuma da taimakon sa ne ta fara nasa Kasuwancin na Safarar giya. Ana cikin haka, sai aka yiwa wani Nagartaccen Dan Sanda mai suna J. A. Majmudar (Nawazuddin Siddiqui) canjin wajen aiki izuwa Fatehpur, inda ya fara Tarwatsa duk wani Wurin siyar da giya.
Babban Minista Pashabhai, Gurbataccen Dan SIYASA ne, kuma yana taimakon Raees a harkar Kasuwancin sa saboda giya da kudi.
Kudin sa da Basirar sa suka sa Raees ya dinga Gocewa duk wani tarkon da  Majmudar yake Dana masa, kuma Ya ci gaba da Kasuwancin sa. Baya ga haka, Raees yana taimakon Al'ummah ta hanyar daukar mata aiki domin su dinga dinka masa Jakukkuna wadanda yake Cinikayyar giyar sa da su.
A hakan ne kuma dai har wayau ya auri Aasiya (Mahira Khan ). Saboda Sabanin fahimtar dake tsakanin su da Raees, sai Jairaj yayi kokarin ganin bayan sa, amma sai ya kubuta Daga wannan tuggun sannan ya kashe Jairaj.
Raees Aasiya sai suka haifi da, wanda suka saka Mishi suna Faizan. Raees ya Gayyaci CM, Pashabhai da sauran mutane domin su taya shi murna. Daga nan ne Pashabai ya baiwa Raees kwangilar korar duk wani Mazauni da baida takardu a wani fili, tare da Gina Sabbin Gidaje a wurin da mutane zasu dinga Amfanuwa da shi.
Raees ya samu Damar Canjawa Majmudar wurin aiki izuwa dakin kula da Kiraye-Kirayen Wayoyi, sai dai kuma ashe TSUGUNO bata kare ba, domin Majmudar sai yayi amfani da wannan damar ya dinga Sauraren duk wata Magana da Raees zaiyi a waya.
Dama Raees ya Jawa Pashabhai kunne kan kada ya fito Kamfe amma yaki ji, don haka yayi amfani da karfin sa ya hana kamfen. Hakan ne yasa CM ya Shawarci Raees da ya daure yaje gidan yari na dan wani lokaci kafin a daidai ta komai. A Yayinda Raees yake can a daure, sai CM and Pasha suka hade masa kai.
Shi kuma Raees sai ya fito takara Alhalin yana gidan yari kuma ya ci nasara. A dai dai wannan lokacin ne kuma aka sake yiwa Majmudar sauyin wajen aiki izuwa Fatehpura.
Hargitsi dai sai ya barke a garin, ganin cewa Raees zai iya zama masa karfen Kafa, sai CM ya hana ci gaba da aikin ginin nan da Raees ya fara kokarin ganin yayi. Hakan yasa Raees ya wayi gari bashi da ko sisi sakamakon ya riga ya an taya duk kudaden sa a cikin maganar ginin nan, Kamfe da kuma taimakon mutane da yayi ta yi a lokacin Hargitsin.
Raees na cikin wannan hali ne sai Musabhai ya bashi wasu makudan kudade domin ya shigar masa da wasu dinarai ta boyayyar hanya.
Bama Bamai Kuma sai suka yi ta tashi a arewacin India. Yayinda 'yan Sanda suka tsananta bincike, sai suka gano cewa wadannan ZINARI da Raees ya shigo dasu suna dauke ne da SINADARAN Bom na RDX.
Cikin kaduwa da nadama Raees yaje ya kashe Musabhai saboda cin Amana da yaudarar sa da yayi ta hanyar kashe mutane babu gaira babu dalili kawai don ya cimma wata Manufar sa. Shi kuma Majmudar take ya bada oda kan cewa da anga Raees kawai a bude masa wuta, amma Raees sai ya zo da 'Yan Jarida ya mika kansa wa hukuma duk da cewa yasan Majmudar kashe shi zai yi. Daga nan Majmudar sai ya tafi da shi wani wuri can bayan gari ya Harbe shi.
Jaruman Fim Din
* Shah Rukh Khan = Raees Alam
Mahira Khan = Aasiya Alam, Raees
Nawazuddin Siddiqui = IPS Jaideep Ambalal Majmudar
Mohammed Zeeshan Ayyub = Sadiq
Sheeba Chaddha = Amina Alam
Atul Kulkarni = Jairaj Seth
Narendra Jha = Musa
Jaideep Ahlawat = Nawab
Uday Tikekar = Pasha Bhai
Pramod Pathak = CM
Utkarsh Mazumdar = Dr. Sanjanwala
Kundan Roy = Kalupor
Ashutosh Jha = Rasul
Sunil Upadhyay = Taufiq
Fareed Arif = Eijaz
Loveleen Mishra = Ratna madam
Anil Mange = Qasim
Anurag Arora = Damla
Sanjay Gurbaxani = Commissioner
Raj Arjun = Ilyas
Bhagwan Tiwari = Sipeta Devji
Shubham Chintamani = Raees Yana Karami
Shubham Tukaram =  Sadiq Yana Karami
Sunny Leone = "Laila
Haiman Khan Raees
@HaimanRaees
08185819176
Infohaiman999@gmail.com

Post a Comment (0)