Assalamu alaikum
Takaitaccen sharhi akan film din RAMAIYA VASTAVAIYA.Wanda Ni Ikramkhan(Veeron ke veer)na kawo maku. Shiri ne da akayi shi akan ..... Zamantakewa na yau da kullun,jajircewa da kuma Soyayya.
An fara shirya wannan film a 25 April 2013,sannan ansaki shirin a 19 July 2013.
Daraktan shiri: Prabhudheva
Produsa: Kumar S. Taurani
Rubutawa: Shiraz Ahmad
Kampani: Tips Industries Limited.
Jaruman shirin: Grish kumar(Ram). Shruti Hassan(Sona). Sonu Sood(Raghuveer). Poonam Dhillon(Ashwini). Randhir kapoor(Siddharth). Vinod khanna(Jami'in jirgin kasa) Da sauran su.
Yanzu bara mu tsunduma cikin shirin..
Idan muka duba hannu na da dama zamu ga Ram(Girish kumar) mai kudi ne shi,dan zamani,mahaifinsa hamshakin mai Kudi ne daga Qasar Australia. Idan kuma muka duba hannuna na hagu,zamuga Sona(Shruti Hassan) 'yar gargajiya ce daga garin Punjab,ta girma ne tare da dan uwanta guda daya tilo- Raghuveer( Sonu Sood). Sun sami tawayan rayuwa ne,yayin da mahaifinsu ya auri wata mace,ya wulakanta su,ya kore su waje,hakan yay sanadiyan mutuwar mahaifiyar su,bayan sun burne ta awani fili nasu,kwatsam saiga wani mai suna Zamindar,yace wannan fili mallakinsa ne,mahaifiyarsu ce ta ara agurinsa,don haka sai ancire kabarin ta afilin,Raghuveer ya roka zaiyi aiki dare da rana don ya biya fansan filin,Zamandar ya amince da hakan.Tare da taimakon wani jami'in jirgin kasa (Vinod khanna) suka girma.
Wata rana babbar kawa ga Sona (Riya)ta gayyace ta izuwa daurin aurenta,a wannan rana kuma Causin din Riya ( Ram) yazo tare da mahaifiyar sa Ashwini (Poonam Dhillon). A hankali a hankali Ram ya kamu da soyayyar Sona,amma ita mahaifiyar Ram bata son hada dangantaka da ahlin Sona,saboda su talakawane,tafi son Ram ya auri 'yar abokin kasuwancin dan uwanta (dolly). Ayayin da dan uwan Sona (Raghuveer) yazo ziyartar auren,sai Ashwini ta wulakanta su,takai ga har suka bar gidan,shi Ram baisan da faruwar hakan ba,yayin da Ram yasami labarin hakan,abin bai masa dadi ba,yaje gidan su Sona,yanemi yafiya bisa wulakancin da akai masu,sannan ya nemi iznin auren Sona. Da fari Raghuveer yaki amince wa, amma daya fuskanci cewa kanwarsa na son shi Ram din,sai ya bashi daman yi masa jarabawa,idan yaci jarabawar sannan zai amince,jarabawar itace kula da dabbobi da duk dawainiyar su,sannan sai yayi noma fiye da abinda shi Raghuveer din ya noma a karshen damina,idan ya fadi jarabawar,to babu shi ba Kanwarsa. A can wani gefe kuma akwai yaron Zamindar,wanda shima yana son Sona,sukai ta yima Ram bita-da-kulli don suga Ram ya fadi wannan jarabawar,shi kuwa Ram aiki yake dare da rana don ganin yayi nasara wa soyayyar sa,karshe dai Ram yayi nasara
Ana cikin hakan,sai Zamindar da dansa suka sace Sona,sukai kokarin yi mata fyade,Ram da Raghuveer da suka sami labarin abinda ke faruwa,suka farma Zamindar da magoya bayan sa,har ta kai ga Ram ya kashe Dan Zamindar,Raghuveer dayaga hakan ta faru sai ya dauki laifin kisan don kasan cewar Sona da Ram atare,aka yanke masa hukuncin shekara bakwai a gidan yari,Ram da Sona basui aure ba,har sai da Raghuveer ya fito daga gidan yari/kassu,sannnan ita mahaifiyar Ram (Ashwini)ta nemi yafiyar abinda tayi,kuma ta amince da auren su.
Wannan shine takaitaccen sharhin Shirin RAMAIYA VASTAVAIYA.
*KADUNA URDU KI FANS ZINDA BAAD.*
Tags:
Fina-Finai (Films)