SHARHIN FIM DIN JAB TAK HAI JAAN

SHARHIN FIM DIN JAB TAK HAI JAAN
Jab Tak Hai Jaan Fim Din India ne da akayi a 2012, sannan Fim Din ya kunshi labari ne akan soyayya. Fim Din shi ne karo na biyu da Jaruma Anushka Sharma ta fito tare da Jarumi Shah Rukh Khan bayan Haduwar su a cikin Fim Din Rab Ne Bana Di Jodi, kuma shi ne Fim na farko da Jarumin ya fara Fim da Jaruma Katrina Kaif. Bugu da kari da wannan Fim ne Shahararre Yash Chopra ya dawo bakin aiki bayan hutu na tsawon shekaru 8 tun bayan fitar da Fim Din Veer-Zaara. Kuma shi ne Fim Din sa na karshe Kasancewar ya mutu a wannan shekarar yana da shekaru 80.
A. R. Rahman shi ne ya hada Kida da sautin Fim Din, Yayinda  Gulzar kuma ya rubuta Wakokin.
Sunan Fim Din Da Hindi - जब तक है जान
Bada Umurni - Yash Chopra
Daukar Nauyi - Aditya Chopra
Labari - Saiyf Jilani
Tsarawa - Aditya Chopra
Da Devika Bhagat
Jarumai - Shah Rukh Khan,
Anushka Sharma Da
Katrina Kaif
Hada Sauti - A. R. Rahman
Dauka Da Kyamara - Anil Mehta
Tacewa - Namrata Rao
Kamfanin Da Ya Shirya - Yash Raj Films
Ranar Fita - 12 November 20 (Mumbaai)
13 November 20 (India, United States, Europe)
Tsawon Fim Din - Minti 176
Kasa - India
Yare - Hindi
Kudin Da Aka Kashe - Crore Miliyan ₹780
Kudin Da Ya Kawo - Crore Biliyan ₹2.11
Jab Tak Hai Jaan labari ne akan wata Ma'aikaciyar gidan Talbijin mai suna Akira Rai wacce ta ci karo da littafin Samar Anand (Shah Rukh Khan ), Kwararren Madatsin Bama Bamai. Littafin ne ya bayyana mata irin yadda yayi fama a garin Landan, tare da bayyana yadda akayi ya hadu da Meera Thapar (Katrina Kaif ).
An saki Fim Din ne a Tsakankanin kwanakin hutu na Diwali Wanda ya fara daga 13 November 2012. Jab Tak Hai Jaan sai da ya zama Fim na uku da yafi kowane Fim Din Bollywood kawo kudi a Kasuwancin kasashen waje a wancan lokacin a bayan 3 Idiots da My Name Is Khan (2010).
LABARIN FIM DIN
Samar Anand ( Shahrukh Khan ), Babban Mai Mukami a cikin Sojojin India, ya datse wani Bam a
Ladakh ba tare da wani shayi ko Fargabar abinda ka iya samun shi ba.
Bayan ya ceci Akira Rai (Anushka Sharma), Ma'aikaciya a Tashar Discovery Channel, Yayinda ta fada ruwa mai matukar sanyi inda ta kusa mutuwa. Yayinda ya taimake ta, sai ya bata rigarsa, wacce ya tafi bai amsa ba. A cikin aljihun rigarsa ne ta tsinci littafin sa wanda yake rubutu a cikin sa.
Littafin yana Kunshe ne da labarin irin kalubalen da Samar ya Fuskanta a Farkon rayuwar sa ta Baindiye Mazaunin Landan wanda yake aiyuka iri iri don ganin ya kula da kansa da kuma abokin zaman sa Zain.
Watarana, sai ya ga Meera Thapar (Katrina Kaif ) a kofar wani Coci, nan take ya kamu da sonta. Yana aiki a matsayin mai bada abinci kuma sai ya sake ganin Meera tare da wanda zata aura mai suna Roger a wurin Shagalin su, hakan ne ya karya masa Zuciya. Meera ta Girma ne ba tare da mahaifiyar ta ba. Kasancewar mahaifiyar tata (Neetu Singh) ta bar gidan domin Kasancewa tare da wani can daban (Rishi Kapoor) lokacin Meera tana da shekaru 11 tare da Mahaifinta (Anupam Kher ) a matsayin mai kula da ita, kuma tana aiki ne a Kamfanin sa.
Meera sai ta bukaci Samar da ya koya mata Wakar 'yan Punjabi domin ta rera ta a yayin bikin Zagayowar ranar haihuwar babanta karo na 50, shi kuma sai yace sai dai in ta amince zata koya masa turanci na tsawon wata daya domin ya gyara turancin sa, dukkan su sai suka yarda da hakan.
Samar sai ya fahimci cewa Meera tana yawan zuwa Coci yin Addu'a. Bayan sun Tika rawa a wani dare a kan titi, sai suka fara son Junan su. Samar sai ya dinga Taimakawa Meera wajen gyara rayuwar ta da Mu'amalar ta, inda har ya dauke ta ya kaita wajen Mahaifiyar ta domin suyi Sulhu. Meera sai ta yanke Shawarar kawai ta fadawa Mahaifin ta Burin ta na kasancewa tare da samar da kuma kyale wancan maganar auren ta na farko. Kwatsam sai Samar ya samu hatsari, Meera sai tayi tunanin itace Sanadin Mummunan halin da ya shiga, nan dai ta roki ubangiji da ya Tseratar da rayuwar sa, sannan ta sha Alwashin ba Zata kara kula shi ba.
Bayan Samar ya warke, sai Meera ta fada masa hukuncin da ta yanke. Cikin fushi, shi kuma sai ya Barta da Landan din gaba daya ya Koma gida tare da Kalubalantar ubangiji da ya ci gaba da Tseratar da rayuwar sa Yayinda shi kuma zai ta jefa rayuwar sa cikin Hadari a kullum. Domin yayi imani cewa Mutuwar sa ce kawai zata sa Meera ta sauko daga inda Zuciyar ta tahau.
Bayan ya Koma India ne ya Shiga aikin soja, inda ya zama Kwararren Madatsin Bam. Bayan Akira ta gama karanta littafin tana mai kuka, sai ta roki da a bata dama ta hada wani Fim na Tarihin Madatsan Bama-Bamai, ta haka ne ta kulla abota da samar. A haka dai har ta fara son Samar wanda shi kuma Sam yaki amincewa da soyayyar tata saboda so Da kaunar da har yanzu yake yiwa Meera.
Cikin sa'a ta kammala Fim Din ta, kuma ta roki samar da ya raka ta Landan domin ta gabatar da shirin nata. Bayan ta dame shi dai da Magiya sai ya amince. Yayinda suka isa Landan, sai mota ta buge samar, bayan an kaishi asibiti ne aka Bayyanawa Akira cewa ya samu buguwa a Kwakwalwar sa ta yadda ya mance duk wani abu da ya faru da shi bayan Hadarin farko da yayi kimanin shekaru goma da suka wuce.
Cikin damuwa, Akira ta san yadda tayi ta Kwakwulo Meera tare da Matsa mata lamba domin ta taimaka wa Samar wajen samun lafiyar sa. Meera sai ta yarda, tare da yiwa Samar karyar ai sunyi aure ne ma kafin ya samu Hadarin. A haka ne Akira ta Fahimci cewa Mejo Samar ba komai bane face wani bangare daban na Samar, Kasancewar mutum ne shi mai son wasa da dariya Da nishadi, Yayinda yanzu kuma yake cikin kadaici da damuwa.
Watarana, Samar sai yayi karo da wani Bam da aka dasa a daya daga cikin hanyoyin garin Landan. Inda ya Datse shi yana mai ganin Jirijiri. Wannan al'amari ne fa yasa ya dawo hayyacin sa tare da gano cewa Meera karya take yi. Don haka sai ya ritsa Meera a Cocin da take yawan yin addu'a tare da bata zabi biyu, ko dai ta amince ta ci gaba da rayuwa tare da shi ko kuma ya ci gaba da kasada da rayuwar sa har ya mutu.
Meera sai ta kasa bashi amsa, domin zuciyata ta karaya. Daganan Samar ya tafi kashmir. Yayinda suke Zantawa da Akira ne Meera ta fahimci cewa, wannan kekashewar nata fa ya saka samar a wani tashin hankali ne wanda yafi mutuwa kuna. Don haka sai ta nufi Kashmir. A dai dai lokacin ne kuma Akira take bada labarin Samar a Landan, Yayinda shi kuma yake datse bam dinsa na karshe. Sannan ya bayyana soyayyar sa ga Meera.
Fim Din ya kare ne da bidiyon Yash Raj Chopra a yayin daukar Fim Din Jab Tak Hai Jaan kafin Mutuwar sa.
JARUMAN FIM DIN DA MATSAYIN SU
Shah Rukh Khan - Major Samar Anand
Katrina Kaif - Meera Thapar
Anushka Sharma - Akira Rai
Sarika - Dr. Zoya Ali Khan
Prerak Patel Frank
Sharib Hashmi - Zain
Jahidul Islam Shuvo -
Jasmine Jardot - Maria
Gireesh Sahedev - Captain Jagdeep Deewan
Amarinder Sodhi - Captain Kamal Singh
Varun Thakur - Lieutenant Hari Krishnan
Jay Conroy - Roger
Anupam Kher - Mr Thapar
Rishi Kapoor - Imraan
Neetu Singh as Pooja
A Yuni  2011, Kamfanin Yash Raj Films Suka sanar da cewa Yash Chopra zai dawo bada umurni tare da bikin cikar sa shekaru 50 da fara aikin sa a Bollywood. Sannan kuma suka ce za'a saki Fim Din ne da bikin Diwali na 2012.
Chopra Yace a wancan lokacin ba'a riga an sakawa Fim Din suna ba kamar Fim Din su na baya Veer-Zaara wanda sai a ranar da za'a kaishi wajen tace Fim Din sannan aka saka masa suna. Furodusoshin Fim Din sunyi ta kai kawo akan sunaye da dama da zasu sawa Fim Din amma duk basu samu nutsuwa da shi ba.
A cikin watan Satumba 2012 ne aka bayyana cewa sunan Fim Din zai kasance i Jab Tak Hai Jaan ne. Kuma wannan suna an samo shi ne daga wata Wakar Fim Din Sholay.
Aditya Chopra yana so mahaifinsa ya sake yin wani Fim, don haka sai ya Tunkare shi da batun Jab Tak Hai Jaan . Shah Rukh Khan shi ne Jarumi na farko da suka fara zaba a matsayin wanda zai Jagoranci shirin, Kasancewar suna da alaka mai karfi a tsakanin su ta hanyar Fim da kuma Mu'amala.
Kasancewar Shah Rukh Khan yana shirya wasu Fina Finan a wancan lokacin, sai aka canja lokacin yin Fim Din. Kamar dai Fina Finan sa na baya, Yash Chopra yana so ya hada Jarumi Shah Rukh Khan Da wata Jaruma Wacce bai taba aiki da ita ba a baya, don haka sai ya zabi Katrina Kaif.
Jaruma Anushka Sharma kuma an saka ta a matsayin mai takewa Jaruman baya ne domin ta cike Kwantiraginta na Fina Finai uku da tayi da Yash Raj Films. Duk da cewa tsara Jaruman da zasu fito a Fim Din an gama Shi nan da nan, fara Fim Din sai da ya dauki lokaci sosai, saboda manyan Jaruman Fim Din suna wasu Ayyukan a wancan lokacin.
Yanayin Da Jarumi Shah Rukh Khan ya fito da shi a Fim Din guda biyu ne, daya a matsayin dan shekaru 28, wanda yake Wake-Wake a kan titunan birnin Landan. Daya kuma a Matsayin Meja mai sanin Makamar aiki a Kashmir.
Shah Rukh Khan ya bayyana cewa Samar mutum ne mai "Fushi, Rashin Yafiya da sauran halaye Makamantan hakan".
Sannan jarumin ya kuma cewa, samar mutum ne da ya tara halaye da yawa, yana da kula, fushi da kuma rashin Yafiya, a takaice dai tamkar ni yake.
Jaruma Katrina Kaif tayi aiki tukuru kafin ta samu Damar yin abinda ya dace tayi a Fim Din tare da taimakon Jarumi Shah Rukh Khan.
An so a fara daukar Fim Din ne tun a watan Nuwambar 2011, amma sai aka dakata saboda Jarumi Shah Rukh Khan yana so ya huta bayan kammala Fina Finan sa guda biyu, wato Ra.One da Don 2.
An fara daukar Fim Din ne a ranar 9 ga watan Janairun Shekara ta 2012 a studio din Yash Raj Studios dake Mumbaai, inda aka taba aikin sosai a wajen. Bayan sun kammala Shirin a India, sai kuma suka Dunguma izuwa Landan a ranar 22 ga watan Fabrairun shekara ta 2012, inda sukayi kwana 25 suna aiki a karkashin sunan PRODUCTION 45.
Shah Rukh Khan ya isa Landan ne a ranar 21 ga watan Fabrairun shekara ta 2012,kuma Ya kammala a ranar 26 ga watan Maris 2012. Ana kan daukar Fim Din ne wani Ya fitar da hotunan Jaruman Fim Din a Yanar gizo. Hakan yasa aka hana shiga wurin da Kyamarori kuma aka kara Tsaurara tsaro.
An nuno Wurare da dama a cikin Fim Din Jab Tak Hai Jaan , irin su Borough Market , Jubilee Walkway , the Great Conservatory, the Palace of Westminster , Westminster Bridge,
Trafalgar Square, the Hungerford Bridge, Golden Jubilee Bridges ,
O2 Arena , Tower Bridge, da kuma
Canary Wharf .
An dauki wata Waka a kusa da King's College London law school a Somerset House. Yayinda aka dauki sin din hatsarin mota a Shepherd's Bush ta hanyar rufe Hanyoyin hudu duka. An kammala daukar Fim Din ne a ranar 27 ga watan Maris 2012.
Rawar Wakar "Ishq Shava" an yita ne da 'yan rawa a wani gidan casu dake karkashin kasa da kuma cikin Jirgin ruwa a kogin River Thames.
An so a dauki karshen Fim Din ne a Kashmir, amma sai aka maida shi Ladakh bisa Shawarar Shah Rukh Khan, saboda anan ne aka yi wani tsohon Fim Din sa mai suna Dil Se. Wani bangare na Fim Din Jab Tak Hai Jaan an shirya shi ne a Garuruwa uku dake kashmir, sune: Srinagar, Pahalgam , da kuma
Gulmarg .
Yash Chopra yaso ya kara wasu Sinasinai a Wakar Fim Din, amma ba'a samu Damar yin hakan ba saboda Mutuwar da yayi. Aditya Chopra yace Abar Fim Din a yadda yake, domin a ganin sa, sake wani abu daga cikin sa kamar batawa mahaifinsa aikin sa ne.
Wakokin Fim Din Jab Tak Hai Jaan.
Shahararre A. R. Rahman shi ne ya hada Kida da Sautin Fim Din, kuma wannan shi ne karo na Farko da suka fara aiki da Yash Chopra. Ya sa hannun fara aikin ne a watan Mayu 2011. Sannan ya kammala Wakar Farko Daga cikin Wakokin Fim Din ne a watan Disambar 2011.
Kundin Wakokin Fim Din ya kunshi Wakoki tara ne, Gulzar shi ne ya rubuta TAKWAS daga cikin su, Yayinda Aditya Chopra. An saki wannan kundi ne dai a Karkashin Kamfanin YRF Music a ranar 9 ga watan Oktobar 2012.
Fim Din Jab Tak Hai Jaan an Fitar Da Shi ne tare da Fim Din Ajay Devgn mai sySon Of Sardar a ranar 13 November 2012, duk da cewa Shi Ajay din ya Shigar da Karar cewa Yash Raj Films sun Mamaye Sinimomin India mafi yawa domin nuna Fim Din su, kotun tayi Watsi da korafin sa.
LAMBOBIN YABO (AWARDS)
Jab Tak Hai Jaan ya samu lambobin Yabo masu yawa. An yabawa Fim Din Matuka wajen bada umurnin sa, tsarin sa da kuma irin alakar dake tsakanin Jaruman Fim Din. Har ma Shahrukh Khan Da Anushka Sharma sun sami lambobin Yabo, amma wasu da dama sun kushe tsarin labarin Fim Din.
Fim Din ya samu lambobin yabon
Filmfare Awards guda hudu, five Zee Cine Awards guda biyar da kuma Colors Screen Awards guda biyu.
Haiman Khan Raees
@HaimanRaees
08185819176 Infohaiman999@gmail.com

Post a Comment (0)