SHARHIN FIM DIN KA HO NA PYAAR HAI

KA HO NA PYAAR HAI
Ka Ho Na Pyaar Hai (Kice Kina Sona/Kace Kana Sona) Kayataccen Fim ne da ya fita a shekara ta 2000, Kuma wannan Fim shi ne Fim na farko da Jarumi Hrithik Roshan da Jaruma Ameesha Patel suka fara yi. Anyi wannan Fim ne Sanadiyyar kwarin guiwar da Marubucin Fim Din ya samu bayan samun nasarar wani Fim Din Kannada mai suna Kannada RATHA SAPTHAMI (1986) wanda Jarumi Shivarajkumar da Asharani suka fito a cikin sa.
Sunan Fim Din Da Yaren Hindi =
कहो ना प्यार है
Bada Umurni =
Rakesh Roshan
Daukar Nauyi =
Rakesh Roshan
Labari Da Rubutawa =
Rakesh Roshan
Tsarawa =
Ravi Kapoor
Da
Honey Irani
Hada Kida = Rajesh Roshan
DAUKA Da Kyamara =
Kabir Lal
Tacewa = Sanjay Verma
Kamfanin Da Ya Shirya =
Filmkraft Productions (I) Pvt. Ltd
Kamfanin Da Ya Yada =
Eros International
Ranar Da Ya Fita =14 January 2000
Tsayin Fim Din = Minti 178
Kasa = India
Harshe = Hindi
Kudin Da aka Kashe ma Fim Din =
5 crore
Kudin Da Ya Kawo = $200 crore
Ka Ho Na Pyaar Hai shi ne Fim Din Bollywood Da yafi kowane Fim samun Nasara a shekarar 2000, Domin Limca Book of Records sun rubuta shi a matsayin Fim Din Bollywood Da Yafi Kowane Fim Samun Lambobin Yabo masu yawa. Da wannan Fim ne Rakesh Roshan ya fara cin Lambar Yabo ta Filmfare Inda ya samu a matsayin Daraktan da yafi kowa nuna Bajinta, kuma a sanadiyyar wannan Fim ne Hrithik Roshan ya zama Sananne cikin dan kankanin lokaci. Sannan a sanadiyyar wannan Fim ne ya kafa wani babban Tarihi a India, inda Ya lashe Kyautar Sabon Jarumi Da kuma Kyautar Jarumin Jarumai ta Filmfare duk shi daya, a shekara daya, kuma da Fim daya.
Labarin Fim Din
Rohit Mehra tare da kanin sa Amit Marayu Ne wadanda suke zaune a hannun Lily Da Anthony. Rohit Matashin Mawaki ne wanda yake aiki a Karkashin Malik. Watarana sai suka hadu da Sonia Saxena, 'Ya a wajen Mr. Saxena Yayinda yaje ya ajiye mota a gidan su a matsayin Kyautar zagayowar ranar haihuwar ta.
Ba tare da sanin kowa ba, ashe Malik da my. Saxena suna harkallar Miyagun Kwayoyi tare da samun hadin kan wasu ofisoshin 'Yan Sanda Guda biyu. A wannan rana kuma dai sai Rohit da Sonia suka sake haduwa a bakin wani kogi inda ita da abokan ta da kawayenta suka hada Casu domin taya ta Murna. Bayan Rohit Yayi mata Waka, sai Atul dan Malik Kuma abokin Sonia ya gayyace shi da ya shigo katon jirgin ruwan domin ya Nishadantar da su.
A garin wannan shagali ne Rohit da Sonia suka bugu da kayan maye har suka fada cikin wani dan karamin kwalekwale wanda daga karshe dai ya rabu da ainahin jirgin da ake Shagalin a cikin sa, suka tafi can suka tsinci kansu a wani Tsibiri. A dan wannan zama da suka yi a wannan Tsibiri ne suka kamu da son junan su.
A karshe dai Mr. Saxena ya zo ya cece su tare da mutanen sa, kuma Ya fahimci soyayya ta shiga tsakanin su
Kuma ya nuna rashin Amincewar sa. Har ma ya nemi Malik da ya kori Rohit daga aiki. Sonia tayi iya kokarin wajen nunawa Mahaifinta cewa Rohit mutumin kirki ne, amma yaki ji, har ma yake bayyanawa Rohit din cewa lallai ne ya tabbatar ya samu nasara a rayuwa tukun kafin ya sa ran samun Sonia, tunda dai ita 'yar manya ce. Domin ya cimma Manufarsa, sai Rohit da abokan sa suka zage damtse har dai ya zama shahararren Mawaki har ma yana shirin hada show nashi na kan shi.
A ranar da za'a yi show din, Rohit yaje makarantar su Amit domin ya dauko shi, sai Rohit yaga Malik da wadannan Munafukan 'Yan Sanda su biyu a lokacin da suka kashe Kwanishina wanda ya gano Mummunar harkallar Miyagun Kwayoyin da suke yi. Yayinda suka Ankara cewa Rohit na wurin sai suka rufe shi da harbi har suka ji masa ciwo. Ya nemi guduwa a mashin suka bishi har yakai kan wata Gada inda ya fada cikin ruwan, Kasancewar bai iya linkaya ba, sai ya nutse a ruwan ya mutu. Kanin sa Amit kuma ya shiga Mawuyacin hali a sakamakon hakan.
Sonia ita ma sai ta shiga cikin Matsanancin hali saboda mutuwar Rohit. Bayan an dan kwana biyu, sai baban ta Mr. Saxena ya tura ta New Zealand domin ta zauna tare da Dan uwansa. 'Yar Uwar ta Neeta ce tayi ta kokarin ganin ta rage mata damuwa ta hanyar janta suna fita Shakatawa. A garin haka ne suka hadu da abokin Neeta Raj Chopra
Wanda suka yi matukar kama da Rohit, kuma shima Mawaki ne. Raj sai ya kamu da son Sonia, amma Kamannin sa da Rohit sai ya kara haddasawa Sonia wata Sabuwar damuwar.
Yayinda Raj ya fahimci halin da take ciki sai ya yanke Shawarar binta India su koma tare, Yayinda suka isa India, sai daya daga cikin Munafukan 'Yan Sandan nan ya gansu kuma nan take ya budewa Raj wuta. Bayan sun samu sun tsira ne, sai Raj ya Fahimci cewa kashe Rohit aka yi kuma wani yana tunanin shi ne Rohit din.
Mutanen gidan su Rohit sun karbi Raj Hannu biyu haka ma abokan sa. Kasantuwar sa a tare da su ne yasa Amit ya fita daga damuwa, kuma a nan ne ya fahimci cewa Amit yaga lokacin da aka kashe Rohit. Daga nan sai Raj ya yanke shawara dana tarkon da zai fallasa wadanda suka yi kisan ta hanyar maye gurbin Rohit, amma Sonia da abokan Rohit ne kawai suka san da hakan.
Daga nan Raj ya bayyana soyayyar sa ga Sonia, duk da cewa ita ma tana son shi, har a wannan lokacin tana cikin Jimamin Rohit, hakan yasa ta kasa amsa masa.
Yayinda Malik ya fahimci cewa Rohit yana raye sai hankalin sa ya tashi. Raj kuma sai yayi rawa a wani show na musamman domin Rohit. Malik da abokan sa Munafukan nan suma sun halarci taron, shi kuma Mr. Saxena saiya fahimci halin da ake ciki ta hanyar Sonia, don haka sai ya kyankyasawa Malik. Bayan an kammala taron, sai Raj ya bayyana wasu boyayyun bayanai dangane da kisan wanda ya ji daga wajen Amit.
Saboda haka, sai Malik yayi tunanin Raj dai Rohit ne na gaskiya, Mr. Saxena kawai so yake ya yaudare shi. Kafin Raj ya bayyana sunan wadanda suka kashe Rohit, sai daya daga cikin Munafukan nan ya Harbe shi, amma bai masa illa ba saboda yana sanye da riga mai bada Kariya daga harbi.
Saboda su kama Raj wanda suke tunanin Rohit ne, Munafukan nan sai suka sace Sonia. Raj kuma ya sheke su duka tare da Mukarraban su kuma ya kwato Sonia. Ana haka kuma sai ga Malik ya diro wajen, yayin da yake kokarin bayyana hadakar sa da Mr. Saxena, sai shi Mr. Saxena din ya Harbe shi wanda ransa ya baci saboda sace masa 'Yarsa da yayi.
Ana haka kuma sai ga Amit, wanda nan take ya gane Malik a matsayin wanda ya kashe Rohit, kuma Ya fada masa cewa a ranar da abun ya faru yaji Malik na waya da wani mai suna SIR JI a waya. Raj sai ya dauki wayar Malik ya lalubo sunan sannan ya danna kira, kawai sai akaji wayar Mr. Saxena tana ruri. A nan ne Raj ya fahimci komai, don haka sai ya tuhumi Saxena wanda ya amsa laifin sa a gaban Sonia da Raj kafin azo a kama shi.
Daga nan Sonia da Raj suka koma New Zealand tare da Amit domin suyi auren su a can su Caskade.
Daga nan Sonia da Raj suka koma New Zealand tare da Amit domin suyi auren su a can su Caskade.
JARUMAN FIM DIN DA MATSAYIN DA SUKA FITO DASHI A FIM DIN
Hrithik Roshan - Rohit Mehra / Raj Chopra
Ameesha Patel  - Sonia Saxena
Anupam Kher - Mr. Saxena / Sirjee
Dalip Tahil - Shakti Malik
Mohnish Behl - SIPETA Kadam
Ashish Vidyarthi - Sipeta Shinde
Satish Shah - Anthony Rodriques
Farida Jalal - Lily Anthony Rodriques
Rajesh Tandon - Atul Malik
Asha Patel  Mrs. Chopra
Tanaaz Currim - Neeta Saxena
Vrajesh Hirjee - Tony
Abhishek Sharma - Amit Mehra
Johnny Lever - Sipeta Parab
Ram Mohan - Kwanishina
Kamya Punjabi - Shobha
Asali da da Kareena Kapoor zasu fito a cikin Fim Din, amma saboda Sabanin fahimta da suka samu da maman ita Kareena Kapoor din mai suna Babita, sai Jarumar ta fasa Fitowa a Fim. Daga nan sa Rakesh, wanda dama can akwai Sanayya tsakanin sa da iyalan gidan su Ameesha Patel sai kawai ya Sata a cikin Fim Din.
Kaho Naa... Pyaar Hai ya samu Karbuwa sosai a wurin Jama'a da masu sharhin Fina Finai domin sai da ya zamo Fim Din da yafi kowane Fim Karbuwa a wannan shekarar.
Kidan Wakokin Fim Din Rajesh Roshan ne yayi su. Yayinda Saawan Kumar Tak , Vijay Akela and Ibrahim Ashq suka rubuta Wakokin Fim Din.
Raye Rayen da akayi a cikin Fim Din kuma Farah Khan ce ta koyar da su.
album din Wakokin Fim Din yayi kasuwa sosai domin sai da aka siyar kwafi  Miliyan goma.
WAKOKIN FIM DIN
1. "Kaho Naa Pyaar Hai"
2. "Na Tum Jano Na Hum"
3. "Pyaar Ki Kashti Mein"
4. "Janeman Janeman
5. "Chand Sitaare"
6. "Janeman Ki Mehfil Me Goonjega Tarana",
7. "Dilwalo Dil Mera Sunne Ko Bekarar Hai"
8. "Kaho Naa Pyaar Hai (Sad Version)"
9. "Ek Pal Ka Jeena"
10. "Believe in Love (Theme Music)" Instrumental
Lambobin Yabo
46th Filmfare Awards Best Film
Rakesh Roshan Best Director
Best Actor Hrithik Roshan Best Debut Male
Best Music Director Rajesh Roshan
Best Playback Singer Lucky Ali
Best Screenplay Ravi Kapoor &
Honey Irani
Best Choreography Farah Khan
Best Editing Sanjay Verma
Star Screen Awards
Best Film Rakesh Roshan Best Director
Best Actor Hrithik Roshan
Best Music Director Rajesh Roshan
Best Male Playback Lucky Ali
Screen Award for Most Promising
Newcomer – Male Hrithik Roshan
Screen Award for Best Screenplay Honey Irani &
Ravi Kapoor
Zee Cine Awards
Zee Cine Award for Best Film Rakesh Roshan
Zee Cine Award for Best Director
Zee Cine Award for Best Actor - Male Hrithik Roshan
Zee Cine Award for Best Male Debut
Zee Cine Award for Best Female Debut Amisha Patel
Zee Cine Award for Best Playback Singer – Male Lucky Ali
Zee Cine Award for Best Playback Singer – Female Alka Yagnik
Zee Cine Award for Best Music Director Rajesh Roshan
IIFA Awards Best Movie Rakesh Roshan
Best Director
Best Actor Hrithik Roshan Best Debut - Male
Best Music Director Rajesh Roshan
Best Male Playback Lucky Ali
Best Female Playback Alka Yagnik
Channel V Awards Best Film Rakesh Roshan Best Director
Best Actor Hrithik Roshan Best Male Debut
Best Music Director Rajesh Roshan
Best Male Playback Singer Kumar Sanu
Haiman Khan Raees
@HaimanRaees
08185819176
Haimanraees@gmail.com

Post a Comment (0)