SHARHIN FIM DIN RAJA

SHARHIN FILMS..
Sunan Film: RAJA
Jarumai : Sanjay Kapoor da Madhuri dixit
Director : INDRA KUMAR
Shekara : 1995
An fara da wani taro na taya murnar zagayowar ranar haiwuwar wani me kudi me suna Bilju (PARESH RAWAL) inda a taron nan xaku fara tabbatar da soyayyar da sukewa juna Shi da wani dan Kaninsa RAJA da be wuce shekaru 7 ba kuma har ila yau dai a wannan lokacin yaron ya ya nuna damuwarsa na rashin ganin wata yarinya da suka shaqu me suna MADHU kanwar abokin yayansa watau RANA SAAB (MUKESH KHANNA) Suna cikin Maganar se ga Sunan Sun karaso cikin murna RANA ya fara tayashi birthday su ma yaron suka ware wani waje domin suyi wasa irin na yara madhu ta bawa Raja kyautar biyu tace wannan naka tunda kaine Raja ni kuma Rani se yace ai ke madhu ce nan suka gama abinsu daga gefe kuma an kira Bilju a waya a ka fada masa Kamfanin sa ya Kama da wuta nan ya rude suka tafi bayan ya tarar kome ya qone qurmus a take Rana yaxo tare da kanwarsa wanda tun suna yaran anso idan sun girma an hadasu aure amma bayan wannan asarar Rana ya Yanke duk wata alaqa dashi da kuma kanwarsa madhu da raja nan fa yara suka fara kuka bayan Rana ya tuqa mota ya tafi raja ya bisu a guje Shi kuma..... dan kada Kaninsa ya bisu shima ya tafi da gudu Ashe mota ta tawo nan ta bigeshi ya fada acikin wasu wayoyi shocking duk suka kama jikinsa bayan Raja ya farfado a gadon asibiti ne ya fara tambayar yayansa nan kowa ya Kasa fada masa suna kuka yaron ya fito cikin damuwa domin ya xagaya asibitin da kansa ko xe ga wane hali yayansa yake ciki ai kuwa yayi Sa'a ya ganshi sedai a wani matsanan cin hali har a lokacin kwakwalwar sa ta juye ba kowa ya fara fashe fashe nan yaron yana kuka yayi qoqarin taimaka masa amma bashi da karfin haka domin kuwa ya se da ya ji masa ciwuka dakyar ya daureshi daga bisani mutane suka karaso bayan an kara yi wa Bilju aiki ya dawo hayyacinsa tare da wani tsakanin soyayyar da yakewa Kaninsa Raja amma har a lokacin duk jikinsa be dawo daidai ba Maganar sa yana in ina sannan shi kansa karkarwa yake a kowane lokaci ana cikin wannan halin Raja ya girma ya zama Babba (SANJAY KAPOOR) Ba jimawa wata yarinya (MADHURI DIXIT) ta kamu da soyayyar sa inda Shi kuma bata soyayya yake ba bayan wani lokaci ya fahimci Ashe wannan yarinyar ce watau Madhu nan shima ya fara kulata daga bisani suka fara soyayya nan kuma Raja ya fadawa yayansa cewa wannan yarinyar ce fa nan fa ya nuna baxai so wannan soyayyar tasu ba amma suka nuna tsananin soyayyar da sukewa juna Sannan shima ya amince kuma yace da kansa xai je wajen yayanta Rana bayan wani lokaci suka tafi tare da kanin nasa Raja inda Rana yayi mamakin ganin su bayan ya yanke alaqar da take tsakanin su amma shi..... ya nuna masa cewa duk da su talakawa ne a yanxu amma yaran nan suna son junan su ya kamata a goya musu baya nan fa Rana da Kaninsa Bushwa (DALIP TAHIL) suka fusata sukace yanxu ma sunyi mata miji to bayan nan fa aka nuno Rana ya tara jamaar sa har yana nuna wani yana cewa shine xai auri karamar kanwarsa kuma yayi umarni a kirawo ta a gaban jamaa suka fito ita da Raja Tana cewa Shi kadai takeso nan fa Bushwa ya dauko bindiga xai harbeshi ita kuma madhu tace sedai akasheta a wannan lokacin Shi kuma Babban yaya watau Rana ya karbi bindigar yana mata fada kuma ya farfasa kwalaban giya na wajen da duk wani abun fashewa da yake tsakanin su yace yana so Raja ya nuna masa irin son yakewa madhu domin a matsayin yayan ta ya nuna mata soyayya a cikin shekaru kusan 20 ai kuwa ya fara taka kwalaban suna farfasa masa kafa tana kuka sbd me xaiyi haka amma shi tafiya yake har ya fadi a cikin su duk suka farfasa jiki anan Rana da Bushwa da sauran mutanan wajen suka fara dariya irin ta mugunta Shi kuma Raja ya kara fusata ya tashi ya karaso wajen ta riqeshi tana kuka Shi kuma yaje wajen Rana din yace bar mishi ita tunda yaga iyakarsa nan fa Rana ya fara dukan sa yana ce masa dan iska mara Kunya Sannan yasa aje a jefar dashi to a yayin da aka jefar dashi a gaban yayansa..... duk da ba daidai yake ba amma ya fusata ya dau makami yaje gidan su Rana din yana masifa Bushwa ya fito ai kuwa Bilju   ya fara dukan sa har se da aka kira police suka tafi dashi ba jimawa aka sakeshi saboda yana da gaskiya
Daga nan kuma Rana da Bushwa suka yanke hukuncin ayi Nisa da madhu yanda babu wanda xe San inda take Ashe duk matar Rana tana saurare tayi maxa taje ta fadawa Raja yaji dadin haka har ya bata wani matsayin kan cewa lallai idan tana wannan gidan to Shi da madhu baxa suyi nesa da juna ba yayi gaggawar bin su ya kwace ta dakyar bayan sun dawo gida Bilju ya daukesu yakaisu wajen da xa ayi musu aure bayan alaqalin ya tambaye su shin su biyun sun amince xasu xama mata da miji duk sukace eh Sannan ya basu takarda su saka hannu se suka jiyo murya daga waje Ashe Rana ne ya karaso nan ya nuna yanxu ya chanja raayi domin yana son abinda kanwarsa takeso tunda har raja takeso shima ya amince amma ba a nan xa ayi musu aure ba nan suka fara Murna musamman ita madhu to bayan nan Bushwa yake tambayar Rana meyasa xai yi haka Rana yayi dariya yace akwai shirin da yake ne..
To Rana kawo sadaki kamar yanda mata suke bayarwa Domin ya tabbatar da gaske yake inda Shi kuma Bilju ya nuna ai duk inda mace irin madhu take kamar haske ce a waje su basa bukatar kome to suna cikin wannan batun ne aka xo da Maganar tafiya kuma aka nemi Raja ne xaiyi yace Ah a domin baxai iya barin yayan sa ba yana bukatar sa a kusa kuma yana bukatar kulawa se Rana yace haba Raja muna raye kake Maganar nan ai duk mun xama daya shi din ai xai iya xama a gidan mu na kwana biyu nan itama madhu ta goyi bayan yayan ta kan yabar yayansa Shi dai ba a son ran sa ba amma ya amince nan duhu yayi bayan Raja ya tafi Ashe Su kuma Rana da Bushwa Sun dauko wani me irin yanayin shi Bilju kuma sun koya masa irin Maganar sa Ashe duk matar Rana tana saurare  amma anyi rashin Saa Sun gan ta nan Rana ya fara mata masifa meyasa taxo tace eh kuma duk taji kome kuma ta fahimta Sannan xataje ta fadawa madhu kome nan ne Rana yace Kinaso na cire miki wannan sarqar ta auren mu watau su rabu ta nuna bataso yace to ta rufe bakin ta bayan nan cikin dare madhu ta raka Madhu da kyar ya Kwantar da hankalin sa ya kwanta saboda haka yanayin jikin sa yake da tsoro.
Bayan madhu ta Kwantar dashi ta tafi daki wancan ma ya shiga da yake ta Kashe fitila kawai se taji motsi tace waye yace ai.... tace kaje kayi bacci mana nan yayi kanta suka fara kokawa acikin duhu ta samu tayi ihu a yayin da Bilju Yaji ya fito da sauri bayan Rana da Bushwa Sun tabbatar ya shiga suka bi bayan sa shi kuma wancan ya tura Bilju kan madhu anan su Rana suka kunna fitila ta fara kuka taje tana fada musu kome to Bushwa ya samu abinda yakeso ya dauko makami yana dukan.... Shi kuma Rana ya kira asibitin mahaukata suka ce ya samu matsala daga nan Raja ya dawo daga aikin da ya tafi yaxo musu da tsaraba ya fara haduwa da madhu yana farin ciki ga tsaraba yaxo musu da ita ga nata ga na yayanta Rana da Bushwa Sannan yace ina kuma yayana duk taqi magana nan yasan da matsala yaje yana tambayar suma yayyan nata da suka fahimci ya damu se Rana yace yana gidan mahaukata nan take Raja ya fusata yana tambayar waye ya kaishi Jikin sa ya bashi tabbas da sa hannun Bushwa ya fara dukan sa madhu ta xo Tana masa fada ya daina taba mata yayanta domin basa hannun su Shi mahaukacin yayan ka shine mai laifi a take idon sa yayi ja ya Kwada mata mari a wajen saka bata har tana ta tsane Shi bayan ta Shiga daki tana kuka Rana da Bushwa suka fara murna aikin su yayi kyau daga bisani ne wannan matar yayan Rana din taji ta takuru indai ba ta fada ba bayan ta fadawa Raja kome har wanda yayi kamannin yayan nasa aka biyashi yaje har wajen sa ya fara dukan sa yace se yakaishi wajen madhu ya fadi kome da kansa Ashe anyi rashin Saa a lokacin Shi wannan dan iskan suna waya da Bushwa be Kashe ba a yayin da su Raja suka shigo mota su kuma su Bushwa Sun shiga wata karuwar mota a take suka bigesu ai kuwa Wancan ya mutu Shi ma Raja yaji ciwuka aka kaishi asibiti matar Rana taji labari ta fito da kanta yau xata fadawa madhu a yayin da take mata bayanin kome Rana mijin ta xai hana ta cikin bacin rai ta cire sarqar auren tace a shirye take da ta rabu dashi Domin ta gaji da zalincin nan jikin sa shima yayi sanyi daga gefe kuma madhu ta fara kaicho da irin rayuwar da yayyen ta suke har ta fara da na sanin xama yar uwarsu sannan ta Yanke hukuncin xata tafi ta nemi yafiya tana qoqarin fita Bushwa ya riqe ta domin hanata tafiya Ashe Shi kuma Rana ya dauko ya haqura shima ya dakatar da kanin nasa watau Bushwa amma da ya fuskan ci xata tafi din kawai ya dauko bindiga ya harbi yayan nasu ta dawo a firgice yace ba inda xataje ita kuma tace se taje yace ke ko Sunan sa ma banaso na kara ji tace Raja yana dukan ta tana fadar Sunan daga karshe ya zuba mata fetir xe kunna mata wuta nan take Raja ya shigo ya fara dukan sa yasa masa fetur tare da xagaye wajen da wuta da yayi qoqarin fitowa xai qoneshi bayan.... ya shigo wajen Ashe shima Rana be mutu ba a take a wajen suka shirya musu auren kuma to da wannan wutar da ta xagaye da Bushwa suka xagaye kamar yanda Al'adar auren su yake shi kuma yana ji yana kalla amma ba yanda xaiyi kuma daga bisani Bilju yasa aka kunna ruwa yaje ya fito dashi nan take Rana ya fara kuka yana bawa su Bilju haquri sannan ya fadawa Kaninsa Bushwa yau gashi mutumin da kake qi Shi ya cece rayuwar ka shima ya fadi Kasa yana basu haquri tare da nadama duk suka yafe musu daga nan ne su Raja suka ci gaba da rayuwa cikin jin dadi da farin ciki...
Anan wannan labari ya kare fatan mun samu wani darasi acikin sa.....

Post a Comment (0)