SHARHIN FIM DIN MUJHSE DOSTI KAROGE

MUJHSE DOSTI KAROGE
Mujhse Dosti Karoge! Fim ne da aka yi shi a shekara ta 2002, labari ne akan wata soyayya da ta faru a tsakanin abokai uku.
Sunan Fim Din Da Hindi:
मुझसे दोस्ती करोगे
Bada Umurni:
Kunal Kohli
Daukar Nauyi:
Yash Chopra
Da Aditya Chopra
Rubutawa: Aditya Chopra
Kunal Kohli
HADA Kida: Rahul Sharma
Dauka da Kyamara:
Ravi K. Chandran
Kamfani : Yash Raj Films Pvt. Ltd
Ranar Fita: 9 August 2002
Tsawon Fim Din : Minti 149
Yare : Hindi
LABARIN FIM DIN
Raj Khanna, Pooja Sahani dayTina Kapoor (Kareena Kapoor ) abokai ne tun suna yara. Ko da yake Shi Raj yana Matukar son Tina, bai taba lura da irin Boyayyen son da Pooja take yi masa ba.
Watarana sai Mahaifin Raj ya yanke Shawarar komawa Ingila tare da iyalan sa domin ya fara wani sabon aiki a can din. Kafin su tafi, Raj sai da yasa Tina tayi mishi Alkawarin cewa zata rubuta masa Wasika ta Hanyar email. Ita kuwa Tina, Kasancewar ta 'yar son Shagali da Nishaɗi, nan da nan sai ta manta ma da wannan batun.
Don haka, sai Pooja ta dinga aikawa Raj sako ta email da sunan Tina domin ta taimaka mata ta cika Alkawarin ta da ta dauka. To shi Raj da Pooja tasu tazo daya, don haka sai wadannan Sakonnin da suke turawa juna ya kara dankon Shakuwa a tsakanin su. Haka aka ci gaba har tsawon shekaru goma sha biyar.
Watarana sai Raj yazo India domin yayi wani dan karamin hutu. Yanzu Kam ya kamu da son wanda suke Zantawa tare, don haka yake da yakinin zai iya gane ta nan take.
Amma Yayinda su ukun suka hadu, sai Raj ya maida hankalin sa kacokan kan Tina ya share Pooja, ita ma Tina a hankali dai sai ta fara son shi. To sai dai kuma a tsawon sati biyun da yayi a India ne ya fahimci cewa Tinar da suke Zantawa da ita fa ba itace wacce suke tare yanzu ba, kuma nan da nan sai abotar su da Pooja ta fara karfi Kasancewar tasu tazo daya, ba tare da sanin cewa itace wacce ya kamu da sonta ba.
Bayan ya Koma Landan, ita ma Pooja sai ta tafi can din domin yin wani gani. Raj sai ya tafi wani Coci da yake yawan zuwa, a nan ne ya ga Pooja tana yin wata Wakar da yake Matukar so, kuma a nan ne ya fahimci cewa Pooja ce take turo masa sako ba Tina ba, domin ya tura mata bayanai akan Wakar da kuma Cocin. Nan dai suka fahimci soyayyar dake tsakanin su kuma suka yanke Shawarar yin aure.
A can kuma India, kwatsam Sai baban Tina ya mutu yabar Tina ita kadai. Amma Burin sa na karshe ita ce Yana son Tina ta auri Raj, kuma Ya Bayyanawa Mahaifinsa Raj din.
Kasancewar Pooja tasan crew Tina ita ma tana son Raj, kuma gashi yanzu bata da kowa, sai taki ta amince ta auri Raj don kada ta karyawa Tinar Zuciya.
Suma iyayen Raj sai suka amince da maganar, ba tare da sun san cewa akwai soyayya mai karfi a tsakanin Pooja da Raj ba. Raj ya dage akan shi fa zai Fadawa iyayen sa gaskiyar abinda ke Faruwa, amma Pooja sai ta hana shi. Cikin fushi sai yayi Rantsuwa akan ba zai taba auren Tina ba sai dai in ita Pooja din zata auri wani daban a wannan ranar.
Rohan Verma dama abokin Raj ne wanda tun tuni yake son Pooja. Don haka sai Pooja ta amince zata aure shi a ranar da Raj zai auri Tina ba don tana son shi ba, sai dai don kawai ta biyawa Raj bukatar sa tare kuma da Samarwa Tina farinciki. Rohan sai ya fahimci cewa Pooja fa ba son shi take yi ba, amma sai ya basar duk da hakan.
A ranar daura auren ne Tina ta fahimci cewa Raj ya kamu da son Tina, don haka sai ta cire kayan bikin nata ta saka kayan gida. Bisa kuskure sai Raj ya buge 'yar tandar da ake zuba garin nan da miji ke shafawa matar sa a goshin ta yayin daura aure, aka ci sa'a kuma ya zuba akan Pooja, wanda a al'adance alama ce ta kulluwar aure. Nan fa Pooja ta fara kokarin kakkabewa amma sai Tina ta hana ta, tare da Amincewa da soyayyar su da Raj. Pooja sai ta baiwa Rohan hakuri wanda shi Sam ma bai damu ba.
Tina ta jinjina musu tare da gode musu bisa irin kaunar da suke mata wacce tasa zasu iya Sadaukar da soyayyar su domin ta. Fim Din dai ya kare ne Yayinda aka nuno Raj da Pooja sunyi aure.
WAKOKIN FIM DIN
1."Andekhi Anjaani"
2. "Jaane Dil Mein"
3. "Jaane Dil Mein 2"
4. "Mujhse Dosti Karoge"
5. "Oh My Darling"
6. "Saanwali Si Ek Ladki"
7. "The Medley"
Box office
The FIM DIN YA SAMU TALLA SOSAI KAFIN FITAR SA, SAI DAI BAI YI TAFSIRI SOSAI A INDIA BA, DOMIN DALA MILIYAN 6.8 KAWAI YA KAWO.
Haiman Khan Raees
@HaimanRaees
08185819176
Haimanraees@gmail.com

Post a Comment (0)